26
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar haɗin gwiwa ta sojojin Nijeriya a Arewa maso Gabas, wato Operation Hadin Kai, ta ce ta ceto mutane sama da 47, akasarinsu mata da yara, daga hannun ‘yan ta’addan ISWAP a jihar Borno. Jami’in yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Maiduguri. Ya ce an ceto mutanen ne a yankin Kangarwa, ƙaramar hukumar Kukawa, ranar 20 ga Yuni 2026, yayin wani samame da sojoji suka ƙaddamar ta ƙasa da sama kan sansanonin ISWAP a yankin tafkin Chadi. A cewarsa, ceton ya…
