ukarofi

12542 Posts
Ba takardar digiri kaɗai ake buƙata a jami’a ba – Shettima

Ba takardar digiri kaɗai ake buƙata a jami’a ba – Shettima

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ce lokaci ya yi da jami'o'in Nijeriya za su sauya salon aikinsu ta hanyar zama cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci da bunƙasa masana'antu, maimakon mayar da hankali kan fitar da masu takardun shaida kawai. Shettima ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da cibiyar Manufacturing Technology Uniɓersity Innoɓation Pod (Manu-Tech UniPod) a Jami'ar Noma ta Michael Okpara da ke Umudike, ƙaramar hukumar Ikwuano a Jihar Abia. An kafa cibiyar ne domin haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire a fannin fasaha da kuma bunƙasa harkokin kasuwanci. Shirin haɗin gwiwa ne tsakanin Shirin Raya ƙasashe na Majalisar ɗinkin…
Read More
Laifi ne ƙin karɓar tsohuwar takardar Naira 100 – CBN

Laifi ne ƙin karɓar tsohuwar takardar Naira 100 – CBN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata raɗe-raɗi da rahotanni masu yayata cewa ya sanar da daina amfani da takardar Naira 100 ta ainihi. Cikin wata sanarwar da CBN ya fitar a ranar Laraba, 8 ga Yuli 2026, mai ɗauke da sa hannun Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama'a da Sadarwa, Hajiya Hakama Sidi Ali, bankin ya yi ƙarin haske kan matsayin takardar kuɗin Naira N100 a matsayin halastacciya abin ci gaba da karɓa da yin hada-hadar kuɗin biyan buƙatun yau da kullum. Kan haka, CBN ya ja hankalin jama'a kan su yi watsi da rahotannin…
Read More
Jaiz na fuskantar hukunci kan zargin ƙin bin umarnin kotu a Kano

Jaiz na fuskantar hukunci kan zargin ƙin bin umarnin kotu a Kano

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bankin Jaiz, wanda shi ne bankin farko mai gudanar da harkokin kuɗi ba tare da ruwa ba a Nijeriya, na fuskantar warin matsin lamba daga ɓangaren shari'a da masu sa ido kan harkokin bankuna, bayan zargin cewa ya ƙi aiwatar da umarnin da Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar na biyan kuɗin da kotu ta yanke. Lamarin ya samo asali ne daga umarnin aarshe na kwace kuɗi domin biyan bashin hukunci (Garnishee Order Absolute) da kotun ta bayar a ranar 8 ga Janairu, 2026, a shari'ar da ke tsakanin Yahaya Usman a matsayin wanda kotu ta…
Read More
Dangote zai gina babbar matatar mai a Kenya

Dangote zai gina babbar matatar mai a Kenya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rukunin Kamfanonin Dangote ya bayyana shirinsa na samar da kuɗaɗen gina sabuwar matatar mai mai ƙarfin tace ganga 700,000 a kowace rana a ƙasar Kenya, ta hanyar haɗa kuɗaɗen shiga na cikin gida, fitar da takardun bashin gwamnati da kuma kuɗaɗen da ake sa ran samu daga sayar da hannayen jari ga jama'a (IPO). Sabuwar matatar, wadda za a gina a Tsibirin Lamu da ke gabar tekun Kenya, ana sa ran za ta kasance mafi girma a Gabashin Afirka, tare da taimakawa wajen ƙarfafa tsaron makamashi a yankin ta hanyar rage dogaro da shigo da tataccen…
Read More
Kotu ta tsare tsohon Shugaban kotun ɗa’ar Ma’aikata, Danladi Umar a Kuje

Kotu ta tsare tsohon Shugaban kotun ɗa’ar Ma’aikata, Danladi Umar a Kuje

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja da ke zama a Maitama, Abuja, ta bayar da umarnin tsare tsohon shugaban Kotun ɗa'a ta Jami'an Gwamnati (CCT), Danladi Umar, a Gidan Gyaran Hali na Kuje har sai an saurari buƙatar belinsa. Hukuncin ya fito ne daga bakin Mai Shari'a Peter Kekemeke bayan Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta'annati (EFCC) ta gurfanar da Umar bisa tuhume-tuhume huɗu da suka shafi zargin amfani da muƙaminsa wajen bai wa kansa wata fa'ida da ba ta dace ba yayin da yake jagorantar Kotun ɗa'a ta CCT. A lokacin…
Read More
Amurka ta bayyana sunayen ’yan Nijeriya 124 za ta koro saboda laifuka

