11
Jul
Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau Ɗan Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Dr. Aminu Sani Jaji, ya bayyana sake tsayar da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a matsayin babban ƙwarin gwiwa ga damar jam’iyyar All Progressives Congress APC a zaɓen. A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis kuma Jamilu Iliyasu Birnin Magaji, mataimakin sa na yaɗa labarai ne ya sanya hannu, Jaji ya ce wannan shawara ta tabbatar da alƙiblar gwamnati kuma alama ce ta ci gaba ga APC gabanin babban zaɓen 2027. Dr. Jaji, wanda ke…
