ukarofi

12546 Posts
APAK ta buƙaci a inganta tsarin tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai

APAK ta buƙaci a inganta tsarin tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Masana a fannin sadarwa, talla da aikin jarida sun buƙaci a inganta harkokin tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai domin bunƙasa sana'ar da kuma kawar da matsalolin da ke addabarta. An bayyana hakan ne yayin taron Advertising Practitioners Association of Kano (APAK) da aka gudanar na kwanaki uku a Kano. Masu jawabi sun tattauna hanyoyin da za a inganta ingancin tallace-tallace, daidaita amfani da harshen Hausa, da kuma tabbatar da ƙa'idojin aikin talla tsakanin Arewa da Kudancin Nijeriya. Taron ya samu halartar masana daga jami'o'i, kamfanonin talla da kafafen yaɗa labarai daban-daban. Daga cikin waɗanda suka…
Read More
Kotu ta ba da belin Sowore kan miliyan N200

Kotu ta ba da belin Sowore kan miliyan N200

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa fitaccen mai fafutukar kare haƙƙin al’umma kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, belin Naira miliyan 200 a shari’ar da ake da shi inda ake zargin sa da aikata laifin da ya shafi intanet. Hukumar ‘yan sandan farin kaya (SSS) ce ta gurfanar da editan jaridar Sahara Reporters bisa zargin cewa ya aikata laifin da ya saɓa da dokokin amfani da intanet bayan kiran shugaba Tinubu da “mai laifi” a wasu rubuce-rubucensa da ya wallafa a shafukan sada zumunta a bara. Mai shari’a Mohammed…
Read More
Shu’aibu Mungadi ya yaba wa Gwamnan Kebbi kan inganta tsaro

Shu’aibu Mungadi ya yaba wa Gwamnan Kebbi kan inganta tsaro

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Kamfanin Optimal Image Media Limited da gidan tababijin na 3rd Eye Africa TV, Alhaji Shu'aibu Mungadi, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamred (Dr.) Nasir Idris, bisa irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen inganta tsaro da kuma aiwatar da ayyukan ci gaba a faɗin jihar tasa. Alhaji Mungadi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da tawagar yaɗa labarai ta Gwamnatin Jihar Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu, Alhaji Yakubu Ahmed BK, ta kai masa ziyarar haɗin gwiwa a ofishinsa da ke Abuja. Ya ce, yadda gwamnatin Nasir Idris ta tunkari…
Read More
Tallafin gwamnati bai tsaya ga sana’ar ƙosai kaɗai ba – Remi Tinubu ta kare kalamanta

Tallafin gwamnati bai tsaya ga sana’ar ƙosai kaɗai ba – Remi Tinubu ta kare kalamanta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu, ta kare kalaman da ta yi kwanan nan game da tallafa wa ƙananan masu sana'o'i kamar ƙosai da gasasshen masara, tana mai cewa shirin tallafin Gwamnatin Tarayya bai tsaya ga masu sayar da ƙosai kaɗai ba, illa ya haɗa da nau'o'in ƙananan ’yan kasuwa daban-daban domin inganta rayuwarsu a ƙarƙashin manufar Sabunta Fata, wato Renewed Hope. Remi Tinubu ta bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ƙaddamar da ɗakin Taro na Abubakar Maje Haruna da ke Fadar Sarkin Hadejia a Jihar Jigawa, kwanaki kaɗan bayan da kalamanta kan masu sana'ar ƙosai,…
Read More
Sojoji 104 sun ɓace bayan harin Boko Haram a sansanin Borno

Sojoji 104 sun ɓace bayan harin Boko Haram a sansanin Borno

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata takardar sirri ta rundunar sojin Nijeriya ta nuna cewa an ayyana sojoji 104 a matsayin waɗanda suka gudu daga bakin aiki bayan wani hari da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka kai sansanin su da ke Jihar Borno. Rahoton ya ce, sojojin na aiki ne a Bataliya ta 162 ta Rundunar Sojin Ruwa da ƙasa (162 Amphibious Battalion) da ke kan hanyar Mandara–Buratai, inda aka kai harin a ranar 5 ga Yunin 2026. Bisa ga takardar da SaharaReporters ta ce ta samu, an bayyana cewa sojojin sun bar wuraren aikinsu ba tare da izini ba, tare da…
Read More
Nijeriya ta yi asarar rayuka 79,323, an yi garkuwa da mutane 34,773 cikin shekaru shida — ORFA

Nijeriya ta yi asarar rayuka 79,323, an yi garkuwa da mutane 34,773 cikin shekaru shida — ORFA