Amurka ta bayyana sunayen ’yan Nijeriya 124 za ta koro saboda laifuka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin ƙasar Amurka ta fitar da sabon jerin sunaye da hotunan ’yan Nijeriya 124 da ta sanya cikin rukunin waɗanda ta bayyana a matsayin "manyan masu laifi mafi muni", a wani ɓangare na sabon matakin da gwamnatin Donald Trump ke ɗauka na tsaurara dokokin shige da fice da korar baƙi. Rahoton ya nuna cewa Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ce ta wallafa jerin a shafinta na hukuma a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa mutanen da aka sanya sunayensu ba ’yan ƙasar Amurka ba ne, kuma Hukumar Shige da Fice da Kwastom ta Amurka…
Read More
Gwamnatin Tinubu ta sauya salon yaƙi da ta’addanci

Gwamnatin Tinubu ta sauya salon yaƙi da ta’addanci

*Ku harbi ’yan ta’adda babu jiran umarninmu – Musa ga dakaru *Ya ce, za a ɗauki sojan da ya jira umarnin harbi tamkar ɗan ta’adda *Majalisa ta nemi dakatar da shirin gyaran halin ’yan ta’adda *Kwamandojin ISWAP shida da iyalansu sun miƙa wuya a Borno Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya umarci dakarun Rundunar Sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro su riƙa ɗaukar mataki kai tsaye kan duk wani ɗan bindiga ko ɗan ta’adda da suka ci karo da shi, yana mai gargaɗin cewa duk jami’in da ya ƙi buɗe wuta saboda jiran umarni…
Read More
Ministan muhalli ya yaba da ƙoƙarin Kano kan sauyin yanayi da farfaɗo da muhalli

Ministan muhalli ya yaba da ƙoƙarin Kano kan sauyin yanayi da farfaɗo da muhalli

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ministan muhalli, Alhaji Balarabe Abbas Lawal, ya yabawa gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf kan irin ƙoƙarin da take yi wajen dashen bishiyoyi da farfaɗo da muhalli. Ya ce Kano ta zama abin koyi a Najeriya wajen aiwatar da matakan da ke taimakawa yaƙi da illolin sauyin yanayi. Haka kuma ya sake tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da mara wa jihar baya wajen dawo da korayen filaye da bunƙasa muhalli. Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin Ranar Babbar Katangar Kore ta 2026 (Great…
Read More
An ɗage shari’ar Samir da Turakin Augie kan zaɓen fitar da gwani

An ɗage shari’ar Samir da Turakin Augie kan zaɓen fitar da gwani

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Birnin Kebbi, a ranar Laraba 8 ga Yulin 2026, ta amince da buƙatar da Samir Salihu Felande ya gabatar na ba shi izinin shigar da ƙarin takardu daga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) a ƙarar da ya shigar kan sakamakon zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC da ta ce ta yi na ƙananan hukumomin Argungu/Augie. Wannan hukunci ya zama wani muhimmin ci gaba a shari'ar da ake yi tsakanin Felande da ɗan takarar APC, Umar Hassan Augie. Da ta ke zantawa da manema labarai bayan kammala zaman…
Read More
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga takwas a Katsina

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga takwas a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Sojojin 17 Bridge sun sami nasarar kashe 'yan bindiga takwas tare da ƙwace bindiga ƙirar AK 47 a ƙaramar hukumar Bakori da ke Jihar Katsina. Kamar yadda jami'in yaɗa labarai na rundunar 17 Bridge Kaftin Abayomi Adisa ya fitar da sanarwa, wannan lamari ya biyo bayan bayanan sirri da wani na kusa da hannun ƙasurgumin ɗan bindiga Idi Abasu Aiki cewa suna ƙoƙarin datse hanyar Kakumi zuwa Guda da nufin kai hari da matafiya hanyar. Da jin haka a cewar sojoji suka isa hanyar da 'yan bindigan suka tare nan sojojin suka shiga bata kashi…
Read More