ukarofi

12547 Posts
Jami’an kwastom 1,516 za su yi ritaya cikin shekaru biyu – NCS

Jami’an kwastom 1,516 za su yi ritaya cikin shekaru biyu – NCS

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta fitar da jerin jami’anta da za su yi ritaya a shekarun 2026 da 2027, inda jimillar jami’ai 1,516 za su bar aiki bisa tanadin dokokin aikin gwamnati ƙasar. Bayanan sun nuna cewa jami’ai 825 za su yi ritaya a shekarar 2026, yayin da wasu 691 za su yi ritaya a shekarar 2027. Wannan na daga cikin mafi girman adadin jami’an da za su fice daga aikin hukumar a lokaci guda a tarihin ta na baya-bayan nan. Takardun sanarwar ritayar, waɗanda Sashen Kula da Harkokin Ma’aikata da Ci Gabansu na Hukumar…
Read More
Gwamnatin Katsina ta musanta zargin ɗaukar nauyin ’yan bindiga zuwa aikin Hajji

Gwamnatin Katsina ta musanta zargin ɗaukar nauyin ’yan bindiga zuwa aikin Hajji

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta yi watsi da zargin da ke cewa ta dauki nauyin wasu shugabannin ’yan bindiga zuwa aikin Hajjin bana, tana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya, sharri da kuma yunƙurin yaudarar al’ummar jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Cikin Gida da Tsaro na Jihar Katsina, Dr. Nasiru Mu’azu Danmusa, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta mayar da martani kan ikirarin da wani mutum mai suna Bashir Kurfi ya yi a wata kafar yaɗa labarai cewa gwamnatin jihar ta dauki nauyin wasu shugabannin ’yan bindiga zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da…
Read More
‘Yan Nijeriya na cikin ƙunci – Rufai ya mayar wa Onanuga martani

‘Yan Nijeriya na cikin ƙunci – Rufai ya mayar wa Onanuga martani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Fitaccen mai gabatar da shirye-shirye na gidan talabijin na Arise TV, Rufai Oseni, ya soki Mai Bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, bisa kalamansa da ke nuna cewa rahotannin da ke bayyana tsananin yunwa da wahalar rayuwa a Nijeriya sun wuce gona da iri. Da yake magana a shirin The Morning Show na Arise Television a ranar Laraba, Rufai ya ƙalubalanci Onanuga da ya fito fili ya rantse cewa yawan ’yan Nijeriya da ke neman taimakon kuɗi daga gare shi bai ƙaru ba tun bayan…
Read More
Atiku ya caccaki Tinubu kan matsalar yunwa da rashin tsaro

Atiku ya caccaki Tinubu kan matsalar yunwa da rashin tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan wasu kalamai da suka nuna cewa kafafen yaɗa labarai ne ke ƙara nuna tsanantar matsalolin yunwa, wahalar rayuwa da rashin tsaro a ƙasar nan. Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce ’yan Nijeriya ba sa buƙatar ’yan jarida su gaya musu cewa suna cikin yunwa ko wahala domin suna fuskantar waɗannan matsaloli a rayuwarsu ta yau da kullum. Ya ce, “’Yan Nijeriya…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Cibiyar Nazarin Bayanai domin yaƙi da talauci

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Cibiyar Nazarin Bayanai domin yaƙi da talauci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wata sabuwar cibiyar tattara da nazarin bayanai mai suna National Poverty Intelligence Lab (NPIL), domin ƙarfafa yaƙi da talauci da kuma inganta tsarin tsara da aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa al’umma a faɗin Nijeriya. Ministan Harkokin Jin ƙai da Rage Talauci, Dr. Bernard Doro, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da wani taron kwanaki uku da aka gudanar a Abuja, wanda aka shirya domin tattauna hanyoyin fara aiki da sabon tsarin da kuma rawar da zai taka wajen rage talauci a ƙasar nan. Da yake jawabi a wajen taron,…
Read More
Nijeriya ta samu nasarar gano ma’adanai masu daraja a Kaduna

