ukarofi

12542 Posts
Sojoji sun daƙile hari a Kebbi

Sojoji sun daƙile hari a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Sojojin Nijeriya da ke aikin samar da tsaro a kan hanyar da ta haɗa Nijeriya da Jamhuriyar Benin sun fatattaki wani ayarin mahara da suka suka kai farmaki a garin Ka'oje da ke ƙaramar hukumar Bagudo cikin daren Larabar nan. Malam Nuhu Ka'oje ya shaida wa waƙilin blueprint Manhaja da cewa maharan sun shigo garin Ka'oje ne da misalin ƙarfe biyu na dare kan babura inda suka yi arba da sojojin. Ya ƙara da cewa maharan ana sa ran masu garkuwa da mutane ne domin neman kuɗin fansa saboda sau da yawa sukan shiga cikin…
Read More
Gwale 2027: Zan ba ilimi, matasa da marayu muhimmanci idan na ci zaɓe – Tijjani Maizare

Gwale 2027: Zan ba ilimi, matasa da marayu muhimmanci idan na ci zaɓe – Tijjani Maizare

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale a jam'iyyar PDP, Hon. Tijjani Rabi'u Alhassan Mai Zare, ya bayyana cewa idan Allah ya ba shi damar wakiltar al'ummar Gwale, zai bai wa ilimi, matasa, mata, ƙananan yara da kuma harkar ruwan sha muhimmanci a ƙaramar hukumar. A zantawarsa da Blueprint Manhaja, Mai Zare ya ce takararsa ta Allah ce, kuma duk wani al'amari sun bar shi ga Ubangiji. Ya ƙara da cewa suna roƙon Allah ya zaɓa musu abin da ya fi alheri. Hon. Tijjani Mai Zare ya bayyana cewa ya…
Read More
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta yi Allah wadai da kama Dakta Bishir Kurfi

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta yi Allah wadai da kama Dakta Bishir Kurfi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Daraktan ƙungiyar kare hakin ɗan Adam a Najeriya (Amnesty International) Malam Isah Sunusi ya yi Allah wadai da kama Dakta Bishir Kurfi da Gwamnatin Katsina da jami'an 'yan sanda suka yi. Malam Isah Sunusi wanda ya faɗi haka a wata hira da yayi a wata kafar sadarwa ya ce tsare Dakta Kurfi da akayi ya saɓa doka,take haƙƙin biladama da nuna amfani da ƙarfin iko wajen aikata ba daidai ba. Ya ce ƙungiyar ta gano kama Dakta Kurfi ya aza ayar tambaya akan wasu abubbuwa da ya zargi gwamnatin Katsina da aikatawa, bai kamata ace…
Read More
Ina da burin ganin kasuwar littafai ta dawo hayyacinta – Saliha Abubakar Abdullahi Zaria

Ina da burin ganin kasuwar littafai ta dawo hayyacinta – Saliha Abubakar Abdullahi Zaria

"Rubutu tamkar zazzaɓi ne, duk lokacin da masassarar ta taso, ɗaukar alƙalami da takarda ne magani" Daga AISHA ASAS Waiwaye dai aka ce adon tafiya ne, yayin da rawar 'yan mata kan ƙayatar ne a lokacin da suke yin gaba suna dawowa baya. Idan akayi zancen Adabin Hausa, dole ne a sanya marubuta mata da suka fara rubutu tun lokacin da kai bai waye ba. Su ne marubutan da suka fuskanci ƙalubale masu yawa kasancewar sun fara abin da al'ummar Hausa ba su fara gani ba, don haka suka jahilce shi har ta kai su na masa mummunar fahimta.  Don…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun gurfanar da Dakta Bashir Kurfi kotu bisa zargin ɓata sunan Raɗɗa

‘Yan sanda a Katsina sun gurfanar da Dakta Bashir Kurfi kotu bisa zargin ɓata sunan Raɗɗa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda a Katsina sun kai malamin jami'a, Dr Bashir Kurfi kotu bisa zargin yiwa Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa karya da ɓata suna. Lauyan wanda ake ƙara Barista AD umar ya bayyana cewa kotu ta gabatar da tuhuma biyu da ake zargin Dr Kurfi da aikatawa wanda ya musanta. Lauyan ya ce yau ne zaman na farko inda suka nemi bada belin wanda ake zargi tunda laifin bai kai matsayin da za a hana beli ba ne. Sai dai a cewar sa 'yan sanda masu gabatar da ƙara sun nuna rashin yarda da…
Read More
Dole ne fulani su kai yaransu makaranta – Abdullahi Gudale

