12
Jul
Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta na wata mai sana'ar gashin masara da ta yi iƙirarin cewa tana samun sama da naira miliyan 2.5 a kowane wata ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Nijeriya, inda wasu suka nuna shakku kan iƙirarin, yayin da wasu kuma suka ce hakan na iya yiwuwa idan kasuwancin yana gudana a wuri mai kyau kuma ana tafiyar da shi yadda ya kamata. A cikin gajeren bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta daban-daban, an ga wata mata tana tambayar mai sayar da masarar yawan kuɗin da take samu daga sana'arta. Da amsa…
