ukarofi

12546 Posts
’Yan sanda sun bankaɗo shagon ajiye makaman ’yan fashi a Abuja

’Yan sanda sun bankaɗo shagon ajiye makaman ’yan fashi a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta bayyana cewa wani shagon sayar da kayan sawa da ke unguwar Jabi a Abuja na da alaƙa da wata ƙungiyar masu fashi da makami da ake zargi da adana bindigogi da sauran muggan makamai da suke amfani da su wajen aikata laifuka a Suleja da wasu yankunan da ke makwabtaka da ita. Bayanan da rundunar ta fitar sun nuna cewa binciken ya fara ne bayan kama wani mutum mai suna Bitrus James, wanda aka cafke yayin da yake ƙoƙarin tserewa da wata babur da aka sace bayan wani harin fashi…
Read More
Nijeriya za ta karɓi mafi girman kamfanin sarrafa ƙarafa mai amfani da hasken rana a Afirka

Nijeriya za ta karɓi mafi girman kamfanin sarrafa ƙarafa mai amfani da hasken rana a Afirka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin African Industries Group ya sanar da shirinsa na kafa mafi girman kamfanin sarrafa ƙarafa da ke amfani da makamashin hasken rana a yankin Afirka da ke Kudu da Hamadar Sahara, bayan da Gwamnatin Jihar Neja ta ware masa fili mai faɗin hekta 500 domin gudanar da aikin. Shugaban kamfanin, Raj Gupta, ne ya bayyana hakan yayin bikin aza harsashin ginin aikin da kuma miƙa filin ga Kamfanin ƙarafa na Abuja Steel Mills Limited, reshen kamfanin African Industries Group, a wani taro da aka gudanar a Abuja a ƙarshen mako. Gupta ya ce wannan tallafi da…
Read More
JAMB ta soke shirye-shiryen digiri a kwalejojin ilimi bayan maida NCE hanyar shiga

JAMB ta soke shirye-shiryen digiri a kwalejojin ilimi bayan maida NCE hanyar shiga

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta ƙasa (JAMB) ta sanar da kawo ƙarshen ɗaukar ɗalibai cikin shirye-shiryen digiri da Kwalejojin Ilimi ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar jami’o’i, lamarin da ya kawo babban sauyi a tsarin horas da malamai a Nijeriya. Sabon tsarin ya tanadi cewa takardar shaidar karatu daga makarantar horar da malamai , wato Nigeria Certificate in Education (NCE) ce kaɗai za ta kasance hanyar shiga Kwalejojin Ilimi daga shekarar karatu ta 2026/2027. An bayyana wannan mataki ne a cikin sabbin ƙa’idojin rajistar NCE da ND Agric da ofishin Shugaban Hukumar JAMB ya…
Read More
NAHCON ta kammala jigilar Alhazan Nijeriya

NAHCON ta kammala jigilar Alhazan Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar alhazai ta Nijeriya NAHCON ta ce a hukumance ta kammala jigilar alhazan Nijeriya sama da 38,000 da suka tafi ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2026. Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NAHCON, Hajiya Fatimah Usara ta fitar ta ce ana sa ran jirgin ƙarshe ɗauke da alhazai daga Jihar Zamfara zai iso Nijeriya a ranar Talata. Usara ta ce kammala jigilar ya kawo ƙarshen ayyukan Hajjin 2026. Sai dai ta ce alhazan Nijeriya 12 a halin yanzu suna jinya a asibitoci daban-daban na ƙasar Saudiyya saboda wasu matsalolin…
Read More
Nijar ta fice daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya

Nijar ta fice daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta miƙa buƙatarta ta ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICCC, a hukumance. Wannan na zuwa ne watanni tara bayan sanar da aniyarta ta barin kotun. Nijar ta sanar da aniyarta ta ficewa daga kotun a watan Satumban bara tare da ƙasashen Mali da Burkina Faso. Kotun mai hedikwata a birnin Hague ta ce ta karɓi buƙatar ficewar Nijar daga cikinta a hukumance a ranar 18 ga watan Yuni, 2026, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito. ICC ta ce ficewar ƙasar ba za…
Read More
Yadda muka ɗauki matakai domin kare yankin Kano ta Arewa daga harin ‘yan bindiga – Yahaya Bagobiri

