ukarofi

12547 Posts
Kwalejin ilimi a Kwara ta dakatar da lakcara bisa dukan ɗaliban IJMB

Kwalejin ilimi a Kwara ta dakatar da lakcara bisa dukan ɗaliban IJMB

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mahukunta a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara sun dakatar da wani malami daga aiki bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna yana dukan wasu ɗalibai da ke karatun shiga jami’a na IJMB a harabar makarantar. A cikin bidiyon, an ga ɗaliban suna durƙushe tare da ɗaga hannayensu yayin da malamin ke dukan su da bulala a tafin hannu. Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi Allah-wadai da amfani da hukuncin duka a cibiyoyin ilimi. Shugaban ƙungiyar ɗaliban Nijeriya, Akinteye Babatunde,…
Read More
Muna gina sabuwar Nijeriya ne da kowa zai amfana – Tinubu

Muna gina sabuwar Nijeriya ne da kowa zai amfana – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta shimfiɗa tubalin Nijeriya sabuwa wadda za ta amfani kowa ta hanyar samar da ci gaba da walwalar al’umma. Tinubu, wanda shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya wakilta, ya bayyana haka yayin ƙaddamar da aikin gina tashoshin gefen hanya a Abuja. Ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara cikin shekaru uku da suka gabata sun kasance masu wahala, amma sun zama dole domin gyara tattalin arziki da bunƙasar ababen more rayuwa. A cewarsa, an fara ganin sakamakon gyare-gyaren ta hanyar gina hanyoyi, gadoji, layukan dogo…
Read More
’Yan Boko Haram na ba wa mayaƙan Bello Turji horo a Sakkwato

’Yan Boko Haram na ba wa mayaƙan Bello Turji horo a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Al’ummomi a gabashin Jihar Sakkwato sun bayyana damuwa bayan bullar rahotanni cewa jagoran ’yan bindigar nan, Bello Turji tare da mayakansa suna gudanar da atisayen dabarun yaƙi a wasu sassan Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Sun kuma yi zargin cewa Turji ya kafa sansanonin horas da mayakansa kan sarrafa sabbin makaman zamanin da ya mallaka suna masu zargin cewa wasu daga cikin mayakan sun hada da tsoffin ’yan ƙungiyar Boko Haram. Hukumomin tsaro sun ce ’yan ta’addan suna gudanar da atisayen ne a yankunan Bingabale, Bafarawa, Bargaja da Gebe, wadanda dukkansu ke cikin…
Read More
Rundunar ’yan sandan Oyo ta ƙaryata rahoton ceto mutanen da aka sace a Igbope

Rundunar ’yan sandan Oyo ta ƙaryata rahoton ceto mutanen da aka sace a Igbope

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta bayyana cewa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa an ceto wasu mutane biyu da aka sace a yankin Igbope ƙarya ce, marar tushe kuma mai yaudarar jama’a. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ƙarƙashin taken “Martanin Hukuma”, ta bayyana cewa bidiyon da ake yaɗawa da ke nuna wai an ceto waɗanda aka sace ba shi da inganci kuma ba a tabbatar da sahihancinsa ba. Sanarwar ta ce mutanen da aka sace, wato Misis Kuburat Omowumi da ɗanta, an yi garkuwa…
Read More
ACF ta ƙaddamar da kwamitin asusun waƙafi domin bunƙasa ilimi da ci gaban Arewa

ACF ta ƙaddamar da kwamitin asusun waƙafi domin bunƙasa ilimi da ci gaban Arewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF), ta ƙaddamar da Kwamitin Asusun Waƙafi da nufin inganta ilimi, bunƙasa tattalin arziki da kuma aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma a faɗin Arewacin Nijeriya. An naɗa tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Muhammad Dikko Abubakar, a matsayin shugaban kwamitin, inda aka ɗora masa alhakin jagorantar aiwatar da manufofi da tabbatar da cimma burin da aka kafa asusun domin su. Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin, Shugaban ACF kuma Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Dalhatu, ya yaba wa mambobin ƙungiyar bisa sadaukarwa, goyon baya…
Read More
Tinubu ya aike da ƙudirin kafa ‘yan sandan jihohi zuwa majalisar dattawa

