ukarofi

12542 Posts
Babban tarihi mafi kyau da Buhari ya bari shine zuba jari a fannin ilimi da gina al’umma

Babban tarihi mafi kyau da Buhari ya bari shine zuba jari a fannin ilimi da gina al’umma

Daga UMAR GARBA a Katsina Uwargidan tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta bayyana cewa babban abin a yaba da mijin nata ya rasu ya bari shi ne zuba jari a fannin ilimi da kuma gina al'ummar Najeriya. A cewarta, Marigayi Buhari ya ba ilimi muhimmanci a lokacin mulkinsa, inda ya aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka yi niyyar inganta ilimi da bunƙasa damar samun ilimi ga 'yan Najeriya. Ta ce wannan ne zai ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za a riƙa tunawa da shi a tarihin ƙasar nan. A'isha Buhari ta…
Read More
Kada ma’aikatan Katsina su damu bisa sabon tsarin fansho – Dakta Faruk

Kada ma’aikatan Katsina su damu bisa sabon tsarin fansho – Dakta Faruk

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho da gratuti na Jihar Katsina, Dr. Faruk Aminu, ya tabbatar wa ma'aikatan gwamnati cewa babu wani abin fargaba dangane da sabon tsarin fansho na gudunmawar ma'aikata (Contributory Pension Scheme). Ya ce sabon tsarin zai tabbatar da tsaro ga kuɗaɗen fansho, tare da ƙara amincewa da yarda daga jama'a. Dr. Faruk Aminu ya bayyana haka ne a Katsina A cewarsa, gwamnatin Dikko Umar Raɗɗa ce ya amince da sabon tsarin domin tabbatar da ɗorewar tsarin fansho ta hanyar rufe duk wata kafa ta almundahana da karkatar da kuɗaɗe. Ya bayyana cewa…
Read More
Shettima ya ƙaddamar da masana’antar sarrafa lithium ta Najeriya

Shettima ya ƙaddamar da masana’antar sarrafa lithium ta Najeriya

Daga JOHN D WADA a Lafiya Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ƙaddamar da wata babbar masana’antar sarrafa lithium ta Najeriya wadda gwamnatin jihar Nasarawa ta gina inda ya bayyana cewa harkar ma’adinai za ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙoƙarin gwamnatin tarayya na sauya fasalin tattalin arziki da samar da ayyukan yi da kuma sanya Najeriya cikin manyan ƙasashe masu fafatawa a kasuwar ma’adinai ta duniya. Da yake wakiltar shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen ƙaddamar da masana’antar Diamond New Energy Projects ta sarrafa lithium a ranar Alhamis, Shettima yace wannan jarin ya nuna ƙaruwar ƙwarin gwiwa kan sauye-sauyen tattalin…
Read More
Gwamnan Nasarawa ya miƙa sandan sarauta ga sabon Aren Eggon

Gwamnan Nasarawa ya miƙa sandan sarauta ga sabon Aren Eggon

Daga JOHN D WADA a Lafia Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya miƙa sandar girma na musamman na sarauta ga Alƙali Ahmed Ubangari Alaku mai ritaya inda ya naɗa shi a hukumance a matsayin sabon Aren Eggon wato sarki mai daraja a faɗin Ƙasar Eggon. Wannan naɗin sarautar mai ɗimbin tarihi ta zo ne kusan shekaru 40 bayan marigayi tsohon gwamnan Filato Solomon Lar ya fara ba da amincewa ta gargajiya ga wani Aren Eggon a lokacin da jihar ta Nasarawa ke cikin tsohuwar jihar Filato lamarin da ya zama muhimmin tarihi a cikin harkar sarautar Eggon. Wakilin mu…
Read More
Harriet Tubman: Matar da ta mayar da ‘yancinta makamin yaƙar bauta 

Harriet Tubman: Matar da ta mayar da ‘yancinta makamin yaƙar bauta 

Lokacin da na ƙetare layin bauta, sai da na kalli hannuna domin tabbatar da ko ni ɗin ce - Harriet Tubman  (Ci gaba daga makon jiya)  Daga AISHA ASAS  A makon da ya gabata mun soma bibiyan tarihin wata jaruma mai matuƙar girma a tarihin duniya, Harriet Tubman wadda aka haifa cikin ƙangin bauta, amma ta ƙi yarda rayuwarta ta ƙare a sarƙoƙin bauta. Mun bi sawun ƙurciyarta a Maryland, mun dubi yadda rayuwar bauta ta gina tsoro tun a lokacin ƙurciya, har zuwa mummunan rauni da ta samu a lokacin ƙurci wanda ya zama rauni da ya sauya mata…
Read More
Ƙarfafa sarakuna zai bunƙasa zaman lafiya da tsaro a Gombe – Akko

