28
Jun
Wani lamari mai ban mamaki ya faru a ƙasar Kanada inda wani mutum ya tarar da wani tsuntsu matacce a harabar gidansa tare da wani kifi a gefensa. Da farko dai mutumin ya kasa fahimtar abin da ya faru, domin babu ruwa ko kogi a kusa da wurin. Bayan masana sun gudanar da bincike, sun bayyana cewa wataƙila wani babban tsuntsu mai farauta ne ya kama kifin daga ruwa domin ya ci. Sai dai yayin da yake shawagi a sama, kifin ya kuɓuce daga bakinsa ya faɗo ƙasa da ƙarfi. Ana zargin cewa kifin ya bugi wani tsuntsu da ke…
