ukarofi

12456 Posts
Hadiza Liman ta fice daga APC zuwa NDC a Zamfara

Hadiza Liman ta fice daga APC zuwa NDC a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wata jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, Hajiya Hadiza Liman, ta sanar da ficewarta daga Jam'iyyar APC zuwa Jam'iyyar National Democratic Congress (NDC). Hajiya Hadiza ta sanar da ficewarta yayin da take magana da manema labarai a gidanta da ke Gusau. A cewarta, ita da magoya bayanta sama da mutum 10,000 daga ƙananan hukumomi 14 sun bar APC sun koma NDC. Ta nuna rashin gamsuwarta da abin da ta bayyana a matsayin sakacin Gwamna Dauda Lawal, tana mai cewa sun ba da cikakken goyon bayansu lokacin da suke cikin Jam'iyyar Peoples…
Read More
Shettima ya ƙaddamar da asusun tallafin zuba jari ga mata 40,000 a Katsina

Shettima ya ƙaddamar da asusun tallafin zuba jari ga mata 40,000 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Fiye da mata 40,000 a Jihar Katsina za su amfana da tallafin jari domin faɗaɗa sana’o’insu da ƙarfafa tattalin arzikinsu Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ne ya ƙaddamar da rabon asusun zuba jari na al’umma (CIF) ƙarƙashin shirin Nigeria for Women Programme Scale-Up (NFWP-SU) a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina. Ya ce shirin wani jari ne ga ƙwarewa, sana’o’i da damar tattalin arzikin mata. Shettima ya ce sama da mata 40,000 ne za su samu jari bayan sun cika sharuɗan cancanta tare da nuna ƙwazo a tsarin ajiyarsu da ayyukan…
Read More
2027: Magoya bayan NDC sun mamaye Lafia domin nuna goyon baya ga Obi da Kwankwaso

2027: Magoya bayan NDC sun mamaye Lafia domin nuna goyon baya ga Obi da Kwankwaso

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Jam'iyyar Nigeria Democratic Congress, NDC, a ranar Asabar ta gudanar da wani babban gangamin nuna goyon baya mai ɗimbin yawa a birnin Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa domin tara goyon baya ga Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso da sauran 'yan takarar jam'iyyar gabanin babban zaɓen 2027. Gangamin wanda jam'iyyar ta bayyana a matsayin gangamin mutum miliyan ɗaya, ya fara ne daga Lubuna House da ke kan titin Sabuwar Kasuwa kuma ya bi ta manyan tituna a Lafiya kafin ya kare a wuri guda. Taron ya jawo hankalin mambobin jam'iyya da magoya baya daga…
Read More
Shugaban hukumar gudanarwa na hukumar alhazai a Katsina ya ajiye muƙamin sa

Shugaban hukumar gudanarwa na hukumar alhazai a Katsina ya ajiye muƙamin sa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban hukumar gudanarwa na hukumar alhazai a Jihar Katsina Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai ya ajiye muƙamin sa. A wata takarda da ya sanyawa hannu kuma ya aikewa sakataran gwamnatin Jihar Katsina,duk da cewa babu wani bayani game da wannan mataki da ya ɗauka,Alhaji Bature ya nuna godiyarsa ga gwamna Dikko Raɗɗa da ya bashi damar hidimtawa jihar. Tsohon shugaban hukumar alhazai ya bayyana cewa zamansa a hukumar ya bashi damar sadaukar da kansa wajen bautawa jihar sa da yace haka ma yana miƙa godiya ga gwamnatin Jihar Katsina. Sarkin Alhazai ya kuma bayyana jin…
Read More
Mutanen Nasarawa sun yaba wa Ibrahim Adamu bisa jajircewarsa wajen aiki

Mutanen Nasarawa sun yaba wa Ibrahim Adamu bisa jajircewarsa wajen aiki

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hukumar da ke kula da asibitoci da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta Jihar Nasarawa (NASPHFIRA), ta taya Babban Sakatare na Ma'aikatar Lafiya, Dr. Ibrahim Adamu Alhassan murna a ranar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ta yaba da jajircewarsa da sadaukar da kai wajen cigaban jihar, musamman a fannin lafiya. Yabon ya zo ne a cikin saƙon taya murna da babbar sakataren hukumar, Dr. Nana Awaya Emeribe, ta aiko a madadin shugabanci da ma'aikatan hukumar. Suma da suke zantawa da wakilinmu a yayin bikin ranar haihuwar babban sakataren a Lafia, wasu masu ruwa da tsaki…
Read More
Jami’in NDLEA ya nutse a ruwa yayin ƙoƙarin kama dillalin ƙwaya

