ukarofi

12546 Posts
PRP ta musanta zargin Kwankwaso ya saye fom ɗin takara 69

PRP ta musanta zargin Kwankwaso ya saye fom ɗin takara 69

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar PRP ta musanta zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya saye fom ɗin takara 69 na jam’iyyar. A ranar Lahadi Shugaban Dandalin Masu Ruwa da Tsaki na Arewa maso Yamma na jam’iyyar, Abdulkaɗir Musa Guza, ya yi zargin cewa Kwankwaso ya saye dukkan fom ɗin takarar PRP domin “ƙwace” jam’iyyar tare da tsayar da mabiyansa takara a cikinta. Sai dai Sakataren PRP na jihar, Alhaji Musa Maigari, ya shaida wa manema labarai a Kano a ranar Litinin cewa an riga an…
Read More
Ba a samun mulki a ɓagas sai da gwagwarmaya – Wike ga ’yan PDP

Ba a samun mulki a ɓagas sai da gwagwarmaya – Wike ga ’yan PDP

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja kuma jagoran jam’iyyar PDP na ƙasa, Nyesom Wike, ya buƙaci mambobin jam’iyyar su shirya tsaf domin fafatawar siyasa mai zafi da ke tafe gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Wike ya bayyana cewa ba a bayar da mulki kyauta a siyasa, sai an yi gwagwarmaya da jajircewa kafin a samu nasara. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron Kwamitin Zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 109 na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Abuja. A jawabinsa, tsohon gwamnan Jihar Ribas ya yi kira ga ’yan takarar jam’iyyar da kada su…
Read More
IHRC-RFT ta nemi a gaggauta tabbatar da adalci kan kisan Malama Ummulkhairi a Kaduna

IHRC-RFT ta nemi a gaggauta tabbatar da adalci kan kisan Malama Ummulkhairi a Kaduna

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Kare Haƙƙin Bil’Adama ta ƙasa da ƙasa, wato International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT) Nigeria, ta bayyana matuƙar alhini, damuwa da kuma Allah-wadai kan mummunan kisan gillar da aka yi wa Malama Ummulkhairi a yankin Mararaban Jos da ke ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, bayan wasu mutane sun zarge ta da wani laifi tare da ɗaukar doka a hannunsu ba tare da an gabatar da ita gaban hukumomin da suka dace ko kotu ba. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata Amb. Abdullahi Bakoji Adamu, Daraktan ƙasa na IHRC-RFT ya sanya…
Read More
Hauhawar farashi na durƙusar da dubban kasuwanci a Nijeriya – ASBON

Hauhawar farashi na durƙusar da dubban kasuwanci a Nijeriya – ASBON

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shekaru uku bayan gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin samar da asusun tallafi na Naira biliyan 200 domin rage tasirin sauye-sauyen tattalin arziki ga masana’antu da ƙananan ’yan kasuwa, masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa har yanzu yawancin waɗanda aka yi niyyar tallafawa ba su amfana da shirin ba. A lokaci guda kuma, miliyoyin ƙananan kasuwanci sun durƙushe tare da rufe ƙofofinsu. Kungiyar Masu ƙananan Kasuwanci ta Nijeriya (ASBON) ta ce kusan ƙananan kasuwanci miliyan biyu ne suka rufe tsakanin shekarun farko uku na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sakamakon cire tallafin man fetur, sauye-sauyen tsarin…
Read More
Gwamnatin Katsina ta samu tallafin Dala miliyan takwas don inganta rayuwar mata

Gwamnatin Katsina ta samu tallafin Dala miliyan takwas don inganta rayuwar mata

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta sake samu tallafin Dalar Amurka Miliyan 8 ($8m) daga bankin duniya domin shirin Nigeria for Women. Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na faɗaɗa shirin Nigeria for Women (NFWP) zuwa dukkanin ƙananan hukumomi 34 na jihar, bayan da bankin duniya ya amince da bayar da ƙarin tallafin da ya kai tsakanin dala miliyan 6 zuwa miliyan 8 domin aiwatar da shirin a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar jami'ain bankin duniya, ma’aikatar harkokin mata ta tarayya da kuma masu…
Read More
Gwamnati ta umarci DSS, EFCC da ’yan sanda su daƙile ɓoye gas da fasaƙwairinsa

