06
Oct
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta naɗa Muhammad Saifuddeen Yakubu Musa sabon babban kwamandan Hisbah a Jihar. Naɗin ya biyo bayan murabus da Dr Aminu Usman (Abu Amar) tsohon shugaban hukumar ya yi. Sabon kwamandan ɗa ne ga Sheikh Yakubu Musa Hassan sautus Sunnah shugaban ƙungiyar Izala a Jihar Katsina. Mutane na ganin murabus da Dr Aminu Usman ya yi bai zo da mamaki ba domin tun a watanni baya ya bi bangaren Ibrahim Kabir Masari mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa. Ibrahim Kabir Masari da Dikko Raɗɗa waɗanda duka ya'yan Jam'iyar APC a Jihar…
