11
Jul
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Ilimin Shari'a ta Makarantar Lauyoyi ta Nijeriya ta gargaɗi ɗaliban da ke jiran bikin rantsuwar kama aikin lauya, wato bar, da su guji sanya kayan aikin lauya tare da bayyana kansu a matsayin cikakkun lauyoyi kafin a hukumance a karɓe su cikin ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya. Rahoton ya nuna cewa wannan gargaɗi na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar Majalisar Ilimin Shari'a kuma Daraktar Gudanarwa, Aderonke Osho, ta sanya wa hannu, wadda Makarantar Horar Da Lauyoyi Ta Nijeriya ta fitar a ranar Talata. Majalisar ta bayyana cewa ta lura da yadda wasu masu jiran…
