06
Oct
Cibiyar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce ta ƙara tsaurara matakan sa ido da shirin ko-ta-kwana bayan gwamnatin Kenya ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola da aka shigo da ita daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC). Cutar dai ta samo asali ne daga kwayar Bundibugyo virus, kuma NCDC na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki a yankin. A cewar sanarwar NCDC ta ranar 6 ga Oktoba 2026, wanda ya kamu da cutar ɗan ƙasar Kenya ne da ya taɓa zama a Kongo. Ya yi tafiya ta hanya daga Kongo zuwa Kampala a Uganda,…