Nijeriya ta samu nasarar gano ma’adanai masu daraja a Kaduna

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta sanar da gano wani katafaren yankin ma’adanai na duniya a Jihar Kaduna, wanda ke ɗauke da ɗimbin ma’adanan platinum, zinari, nickel, tagulla, lithium da kuma wasu muhimman ma’adanai masu daraja da ake kira ‘Rare Earth Elements’. Ministan Ma’adanai na ƙasa, Dakta Dele Alake, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin buɗe taron zuba jari kan albarkatun ƙasa da makamashi na Afirka karo na biyar (AFNIS 2026), wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja. Taron, wanda aka gudanar ƙarƙashin taken “Afirka ɗaya, Manufa ɗaya Kan Albarkatun ƙasa”,…
Read More
Sarkin Kano ya naɗa Kachallan Kano, Mayana da Sarkin Arewa

Sarkin Kano ya naɗa Kachallan Kano, Mayana da Sarkin Arewa

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya naɗa sabbin masu sarauta a Masarautar Kano, ciki har da Alhaji Muhammadu ɗan'iya Ibrahim a matsayin Kachallan Kano, Alhaji Sa’adu Ali Ibrahim Matawalle a matsayin Mayanan Kano, da kuma Alhaji Sa’adu Giɗaɗo a matsayin Sarkin Arewan Kano. An gudanar da bikin naɗin sarautun ne a Fadar Sarkin Kano a ranar Juma’ar da ta gabata, inda aka halarta daga sassa daban-daban na jihar da ma ƙasa baki ɗaya. Da yake jawabi bayan naɗin nasa, sabon Kachallan Kano, Alhaji Muhammadu Daniya Ibrahim, ya bayyana farin cikinsa tare da…
Read More
Kasuwar Kurmi, Abbatuwa da Gidan Bos sun koka kan rashin tallafi daga gwamnatin Kano

Kasuwar Kurmi, Abbatuwa da Gidan Bos sun koka kan rashin tallafi daga gwamnatin Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Yayin da gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke cika shekaru uku a mulki, shugabannin wasu manyan kasuwanni a jihar sun bayyana buƙatunsu tare da neman ƙarin tallafi daga gwamnati domin magance matsalolin da suke fuskanta. Kasuwannin da suka bayyana damuwarsu sun haɗa da Kasuwar Kurmi, Kasuwar Abba Tuwa da kuma Kasuwar Gidan Bos, waɗanda ke daga cikin muhimman cibiyoyin kasuwanci a jihar Kano. Da yake zantawa da wakilinmu, Shugaban ƙungiyar ’Yan Kasuwar Kurmi, Alhaji Sulaiman Umar Sanka, ya ce duk da irin ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke yi, har…
Read More
EFCC za ta gurfanar da shugaban Miyetti Allah kan zargin badaƙalar kuɗi ta tallafa wa ta’addanci

EFCC za ta gurfanar da shugaban Miyetti Allah kan zargin badaƙalar kuɗi ta tallafa wa ta’addanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shirya gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin badakalar kuɗi da kuma tallafa wa ayyukan ta’addanci. Jaridar Punch ta rawaito cewa, EFCC ta shigar da tuhume-tuhume guda 12 a kansa, inda ta zarge shi da karɓar kuɗaɗen dala har miliyan 2.53 ta Amurka da ake zargin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka. A cewar hukumar, Bodejo ya karɓi kuɗaɗe daga tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sa’idu Abubakar, ba tare…
Read More
Kisan Maraban Jos da hatsarin al’adar ɗaukar doka a hannu

Kisan Maraban Jos da hatsarin al’adar ɗaukar doka a hannu

Kisan gilla da aka yi wa wata matar aure a garin Maraban Jos da ke ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna ya sake fito da wata babbar matsala da ta daɗe tana addabar al’ummomin Nijeriya – wato al’adar ɗaukar doka a hannu. Wannan mummunan lamari, wanda ya ƙare da banka wa wata mata wuta da ranta saboda zargin satar yara da ba a tabbatar ba, ya kamata ya zama abin da zai sa kowa ya tsaya ya yi tunani a kan inda al’umma ke dosa idan aka ci gaba da amincewa da irin wannan ɗabi’a mai haɗari. Rahotanni sun nuna…
Read More