07
Jul
Daga JOHN D WADA a Lafia Shugaban yankin raya Lafia ta Arewa Hon. Nasiru Kasimu Akanza ya yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa bisa ayyukan hanyoyi da ake cigaba da yi, yana mai cewa ayyuka ne na tarihi da za su inganta cigaban tattalin arziki da sauƙaƙe zirga-zirga a faɗin ƙasa. Da yake tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Shabu na ƙaramar hukumar Lafia, Akanza ya yaba da ƙaddamar da aikin babbar hanyar Akwanga zuwa Jos da Gombe da Maiduguri da kuma buɗe hanyar kilomita 3 mai layi biyu da aka…
