18
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Tsohon shugaban rundunar sojojin ƙasa na Nijeriya, Laftanal Janar Theophilus Yakubu Ɗanjuma ya ƙalubalanci jagororin tsaro su kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci da suka addabi sassa daban-daban na ƙasar. TY Ɗanjuma ya bayyana haka ne a lokacin gabatar da wani littafi mai suna 'Big Boots: Lessons from My Military Service' wanda Manjo-Janar Solomon Udouma ya wallafa, da aka yi a ɗakin taro na sojoji da ke Abuja. Ya ce, a halin yanzu babu wani uzuri da za a bai wa jami'an kan halin taɓarɓarewar tsaro da ke cigaba da addabar Nijeriya. TY, wanda tsohon ministan tsaro ne,…
