ukarofi

12546 Posts
An garzaya da wata uwargida asibiti bayan samun labarin mijinta ya ƙara aure a ɓoye

An garzaya da wata uwargida asibiti bayan samun labarin mijinta ya ƙara aure a ɓoye

Wata mata mazauniyar garin Ashaiman da ke ƙasar Ghana ta kwanta jinya a asibiti bayan ta suma sakamakon gano cewa mijinta ya auri wata mata a matsayin mata ta biyu ba tare da sanar da ita ba. Rahotanni sun bayyana cewa yayin da ake gudanar da bikin auren matar ta biyu a wani wuri daban, mijin ya shafe ranar yana gida tare da matarsa ta farko kamar yadda suka saba yi, ba tare da ya nuna wata alamar cewa yana shirin ƙara aure ba. An ce matar ta farko ta samu labarin auren ne bayan an kammala komai, lamarin da…
Read More
Ministan Labarai ya buƙaci masu masana’antar buga takardu su haɗa kai don samun bunƙasa

Ministan Labarai ya buƙaci masu masana’antar buga takardu su haɗa kai don samun bunƙasa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Mohammed Idris, ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a kamfanonin buga takardu ta Nijeriya da su rungumi haɗin kai, sasanci da kuma haɗin gwiwa domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da kuma ƙara wa fannin ƙarfin gasa a matakin duniya. Ministan ya bayyana hakan ne a yayin Taron Masu Ruwa da Tsaki na Masana'antar Buga Takardu ta Nijeriya na 2026, mai taken "Daga Sasanci Zuwa Farfaɗowa", wanda aka gudanar a ranar Talata a Abuja. Ya ce, warware rikicin shugabanci da ya daɗe yana…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta kafa kotun musamman domin saurin warware rikice-rikicen kasuwanci

Gwamnatin Tarayya za ta kafa kotun musamman domin saurin warware rikice-rikicen kasuwanci

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana shirinta na kafa Kotun Musamman ta Warware Rikice-rikicen Kasuwanci, domin hanzarta sasanta rikice-rikicen da suka shafi harkokin kasuwanci da zuba jari a faɗin ƙasar. Ministan Kuɗi kuma Ministan Da Ke Kula da Harkokin Tattalin Arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake gabatar da lakcinsa na farko a matsayin ɗan ƙungiyar Masanan Ilimin Kasuwar Jari ta Nijeriya (CMAN) a taronta na biyu da ake gudanarwa duk bayan shekara biyu a Abuja. Taron ya gudana ne ƙarƙashin taken "Kasuwar Jarin Nijeriya a Matsayin Ginshiƙin Ci Gaba…
Read More
Hana mata kasuwanci a Afirka zai jefa kasuwar Dala tiriliyan 3.4 cikin haɗari – UNDP

Hana mata kasuwanci a Afirka zai jefa kasuwar Dala tiriliyan 3.4 cikin haɗari – UNDP

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shirin Raya ƙasashe na Majalisar ɗinkin Duniya (UNDP) tare da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki sun yi kira da a gaggauta kawar da matsalolin kuɗi, na iyakoki da sauran ƙalubalen da ke hana mata gudanar da kasuwanci cikin sauƙi a nahiyar Afirka, suna masu gargaɗin cewa ci gaba da ware mata daga cikakken shiga harkokin kasuwanci na iya jefa kasuwar bai ɗaya ta nahiyar da darajarta ta kai dala tiriliyan 3.4 cikin haɗari. An bayyana wannan ne a yayin taron yanki na HerAfCFTA 2026 da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin inuwar Yarjejeniyar…
Read More
Farashin gas ya fara sauka bayan wadatarsa a Nijeriya

Farashin gas ya fara sauka bayan wadatarsa a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Al’ummomi a sassa daban-daban na Nijeriya sun fara samun sassauci kan farashin gas na girki, bayan da farashin iskar gas mai ruwa (LPG) ya fara raguwa sakamakon ƙarin wadatar kayayyakin da kuma saukar farashin saye daga manyan cibiyoyi. Rahoton kasuwa na baya-bayan nan daga masu kasuwancin gas ya nuna cewa farashin gas na girki ya fara sauka a manyan biranen ƙasar nan bayan makonni da aka shafe ana fama da tsadar sa. Sai dai raguwar farashin ba ta zo daidai a ko ina ba, saboda bambancin kuɗin sufuri, nisan wuraren ajiya da kuma ribar da dillalai…
Read More
Sabon cece-kuce ya ɓarke kan mutuwar jarumi Alex Ekubo 