Gwamnati ta umarci DSS, EFCC da ’yan sanda su daƙile ɓoye gas da fasaƙwairinsa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Tarayyar Nijeriya ta kira wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da ya haɗa da jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) da kuma Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, domin nemo mafita ga matsalar ɓoye iskar gas na girki (LPG) da kuma karkatar da shi zuwa ƙasashen maƙwabta. Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA) ce ta ce, an shirya taron ne bayan hauhawar farashin gas ɗin girki da aka samu a baya-bayan nan, tare da…
Read More
Hukumomin NASENI da REA sun ƙulla yarjejeniyar ƙera na’urorin solar na gida

Hukumomin NASENI da REA sun ƙulla yarjejeniyar ƙera na’urorin solar na gida

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Nijeriya na ci gaba da yunƙurin rage dogaro da kayayyakin makamashin hasken rana da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, bayan Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani wajen samar da wata muhimmiyar yarjejeniya tsakanin Hukumar Kula da Bincike da Bunƙasa Injiniyanci ta ƙasa (NASENI) da Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (REA) domin fara ƙera kayayyakin solar a cikin ƙasa. An rattaba hannu kan wannan yarjejeniya ne a Abuja a ranar Litinin, inda aka amince da haɗin gwiwar da zai ƙara haɓaka samar da na’urorin hasken rana, batir, inverter da sauran muhimman kayan aikin…
Read More
Sabuwar ɓarkewar zazzaɓin Lassa ta halaka babban likita a Benuwe

Sabuwar ɓarkewar zazzaɓin Lassa ta halaka babban likita a Benuwe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani babban likita da ke aiki da ƙungiyar APIN a ƙaramar Hukumar Konshisha ta Jihar Benuwe ya rasu bayan ya kamu da cutar zazzaɓin Lassa. Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jinƙai na Jihar Benuwe, Dakta Paul Ejeh-Ogwuche, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin a Makurdi, inda ya bayyana cewa ma’aikatar ta fara bin diddigin waɗanda suka yi hulɗa da marigayin tare da ƙarfafa matakan sa ido domin daƙile yaɗuwar cutar. A cewar kwamishinan, marigayin ya shafe sama da makonni biyu yana fama da rashin lafiya kafin yanayinsa ya tsananta. Ya ce, mutuwar likitan ta…
Read More
Shigo da fetur ya ragu zuwa ƙasa da tiriliyan N90 sakamakon matatun gida – Gwamnati

Shigo da fetur ya ragu zuwa ƙasa da tiriliyan N90 sakamakon matatun gida – Gwamnati

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kuɗin da Nijeriya ke kashewa wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje ya ragu ƙwarai daga kusan Naira tiriliyan 2.3 a farkon shekarar 2025 zuwa ƙasa da Naira tiriliyan 90 a shekara guda bayan haka. Wannan ci gaba, a cewar gwamnati, ya samo asali ne daga bunƙasar matatun mai na cikin gida da kuma ƙara yawan man da ake tacewa a ƙasar. Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Makamashi, Olu Verheijen, ce ta bayyana hakan yayin taron Ranar Makamashi na ƙungiyar Kasuwancin Nijeriya da Birtaniya na shekarar 2026 da…
Read More
Karfin gwamnati ya zarce na kowace ƙungiyar ’yan bindiga – Gwamnan Zamfara

Karfin gwamnati ya zarce na kowace ƙungiyar ’yan bindiga – Gwamnan Zamfara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada matsayar gwamnatin sa na ƙin shiga tattaunawa ko ƙulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga, yana mai cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da zaman sulhu da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ba. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, wadda aka saurara a Kaduna, inda ya ce gwamnatinsa na ci gaba da goyon bayan dabarar yaƙi da rashin tsaro ta hanyar amfani da jami’an tsaro maimakon tattaunawa da masu aikata laifuka. Dauda Lawal ya ce, ba abin yarda ba…
Read More