Dole ne fulani su kai yaransu makaranta – Abdullahi Gudale

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Alhaji Abdullahi Muhammad Gudale sakataren ƙungiyar Miyetti Allah ƙaramar hukumar Augie ya yi kira ga Fulani da su kai yaran su makaranta. Ya yi wannan kira ne ranar Talatar da ta gabata a garin Augie yayin wani taron shugabannin Fulani da jami'an ƙaramar hukumar. Ya bayyana cewa yanzu haka duk makarantun da aka gina domin yaran Fulani suna nan suna komawa kufai saboda rashin ɗalibai. Yanzu haka malamai sun daina zuwa sanadiyyar ba kowa duk da ya ke a kowane wata gwamnati tana biyan su albashi.Sanin kowa ne fulani mutane ne masu basira sosai da…
Read More
Tarihin Gobir da yadda Gobirawa suka riski ƙasar Hausa

Tarihin Gobir da yadda Gobirawa suka riski ƙasar Hausa

Masarautar Gobir na ɗaya daga cikin tsofaffin daulolin ƙasar Hausa, kuma tana daga cikin manyan masarautun da suka taka muhimmiyar rawa a tarihin Arewacin Nijeriya da yankin Sahel. A tarihin da aka fi sani, ƙasar Gobir ta yi iyaka da Agades daga arewa, Zamfara daga kudu, Mayali daga gabas, sannan daga yamma ta yi iyaka da Konni. Sai dai, akwai ra'ayoyi mabambanta kan asalin Gobirawa. Wasu masana da masu riƙe da tarihin gargajiya na cewa Gobirawa ba Hausawa ba ne a asali, suna kuma danganta asalinsu da Gabas ta Tsakiya, musamman ƙwasar Masar (Egypt). Haka kuma, akwai masu cewa wasu…
Read More
Fitilar bada hannu: Ma’ana, muhimmancinta da illar rashin amfani da ita

Fitilar bada hannu: Ma’ana, muhimmancinta da illar rashin amfani da ita

Tare da BILKISU YUSUF ALI Gabatarwa A zamanin yau, harkokin sufuri da zirga-zirgar ababen hawa sun zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar ɗan adam, musamman a birane. Yawaitar motoci da  babura da masu tafiya a ƙafa ya haifar da buƙatar tsari mai kyau domin tabbatar da tsaro da ingantacciyar zirga-zirga. ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da ake amfani da su wajen sarrafa zirga-zirga shine fitilar bada hannu, wato traffic light a turance. Fitilar bada hannu wata na’ura ce da ake sanyawa a hanyoyi domin sarrafa motsin ababen hawa da masu tafiya a kafa ta hanyar amfani da launuka uku: ja,…
Read More
Lokaci ya yi da za mu haɗa kanmu a ADC – Ƴargiwa

Lokaci ya yi da za mu haɗa kanmu a ADC – Ƴargiwa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Argungu da Augie Honarabul Sani Yakubu Ƴargiwa ya yi kira ga ƴaƴan jam'iyyar ADC da su ajiye duk wani bambance-bambance su zo a haɗu don fuskantar zaɓe mai zuwa. Ya yi wannan kira ne a garin Argungu a wani taron shugabannin jam'iyyar na ƙaramar hukumar Augie. Honarabul Ƴar Giwa ya ce a jam'iyyar ADC babu wani bambanci ga dukkan ƴan takarar da aka tsayar tun kama daga ƴan majalisar dokoki, tarayya, dattawa da gwamna da kuma shugaban ƙasa. ADC ɗaya ce kuma mai manufa ɗaya saboda haka yanzu…
Read More
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da shugabancin LP na Nenadi Usman

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da shugabancin LP na Nenadi Usman

Daga AHMID LAWAL a Abuja Kotun ɗaukaka ƙara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na ƙasa ne kawai, ƙarƙashin Sanata Nenadi Usman, ne zai iya ba da izinin shigar da ƙara a madadin jam’iyyar. Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar Labour Party na ƙasa, Ken Asogwa, ya fitar a Abuja ranar Litinin. Ya ce hukuncin ranar 2 ga Yuli na kotun ɗaukaka ƙara, shiyyar Owerri, a cikin ƙarar lamba CA/OW/104/2026: Labour Party da 14 wasu da sauransu v. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Abia da wasu huɗu ya…
Read More