Sabon cece-kuce ya ɓarke kan mutuwar jarumi Alex Ekubo 

Ya wofantar da mahaifiyarsa, ba mai mutunci a idonsa sai matar ubansa, inji ɗan uwan jarumin  Daga AISHA ASAS  Watanni kaɗan bayan rasuwar fitaccen jarumin Nollywood Alex Ekubo, sabon rikici ya ɓarke cikin iyalansa bayan wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin ɗan uwansa, Clinton Ekubo, ya fito da jerin zarge-zarge da suka sake ɗaga hankalin jama'a kan yadda rayuwar marigayin ta kasance kafin mutuwarsa da kuma yadda aka gudanar da jana'izarsa. A cikin wani dogon saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Clinton ya yi ikirarin cewa matar mahaifin Alexx ta taka muhimmiyar rawa wajen yanke muhimman…
Read More
Jarumi Joseph Momodu ya zama sojin Amurka 

Jarumi Joseph Momodu ya zama sojin Amurka 

Daga AISHA ASAS  A wani mataki da ya ba da mamaki ga masoyansa, fitaccen jarumin fina-finan Nollywood Joseph Momodu ya sanar da cewa ya zama cikakken soja a rundunar sojin Amurka, bayan ya kammala horon farko na aikin soja cikin nasara. Jarumin ya bayyana cewa wannan nasara ba kawai cikar wani buri na ƙuruciya ba ce, har ila yau hanya ce ta girmama mahaifinsa marigayi, wanda ya yi shekaru yana aiki a rundunar 'yan sandan Najeriya. Momodu ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya waiwayi tafiyar da ta kai shi ga…
Read More
Jarumi Hanks ya tayar da ƙura bayan fitar bidiyon sa zaune gefen hanya a Abuja 

Jarumi Hanks ya tayar da ƙura bayan fitar bidiyon sa zaune gefen hanya a Abuja 

Daga AISHA ASAS  Sabon bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya sake jefa masoya fina-finan Nollywood cikin damuwa bayan an hango fitaccen jarumi Hanks Anuku zaune shi kaɗai a gefen wata hanya a Abuja. Bidiyon ya fara yaɗuwa ne bayan wani mai amfani da shafin X mai suna Anthony Ehilebo ya wallafa shi, yana mai cewa shi da kansa ya ci karo da jarumin a yankin Wuse 2 da ke Abuja. A cikin bidiyon, an ga Hanks Anuku zaune a kan ciyawa da ke gefen hanya yana riƙe da wani abu mai kama da kofi. Da yake wallafa…
Read More
Fitattun taurarin da suka yi ridda: Mene ne alaƙar dake tsakanin fitattun mutanen da suka bar Musulunci?

Fitattun taurarin da suka yi ridda: Mene ne alaƙar dake tsakanin fitattun mutanen da suka bar Musulunci?

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS A taƙaice dai sauya addini a cikin al'ummar Yarbawa bai zama abin faɗi ba ko bada labari ba, kuma kaso mai yawa daga cikinsu suna canza addinin ne zuwa inda ya fi masu sauƙi ba wai gano gaskiya ba. Ba wai ina nufin al'ummar Yarbawa ba sa riƙo da addini ba, a binciken da aka yi a kwanakin baya ya nuna yadda bayaraben da ya yi riƙo da addini ke zarce kowa wurin iya yi masa sadaukarwa. Akan samu wasu ƙalilan daga Yarbawan da suka ƙiya wa wannan al'ada tasu ta fifita…
Read More
Yadda zargin sauya sunayen ‘yan takara ke haifar da barazana a APC

Yadda zargin sauya sunayen ‘yan takara ke haifar da barazana a APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Yayin da jam'iyyun siyasar Nijeriya suka fara shigar da sunayen 'yan takararsu na kujeru daban-daban a shafin Hukumar Zaɓe ta ƙasar INEC, wata sabuwar ƙura ta sake tashi a cikin jam'iyyar APC mai mulki, inda wasu daga cikin 'yan takarar da suka yi nasara a zaɓukan fidda gwani ke zargin cewa an sauya ko kuma ana shirin sauya sunayensu duk da cewa su ne suka lashe zaɓe. Dama dai tun bayan kammala zaɓukan fidda gwanin ne wasu mambobin jam'iyyar suka riƙa bayyana ƙorafe-ƙorafe kan yadda aka gudanar da zaɓukan, lamarin da ya sa jam'iyyar…
Read More