Ƙarfafa sarakuna zai bunƙasa zaman lafiya da tsaro a Gombe – Akko

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Majikiran Gona, Arc. Mohammed Abubakar Akko, ya yi kira ga gwamnatin jihar Gombe da ta inganta tsarin jin daɗin mambobin majalisar sarakuna da hakiman jihar, yana mai cewa ƙarfafa cibiyoyin gargajiya zai taimaka wajen bunƙasa zaman lafiya, tsaro da ci gaban al'umma. Akko ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikice-rikice, tabbatar da zaman lafiya da kuma tallafa wa gwamnati a harkokin tsaro, don haka ya zama wajibi a samar musu da ingantaccen tallafi da kayan aiki domin sauƙaƙa musu gudanar da ayyukansu. Ya yabawa gwamnatin jihar bisa gyaran da ake…
Read More
An yi kira ga gwamnatin Katsina ta binciki yadda gobara ta lashe cibiyar kula da lafiya ta Funtua

An yi kira ga gwamnatin Katsina ta binciki yadda gobara ta lashe cibiyar kula da lafiya ta Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Ƙungiyar cigaban Funtua a Jihar Katsina ta yi kira ga gwamnatin Katsina da ta binciki yadda Gobara ta laƙume cibiyar kula da lafiya na Funtua tare da ɗaukar mataki na gyaran cibiyar duba da mahimmancin da take da shi wajen kula da lafiyar al'ummar yankin. Shugaban ƙungiyar Kwamred Mannir Suleiman ya yi wannan kira bayan shi da ya'yan kungiyar suka ziyarci cibiyar wadda ita ce ta biyu bayan babban asibitin Funtua. Ya ce gobarar ta lashe ginin cibiyar gaba ɗaya tare da duk abinda ke ciki. Ya ce cibiyar ita ce ta biyu bayan babban…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun kama wani matashi da ake zargi da aikata fashi da makami

‘Yan sanda a Katsina sun kama wani matashi da ake zargi da aikata fashi da makami

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda a Katsina sun sami nasarar kama wani matashi mai suna Adan Ibrahim Tama ɗan shekara 20 da aikata fashi da makami da yunkurin hallaka 'yar uwarsa a Katsina. Jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗi haka a wata takardar sanarwa da ya fitar a Katsina. DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa Hajiya Jamila Ibrahim Tama 'yar wanda ake zargi ta kai koke ga ofishin 'yan sanda da ke Sabon Gari a Katsina cewa wanda ake zargi ya Kai hari ga ɗiyar ta Fatima Nura Lawal…
Read More
Jami’in KAROTA ya bada jininsa domin ceton rayuwar wata yarinya a Kano

Jami’in KAROTA ya bada jininsa domin ceton rayuwar wata yarinya a Kano

Sauye-sauyen da ake ci gaba da aiwatarwa a hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ƙarƙashin jagorancin Alhaji Faisal Mahmud Kabir, sun fara haifar da gagarumin sakamako, inda jami'an hukumar ke nuna ƙwarewa, kishin ƙasa, tausayi da kuma sadaukar da kai wajen yi wa al'umma hidima. A cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharada, ya fitar a ranar Juma'a, ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarori masu yawa wajen tabbatar da bin dokokin zirga-zirga tare da rungumar tsarin aiwatar da doka cikin mutuntaka da jin ƙai. Ɗaya daga cikin nasarorin da…
Read More
Hukumar hisbah ta kai samame a Argungu

Hukumar hisbah ta kai samame a Argungu

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Hukumar hisba ta jihar Kebbi ta sami nasarar kama waɗansu mutane 25 yayin wani samame da ta kai a wani otel da ke garin Argungu. Rahotanni sun nuna cewa hukumar hisbah ta Jihar Kebbi ta kama mutane 25 da suka haɗa da maza da mata, yayin wani samame da ta kai a wani otel da ke garin Argungu bayan samun bayanan cewa ana gudanar da baɗala a wurin. Hukumar ta ce an kama waɗannan mutane ne bisa zargin karya doka da haramtacciyar hulɗa tsakanin maza da mata.Hukumar ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike…
Read More