ukarofi

12542 Posts
An buƙaci masu ruwa da tsaki da su sa baki kan taɓarɓarewar hanyoyin Gwamnatin Tarayya a Katsina

An buƙaci masu ruwa da tsaki da su sa baki kan taɓarɓarewar hanyoyin Gwamnatin Tarayya a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kungiyar cigaban Funtua tayi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa, 'yan majalisar ƙasa,Sarakuna, manyan 'yan kasuwa da sauran masu faɗa a ji da su buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya bada umurnin gyaran honyoyin gwamnatin tarayya tun kafin damina ta tafi da wasu. Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman wanda yayi wannan kira a Funtua a hira da manema labarai ya ce babu wata hanya ta gwamnatin tarayya a Katsina da bata lalace ba. Kwamred Suleiman ya nuna rashin jin daɗin sa ga yadda gwamnatin tarayya ta zuba makudan kuɗi kan gyaran wasu hanyoyi a wasu…
Read More
Hukunta ‘yan ta’adda 150 cikin kwanaki biyu ya nuna sauyin salo a yaƙi da matsalar tsaro

Hukunta ‘yan ta’adda 150 cikin kwanaki biyu ya nuna sauyin salo a yaƙi da matsalar tsaro

Samun nasarar hukunta mutum 150 da aka samu da laifukan ta'addanci cikin kwanaki biyu kacal ya zama wani babban ci gaba a tsarin shari'ar Nijeriya. Wannan mataki ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta fara ɗaukar yaƙi da ta'addanci da muhimmanci, tare da ƙoƙarin tabbatar da cewa masu aikata irin waɗannan manyan laifuka sun fuskanci hukunci cikin gaggawa. Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa a sabon zagayen shari'ar da aka gudanar a Abuja, an saurari shari'o'i kusan 160, inda aka samu hukuncin ɗaurin laifi ga kusan mutum 150. Ya kuma buƙaci al'umma su ci gaba da…
Read More
EFCC ta gurfanar da tsohon manajan matatar mai ta Fatakwal, Dikko, kan zargin karkatar da kuɗi

EFCC ta gurfanar da tsohon manajan matatar mai ta Fatakwal, Dikko, kan zargin karkatar da kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Matatar Mai ta Fatakwal (PHRC), Ahmed Dikko, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa tuhume-tuhume 12 da suka shafi zargin wankin kuɗi. An gurfanar da Dikko tare da kamfanin Masterpiece Projects & Investment Ltd, wanda shi ma ke fuskantar tuhume-tuhume a cikin shari'ar. A zaman kotun da Mai Shari'a Inyang Ekwo ya jagoranta, Dikko ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da EFCC ta gabatar a kansa, yayin da lauyan kamfanin da ake tuhuma tare da shi ya…
Read More
Madarasatul Irshadussibyan Islamiyya ta yi walimar saukar Alƙur’ani ga ɗalibai 60

Madarasatul Irshadussibyan Islamiyya ta yi walimar saukar Alƙur’ani ga ɗalibai 60

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Makarantar Madarasatul Irshadussibyan Islamiyya Lidarasatil Islamiyya Wa Tahfizul ƙur’an, da ke unguwar Darmanawa a ƙaramar Hukumar Tarauni ta jihar Kano, ta gudanar da walimar saukar Alƙur’ani ga ɗalibai 60. Shugaban makarantar, Ustaz Mannir Bello, ya bayyana cewa ɗalibai 55 ne da kuma mata masu aure biyar suka kammala karatun Alƙur’ani a wannan karo na biyar da makarantar ta shirya irin wannan walima. Taron ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na jihar Kano, inda aka kuma ƙaddamar da kalandar makarantar domin tallafa wa ayyukanta. A wajen taron, AIG Ma’azu Yarima PhD, wanda shi ne…
Read More
An buƙaci gwamnati ta tallafa wa masu kiwon kaji

An buƙaci gwamnati ta tallafa wa masu kiwon kaji

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano ɗaya daga cikin jami’an kamfanin Albarka Poultry, Alhaji Umar Ibrahim, ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da jihohi da su fara bai wa masu kiwon kaji tallafi kamar yadda ake yi wa manoma. Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kai da kamfanin ya shirya ga masu kiwon kaji a Kano domin bunƙasa sana’ar da inganta ribar masu gudanar da ita. Alhaji Umar ya ce taron ya mayar da hankali ne kan koyar da dabarun zamani na kiwon kaji da hanyoyin samun riba mai yawa a sana’ar. Ya kuma nuna damuwa kan yadda…
Read More
Majalisar Dattawa ta fara binciken alawus na miliyan N943 a NWDC

