05
Jul
Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu da ake zargin ɓarayin daji ne sun toshe hanyar Bakori zuwa Guga a jihar Katsina, inda suka sace matafiya aƙalla tara bayan sun dawo daga kasuwa ta mako-mako, in ji mazauna yankin. An rawaito cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yamma ranar Juma'a a garin Dawan La'ila, sun toshe wani sashe na hanyar da ta haɗa al'ummomin Bakori da Guga, inda 'yan bindigar suka tare motar da ke ɗauke da fasinjojin waɗanda suka dawo daga kasuwar Bakori. Wani shugaban al'umma, Mahadi Ɗanbita, ya shaida wa majiyar Blueprint Manhaja a wata…
