07
Jul
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jamaʼa, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin taron Arewa Media Summit da ofishin mai taimaka wa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da wayar da kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya shirya a ranar Litinin a birnin Kano. Ministan ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa haɗin kai, juriya da kyakkyawan fata a tsakanin al'umma. Ya kuma yi gargaɗin cewa yaɗuwar labaran ƙarya da bayanan da ba su da tushe a kafafen sadarwa na iya yin barazana ga haɗin kan ƙasa da amincewar…
