ukarofi

12546 Posts
ADC ta gudanar da babban taro a Kano, ta soki gwamnatin APC

ADC ta gudanar da babban taro a Kano, ta soki gwamnatin APC

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta gudanar da wani babban taron siyasa a Kano, inda shugabanni da magoya bayanta suka yi kira ga 'yan Nijeriya su goyi bayan jam'iyyar a babban zaɓen 2027. Taron ya samu halartar magoya bayan tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar daga sassa daban-daban na ƙasar. Da yake jawabi, Alhaji Usman Mado, wanda aka fi sani da Sarkin Yaƙin Atiku, ya ce matsalar tsaro ta ƙara taɓarɓarewa musamman a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Borno da Katsina, inda ya ce hakan ya shafi noma, kasuwanci da…
Read More
2027: INEC ta bai wa APC, PDP, ADC, NDC da sauran jam’iyyu damar ɗora ‘yan takararsu a shafinta

2027: INEC ta bai wa APC, PDP, ADC, NDC da sauran jam’iyyu damar ɗora ‘yan takararsu a shafinta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bai wa jam'iyyun siyasa tara lambobin shiga (access codes) domin su fara loda sunayen 'yan takararsu a shafin hukumar gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Binciken jaridar Leadership ya nuna cewa jam'iyyun da suka samu lambobin sun haɗa da All Progressiɓes Congress (APC), Peoples Democratic Party (PDP), African Democratic Congress (ADC), Nigeria Democratic Congress (NDC) da wasu jam'iyyu masu rijista. Ana sa ran jam'iyyun za su yi amfani da lambobin wajen loda sunayen 'yan takararsu na kujerun Shugaban ƙasa, Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da kuma gwamna…
Read More
NDC a shirye take ta haɗa kai da ADC, Atiku domin tunkarar zaɓen 2027 – Dickson

NDC a shirye take ta haɗa kai da ADC, Atiku domin tunkarar zaɓen 2027 – Dickson

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jagoran jam’iyyar NDC, sanata Seriake Dickson, ya bayyana cewa jam’iyyarsa a shirye take ta tattauna yiwuwar haɗaka da sauran jam’iyyun adawa musamman jam’iyyar ADC domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. Dickson, wanda ke wakiltar mazaɓar Bayelsa ta yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Tɓ a shirin Sunday Politics. Ya ce, duk da cewa NDC ta shafe kusan watanni biyar ne kacal da kafuwa, ta riga ta zama babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, kuma a shirye take ta shiga tattaunawa da sauran ‘yan adawa bayan…
Read More
Gidauniyar Sidiya Charity ta fara horar da mata sana’o’in dogaro da kai

Gidauniyar Sidiya Charity ta fara horar da mata sana’o’in dogaro da kai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A wani gagarumin yunƙuri na bunƙasa rayuwar mata da inganta walwalar al’umma, Gidauniyar Sidiya Charity Foundation ta ƙaddamar da wani shiri na musamman na horas da mata sana’o’i da dabarun dogaro da kai, domin ba su damar samun hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma ƙarfafa matsayinsu a fannin tattalin arziki. An ƙaddamar da shirin ne cikin yanayi na farin ciki da fatan alheri, inda manyan baƙi, shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da sauran masu goyon bayan ayyukan ci gaba suka halarci taron domin nuna goyon bayansu ga wannan shiri. Da take jawabi a wajen taron,…
Read More
Katin zaɓe ginshiƙi ne na zaɓen nagartaccen zhugabanci da ci gaban al’umma – Maifata

Katin zaɓe ginshiƙi ne na zaɓen nagartaccen zhugabanci da ci gaban al’umma – Maifata

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An yi kira ga al’ummar jihar Kano da su gaggauta yin rajista da karɓar katin zaɓe domin tabbatar da cikakken shiga cikin harkokin dimokuraciyya da kuma zaɓen shugabanni nagari da za su inganta rayuwar jama’a. An bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kai kan muhimmancin katin zaɓe da Kwamitin Wayar da Kan Al’umma kan Rajistar da Karɓar Katin Zaɓe ya gudanar a Sakatariyar ƙaramar Hukumar Bichi, tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin aikin gayya daga ƙananan hukumomi takwas da suka haɗa da Bagwai, Bichi, Dawakin Tofa, Gwarzo, Rimin Gado, Shanono da Tsanyawa. Da yake jawabi…
Read More
Kungiyar ’yan kasuwar Bichi ta nemi tallafin jari domin bunƙasa kasuwar Kabiru Abubakar