Tinubu ya aike da ƙudirin kafa ‘yan sandan jihohi zuwa majalisar dattawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya aike wa majalisar dattawa da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki domin kafa rundunar ’yan sandan jihohi a faɗin ƙasar nan. ƙudirin na neman yin gyare-gyare ga wasu sassan kundin tsarin mulkin shekarar 1999 domin samar da sahihin tsarin doka da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yan sandansu. Matakin ya biyo bayan kiraye-kirayen da shugaban ƙasar ya dinga yi na a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin bai wa jihohi damar taka rawar gani wajen samar da tsaro a yankunansu. A watan Fabrairun wannan shekara, Tinubu ya…
Read More
An kashe ‘yan ta’adda da dama a Kebbi

An kashe ‘yan ta’adda da dama a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Rahotanni daga garin Kangiwa da ke jihar Kebbi sun bayyana cewa da sanyin safiyar Juma'ar nan an yi bata-kashi tsakanin sojojin Nijeriya da waɗansu ƴan bindiga da a ke sa ran mayaƙan lakurawa ne inda sojojin Nijeriya suka sami galaba kan su suka kashe da dama daga cikin lakurawan yayin da sauran suka gudu da raunuka.Malam Yusuf wani mazauni garin na Kangiwa ya shaida wa waƙilin blueprint Manhaja da cewa kwanakin nan suna ganin mayaƙan suna shawagi a yankin ba dare ba rana a kan babura ɗauke da mutane biyu ko uku da su ke…
Read More
Gidauniyar jinƙai ta Ɗahiru Mangal ta fara tantance masu lalurar gwaiwa a Katsina

Gidauniyar jinƙai ta Ɗahiru Mangal ta fara tantance masu lalurar gwaiwa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina ‎Gidauniyar jin ƙai ta Ɗahiru Bara’u Mangal Foundation ƙarƙashin jagorancin Alh. Ɗahiru Mangal ta fara gudanar da tantance masu lalurar gwaiwa da ƙaba a Katsina.‎Gidauniyar ta fara gudanar da tantance masu fama da wadannan lalura a babban asibitin Katsina (General Hospital).‎‎Da yake bayyana ma manema labarai yadda aikin ke gudana, ɗaya daga cikin ’yan kwamitin amintattu na gidauniyar Alhaji Hussaini Kabir, ya bayyana cewa" Wannan aiki ana gudanar da shi ne ƙarƙashin wannan gidauniya ta Mangal Foundation shekaru da dama kuma kyauta .‎‎Hussaini ya ƙara da cewa aikin yana kasancewa ne lokaci zuwa lokaci. "Kamar…
Read More
Ta’addanci: Sarki Salman ya raba wa ‘yan gudun hijira 4,399 kayan abinci a Kebbi

Ta’addanci: Sarki Salman ya raba wa ‘yan gudun hijira 4,399 kayan abinci a Kebbi

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi Cibiyar gudanarwa ta Sarki Salman na ƙasar Saudiyya, ta rarraba kayayyakin abinci ga gajiyayyu da 'yan gudun hijira, 4,399 waɗanda 'yan ta'adda suka kora daga garuruwansu, da ke Jihar Kebbi. Abincin ya ƙunshi hatsi da shinkafa da taliya da tumatur na gwangwani da man-girki da kuma gishiri mai gina jiki. A sa'ilin taron, darakta-janar ta hukumar bada agaji ta ƙasa, NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta bayyana cibiyar gudanarwa ta Sarki Salman, a matsayin 'ginshiƙin jin-ƙai' da ke aiki tare da Najeriya, wurin bayar da agaji ga gajiyayyu da waɗanda bala'oi suka rutsa da…
Read More
Ban ga tsananin yunwar da ‘yan Nijeriya ke magana a kai ba – Onanuga

Ban ga tsananin yunwar da ‘yan Nijeriya ke magana a kai ba – Onanuga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce ba ya ganin irin matsanancin yunwar da wasu ‘yan Nijeriya ke korafi a kai, yana mai cewa manufofi da gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatin tarayya na fara haifar da amfani ga jama’a. Jaridar TheCable ta rawaito cewa, da yake magana a tashar Arise TV, Onanuga ya ce an ƙirƙiri tunanin cewa yunwa ta mamaye ƙasar tun bayan hawan gwamnatin Tinubu, yana mai cewa mutane da dama na cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati. Ya bayyana cewa yana tambayar ma’aikatansa halin da suke…
Read More