Yadda muka ɗauki matakai domin kare yankin Kano ta Arewa daga harin ‘yan bindiga – Yahaya Bagobiri

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Alhaji Yahaya Umar Bagobiri, jigon ɗan siyasa a jihar Kano ɗan asalin Faruruwa a ƙaramar Hukumar Shanono, ya bayyana cewa haɗin kan al’umma da jami’an tsaro shi ne sirrin samun nasara kan ‘yan bindiga a yankin Arewacin Kano. Bagobiri ya ce matsalar tsaro ta wuce wuri ɗaya, “Nijeriya ce gaba ɗaya. Nan da can abubuwa na faruwa, sai dai addu’a.” Ya ce tun a watan Afrilu 2022, da suka ga ta’addanci ya soma shigowa yankin Kano daga yankin Gulbin Karaɗuwa har zuwa cikin Faruruwa, sai suka zauna da masu ruwa da tsaki. “Mun haɗa Dagatai,…
Read More
’Yan sanda a Bauchi sun ceto yara mata biyu da aka sace daga Taraba

’Yan sanda a Bauchi sun ceto yara mata biyu da aka sace daga Taraba

Daga MU'AZU HARDAWA a Bauchi Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta yi nasarar ceto wasu yara mata biyu masu shekaru 13 da aka sace daga Jihar Taraba, tare da kama wasu matasa biyu da ake zargi da hannu wajen aikata laifin a ƙaramar Hukumar Kirfi ta jihar. A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar, ya bayyana cewa an ceto yaran ne bayan wani mutum mai shekaru 57 daga ƙauyen Fangari da ke ƙaramar Hukumar Bali a Jihar Taraba ya kai rahoton ɓacewarsu ga jami’an tsaro a ranar 10 ga Maris, 2026.…
Read More
Rikicin cikin gida ya sa gwamnatin Bauchi ta rufe masallacin Ibadurrahman

Rikicin cikin gida ya sa gwamnatin Bauchi ta rufe masallacin Ibadurrahman

Daga MU'AZU HARDAWA a Bauchi Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayar da umarnin rufe Masallacin Ibadurrahman da ke Unguwar Shingen Abba a cikin garin Bauchi sakamakon rikicin da ya daɗe yana ci gaba tsakanin kwamitin gudanarwar masallacin da limaminsa. Da yake zantawa da manema labarai bayan kulle masallacin, Kwamishinan Hisba na Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi, Barrista Aminu Balarabe Isah, ya ce an ɗauki matakin ne bisa umarnin gwamnatin jihar da kuma sahalewar kotu domin kauce wa yiwuwar tashin hankali da ka iya janyo asarar rayuka ko jikkata mutane. Ya bayyana cewa rikicin ya kwashe kusan shekaru uku yana gudana…
Read More
JIBWIS na shirin kai Sheikh Masussuka kotu

JIBWIS na shirin kai Sheikh Masussuka kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata sabuwar takarda mai ɗauke da wasu zarge-zarge da gargaɗi daga Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Jihar Katsina ta jawo hankalin al’umma bayan da lauyoyin ƙungiyar suka aika da ita ga wani malamin addinin Musulunci mai suna Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka, mazaunin garin Dutsinma a jihar ta Katsina. Takardar, wacce aka rubuta a ranar 15 ga Yuni, 2026, ta fito ne daga Imtiyaz Law Chambers, lauyoyin da ke wakiltar JIBWIS, inda suka bayyana damuwarsu kan irin wa’azuzzuka da koyarwar da malamin ke yi, waɗanda suka ce suna haifar da cece-kuce a…
Read More
Kwalejin ilimi a Kwara ta dakatar da lakcara bisa dukan ɗaliban IJMB

Kwalejin ilimi a Kwara ta dakatar da lakcara bisa dukan ɗaliban IJMB

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mahukunta a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara sun dakatar da wani malami daga aiki bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna yana dukan wasu ɗalibai da ke karatun shiga jami’a na IJMB a harabar makarantar. A cikin bidiyon, an ga ɗaliban suna durƙushe tare da ɗaga hannayensu yayin da malamin ke dukan su da bulala a tafin hannu. Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi Allah-wadai da amfani da hukuncin duka a cibiyoyin ilimi. Shugaban ƙungiyar ɗaliban Nijeriya, Akinteye Babatunde,…
Read More