Kungiyar ’yan kasuwar Bichi ta nemi tallafin jari domin bunƙasa kasuwar Kabiru Abubakar

Daga WAKILINMU Kungiyar 'Yan Kasuwar Zamani ta Bichi, wato Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited, ta yi kira ga gwamnati, shugabanni, masu ruwa da tsaki, manyan 'yan kasuwa da masu zuba jari da su haɗa hannu wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a ƙaramar Hukumar Bichi. Shugaban ƙungiyar 'Yan Kasuwar Zamani ta Bichin, Alhaji Abubakar Mazahimu Sale ne ya bayyana wannan kiran, bayan kammala gina kasuwar Kabiru Abubakar Ultra-Modern Market Bichi, ƙarƙashin jagorancin ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar. Ya ce, a wannan karon da ake shirin fara amfani da rukuni na biyu na shagunan da aka kammala, lokaci…
Read More
Sojoji sun ceto hakimin Farin Hawa daga hunnun ‘yan bindiga a Katsina

Sojoji sun ceto hakimin Farin Hawa daga hunnun ‘yan bindiga a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina‎‎Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto hakimin Farin Hawa da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, bayan da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi.‎‎A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 2 lokacin da maharan suka kai hari ƙauyen Farin Hawa inda suka sace hakimin, Alhaji Mubarak Sharin.‎‎Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirri, dakarunta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun bi sahun maharan, inda suka yi musayar wuta da su.‎‎A cewar sanarwar, an kashe ɗaya daga cikin maharan,…
Read More
Filato: An kashe ɗan bindiga ɗaya a yunƙurin kai hari na uku a makarantar NIPSS

Filato: An kashe ɗan bindiga ɗaya a yunƙurin kai hari na uku a makarantar NIPSS

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos Jami’an tsaro sun samu nasarar halaka wani ɗan bindiga ɗaya, cikin gungun wasu ýan bindiga da suka sake yunƙurin kai hari Cibiyar bada horo kan dabarun jagoranci ta ƙasa dake Kuru a kusa da Jos a karo na uku. Lamarin ya faru ne cikin daren Laraba, yayin da maharan suka gamu da turjiya daga haɗin gwiwar jami'an tsaro na soja da ýan sanda da ke cikin shirin ko-ta-kwana, a dalilin haka aka samu nasarar kashe ɗaya daga cikin maharan, wasu kuma suka tsere da raunin harbin bindiga a jikinsu. Mai magana da yawun cibiyar ta…
Read More
Kafa ‘yan sandan jihohi zai mayar da Nijeriya baya – CP ‘Singham’

Kafa ‘yan sandan jihohi zai mayar da Nijeriya baya – CP ‘Singham’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Kwamishinan 'Yan Sanda, Muhammad Wakili, wanda aka fi sani da CP Singham, ya bayyana rashin goyon bayansa ga shirin kafa 'yan sandan jihohi, yana mai cewa matakin zai iya mayar da Nijeriya ga irin matsalolin da suka sa aka soke tsarin a shekarar 1972. A wata hira da ya yi da NewsBreakNaija, Wakili ya ce Nijeriya ta taba gwada tsarin 'yan sandan jihohi a baya, amma an samu kalubale da suka hada da amfani da rundunar wajen cimma manufofin siyasa. Ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa kafa 'yan sandan jihohi…
Read More
‘Yan Nijeriya miliyan 1.57 sun yi rajistar katin zaɓe cikin makonni bakwai — INEC

‘Yan Nijeriya miliyan 1.57 sun yi rajistar katin zaɓe cikin makonni bakwai — INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa ta bayyana cewa aƙalla 'yan Nijeriya 1,565,873 ne suka kammala rajistar katin zaɓe zuwa ranar 26 ga watan Yuni. A cewar ƙididdigar da hukumar ta fitar a ranar Talata a Abuja, adadin ya kunshi mutum 620,933 da suka yi rajista ta yanar gizo, yayin da 944,940 suka kammala rajistar su a cibiyoyin rajista. Sai dai INEC ta ce wannan kididdiga ta wucin gadi ce, domin za a sake tantance bayanan kafin a fitar da adadi na ƙarshe ta hanyar tsarin tantance bayanan masu rajista. ƙididdigar ta nuna…
Read More