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani sabon bincike da Cibiyar Sa-Ido Kan ’Yancin Addini a Afirka (ORFA) ta gudanar ya bayyana cewa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025, an kashe mutane 79,323 tare da yin garkuwa da fararen hula 34,773 sakamakon hare-haren ta’addanci a Nijeriya. Rahoton mai taken "Four Times Boko Haram? How the World Misreads Nigeria’s Violence", wanda aka ƙaddamar a Jos ranar Talata, ya ce alƙaluman sun bayyana girman matsalar tsaro da kuma sauyin yanayin tashe-tashen hankula da ƙasar ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da Babban Manazarcin Bincike na ORFA, Frans Vierhout, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa…
Read More
Kebbi ta ƙaddamar da hukumar kula da jami’ar jihar bayan an shawo kan matsalolin makarantar

Kebbi ta ƙaddamar da hukumar kula da jami’ar jihar bayan an shawo kan matsalolin makarantar

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi. Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kaddamar da hukumar kula da jami'ar kimiyya da ƙere-ƙere ta Andullahi Fodio da ke Alieru, mallakin Jihar, yana mai imanin cewar wakilan hukumar na da hazaƙar maido da zaman lafiya a jami'ar da kuma ficen da tayi wurin karatu. A lokacin bikin, a Birnin Kebbi, Gwamna Idris yana mai yaƙinin cewar, shugaban hukumar wanda tsohon mataimakin shugaban gudanarwa ne na jami'ar, Farfesa Muhammad Abubakar Ka'oje, zai jagoranci sauran wakilan hukumar su cimma burin da aka kafa wannan makarantar ta ilmi mai zurfi don shi. Yayi bayanin cewar…
Read More
Duk ma’aikacin Katsina da ba shi da takarda za mu kore shi, in ya so ya je ya zaɓi Firauna – Dikko Raɗɗa

Duk ma’aikacin Katsina da ba shi da takarda za mu kore shi, in ya so ya je ya zaɓi Firauna – Dikko Raɗɗa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya ce gwamnatin sa ba ta ɗaukar jahili aiki a jihar. Gwamnan ya yi wannan magana ne a wajan bikin miƙawa malaman makarantun firamare da sakandire takardun kama aiki a Katsina. Ya mai da martani ne kan wasu ma'aikatan gwamnatin jihar da aka dakatar suka kai ziyara ga wani ɗan takarar gwamnan Jihar ƙarƙashin ɗaya daga cikin jam'iyar adawa. Ya ce gwamnati ta kafa kwamitin tantance ma'aikatan jihar Kuma sun gudanar da aikin su bisa ƙwarewa da adalci. "Saboda haka idan an dakatar da ma'aikaci daga aiki to sai…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ɗauki sabbin malaman firamare da sakandire 2,185

Gwamnatin Katsina ta ɗauki sabbin malaman firamare da sakandire 2,185

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki ƙarin malamai na makaratun firamare da na sakandire 2,185 da gwamna Raɗɗa ya ce wani cigaba ne aka samu a ƙoƙarin gwamnatin sa na sake gina harkar Ilimi a jihar. Gwamnan wanda ya ƙaddamar da bada takardar kama aiki ga malaman a Katsina ya bayyana ilimi a matsayin wani makami da zai canza rayuwar al'ummar" Zuba jari a harkar Ilimi tamkar zuba jari a makomar Jihar ne. Dikko ya ce a 2023 shekarar da suka hau kujerar mulki sun ɗauki malamai na firamare da sakandire 7,323 da malaman kiwon lafiya…
Read More
A duba kiran Sarkin Kano kan buƙatar sasancin ECOWAS da ƙasashen Sahel

A duba kiran Sarkin Kano kan buƙatar sasancin ECOWAS da ƙasashen Sahel

Kiran da Mai Martaba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II, ya yi ga Ƙungiyar Tarayyar ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) da ta sasanta da ƙasashen Nijar, Burkina Faso da Mali abin dubawar shugabannin yankin ne. Kira ne da aka yi da hikima da hangen nesa a daidai lokacin da yankin Afrika ta Yamma yake fuskantar manyan ƙalubalen tsaro, tattalin arziki da siyasa waɗanda ba a taɓa ganin irin su ba. Maimakon a bar saɓanin ra'ayi ya rikiɗe zuwa rarrabuwar kai ta dindindin, ya kamata ƙungiyar ECOWAS ta yi amfani da kowace dama wajen dawo da aminci da sake gina haɗin…
Read More