04
Jul
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da saura kusan watanni shida kacal a gudanar da babban zaɓen shekarar 2027, manyan jam’iyyun adawa a Nijeriya na ci gaba da fuskantar rikice-rikicen shugabanci da ƙararrakin kotu, lamarin da ke ƙara raunana su a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ke ƙarfafa tsarinta domin tunkarar zaɓen. Daga Jam’iyyar PDP, zuwa ADC, LP da kuma NDC, kusan dukkaninsu na fama da rarrabuwar kawuna, shugabanni masu taƙaddama, tarukan zaɓen fidda gwani daban-daban da kuma jerin shari’o’in kotu da suka dabaibaye harkokinsu. Lamarin ya jefa dubban ’yan takarar da aka tantance domin shiga zaɓen 2027 cikin…
