10
Jul
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Zartarwa ta Jihar Kaduna ta amince da sayen tan 6,000 na takiin zamani, kwatankwacin buhu dubu 120,000, domin rabawa ƙananan manoma a jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu, Ahmed Maiyaki, ya ce an ɗauki wannan mataki ne a taron majalisar da Gwamna Uba Sani ya jagoranta ranar Talata, a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa noma da bunƙasa samar da abinci. Ya tunatar da cewa a watan Agustan 2025, gwamnatin jihar ta raba manyan motocin taki 400 kyauta ga manoma 100,000, sannan a shekarar 2024 ta aiwatar da mafi girman shirin rabon…