Majalisar Dattawa ta fara binciken alawus na miliyan N943 a NWDC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da ci gaban yankuna ya fara bincike kan yadda hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC) ke gudanar da ayyukanta, inda ya nuna damuwa kan kashe naira miliyan 943 a matsayin alawus ga mambobin kwamitin gudanarwa. A zaman binciken da aka gudanar ranar Talata, sanatocin sun ce matsalolin shugabanci da na gudanarwa na hana hukumar cika manufarta ta magance matsalar tsaro da gibin ababen more rayuwa a yankin Arewa maso Yamma. ƙaramin Ministan raya yankuna, Uba Ahmadu, ya bayyana cewa har yanzu NWDC ce kaɗai daga cikin hukumomin raya yankuna…
Read More
Karamar Hukumar Dandi ta nuna damuwa kan rashin waƙilci nagari

Karamar Hukumar Dandi ta nuna damuwa kan rashin waƙilci nagari

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Wasu al’ummar ƙaramar Hukumar Mulki ta Dandi da ke Jihar Kebbi sun bayyana damuwarsu kan abin da suka bayyana a matsayin rashin ingantaccen wakilci daga ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Arewa/Dandi a Majalisar Wakilai ta Tarayya. Daya daga cikin shugabannin matasa a yankin, Malam Hashimu Musa Buma, ya bayyana cewa akwai buƙatar sake nazari kan wakilcin Hon. Garba Rabi’u Kamba, wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Arewa da Dandi, yana mai zargin cewa wakilcin bai kai yadda al’umma ke tsammani ba. Ya ce ya kamata a yi la’akari da ra’ayin jama’a da kuma ƙarfafa shugabanci…
Read More
Majalisa Dattawa ta dakatar da mataki kan biliyan N1.3 da aka ware wa PFIPC, tana jiran rahoton ICPC

Majalisa Dattawa ta dakatar da mataki kan biliyan N1.3 da aka ware wa PFIPC, tana jiran rahoton ICPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Dattawa ta yanke shawarar jiran sakamakon binciken da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ke gudanarwa kafin ɗaukar wani ƙarin mataki kan takaddamar da ta shafi abin da ake kira Majalisar Bunƙasa Shigar da Jari daga ƙasashen Waje ta Fadar Shugaban ƙasa (PFIPC) da kuma yadda aka saka ta cikin kasafin kuɗin shekarar 2026. Matsayar ta biyo bayan wani ƙuduri da Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu mai wakiltar Kano ta Kudu ya gabatar, inda ya buƙaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan kuɗaɗen da aka ware wa hukumar,…
Read More
Tsaro: Gwamnonin Arewa sun kafa asusun musamman na naira biliyan ɗaya duk wata 

Tsaro: Gwamnonin Arewa sun kafa asusun musamman na naira biliyan ɗaya duk wata 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnonin Arewa sun ƙaddamar da Kwamitin Amintattu na Asusun Tsaron Arewacin Nijeriya, tare da jaddada haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya domin tinkarar matsalar tsaro. Gwamnonin jihohin Arewacin Nijeriya sun ƙaddamar da Kwamitin Amintattu (Board of Trustees) na Northern Nigeria Security Trust Fund (NNSTF) tare da amincewa cewa kowace jiha za ta rika bayar da gudunmawar Naira biliyan ɗaya duk wata domin ƙarfafa ayyukan tsaro a yankin. An cimma wannan matsaya ne a taron haɗin gwiwa na ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (Northern States Governors’ Forum) da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa, wanda aka gudanar a…
Read More
Za mu aiwatar da ayyukan raya ƙasa kamar na Abuja a dukkan jihohin Nijeriya – Tinubu 

Za mu aiwatar da ayyukan raya ƙasa kamar na Abuja a dukkan jihohin Nijeriya – Tinubu 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta faɗaɗa irin ci gaban ababen more rayuwa da ake samu a Babban Birnin Tarayya (FCT) zuwa sassan Nijeriya. Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da sabuwar hanyar Transitway N2 da ta haɗa Babban Yankin Kasuwanci da Wuse, tare da gadoji biyu da hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ta gina. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya wakilce shi. Ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa dukkan yankunan ƙasar sun amfana da hanyoyi, gadoji, layukan dogo da sauran muhimman ayyukan more…
Read More