Jami’in NDLEA ya nutse a ruwa yayin ƙoƙarin kama dillalin ƙwaya

Wani jami’in Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ya rasa ransa a yayin da yake ƙoƙarin kama wani dillalin miyagun ƙwayoyi da ya tsere bayan an kama shi. Jami’in ya rasu ne bayan da ya nutse a kogin Ethiope a yayin da yake bin wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a garin Obiaruku da ke ƙaramar Hukumar Ukwuani ta Jihar Delta a ƙarshen mako. Shaidu sun ce jami’an NDLEA da ke yankin sun kama wani wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, a yayin da yake safarar haramtattun ƙwayoyi, sannan suka nufi wurin gadar kogin…
Read More
Karancin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya na kawo cikas ga cigaba – Bagudu

Karancin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya na kawo cikas ga cigaba – Bagudu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu, ya ce tattalin arzikin Nijeriya har yanzu bai kai bunƙasar da zai iya biyan manyan buƙatun cigaban ƙasar ba. Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Majalisar ƙasa, inda ya ce idan Nijeriya ba ta ɗauki matakan da suka dace wajen bunƙasa tattalin arzikinta ba, ƙasar za ta ci gaba da kasa cimma muradun da ’yan ƙasa ke sa ran gwamnati za ta cika. Bagudu ya bayyana hakan ne yayin wani taron horas da ’yan jarida kan harkokin kasafin kuɗi, inda ya ce Nijeriya na daga…
Read More
Kano ta gaza bayyana kuɗaɗen shigar ƙananan hukumomi yayin da na jiha suka ninka

Kano ta gaza bayyana kuɗaɗen shigar ƙananan hukumomi yayin da na jiha suka ninka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jihar Kano ta kasa bayyana adadin kuɗaɗen shiga da ƙananan hukumominta 44 suka samar aƙalla sau uku cikin rahotannin baya-bayan nan na Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS), duk da cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida na gwamnatin jihar sun kusan ninka sau uku tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025. Wani kwatanci tsakanin bayanan NBS da na gwamnatin jihar ya nuna hakan. Bayanan NBS sun nuna cewa Kano na cikin jihohi 16 da suka bayar da rahoton cewa ƙananan hukumominsu ba su samu ko sisin kwabo na kuɗaɗen shiga a shekarar 2023 ba. Sauran jihohin sun haɗa da…
Read More
Biyan bashin cikin gida ya ragu zuwa tiriliyan N2.14 a tsakiyar 2026 – DMO

Biyan bashin cikin gida ya ragu zuwa tiriliyan N2.14 a tsakiyar 2026 – DMO

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Biyan kuɗaɗen bashin cikin gida da Nijeriya ke bi ya ragu da kusan Naira tiriliyan ɗaya a tsakiyar shekarar 2026, inda ya koma Naira tiriliyan 2.14 daga Naira tiriliyan 3.14 da aka biya a farkon shekarar. Bayanan Hukumar Kula da Bashin ƙasa (DMO) sun nuna cewa raguwar ta kai kashi 31.8 cikin 100 idan aka kwatanta da lokutab baya, duk da cewa jimillar bashin gwamnati ta ƙaru a cikin wannan lokaci. Bayanan DMO sun nuna cewa kuɗaɗen ruwa da na haya sun kai Naira tiriliyan 1.98 daga cikin jimillar kuɗin hidimar bashin da aka biya a…
Read More
2030: Gwamnatin Tarayya na shirin samar da kashi 70 na muhimman magunguna a gida

2030: Gwamnatin Tarayya na shirin samar da kashi 70 na muhimman magunguna a gida

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin samar da aƙalla kashi 70 cikin 100 na muhimman kayayyakin kiwon lafiya a cikin gida nan da shekarar 2030, a wani mataki na ƙarfafa wadatar magunguna da rage dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje. Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Iziaƙ Salako, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Legas, yayin da yake buɗe bikin baje kolin masana’antun magunguna na Nijeriya karo na takwas, wanda ƙungiyar Masu Harhaɗa Magunguna ta ƙungiyar Masana’antun Nijeriya (PMG-MAN) ta shirya. Taken taron shi ne “Bunƙasa Masana’antu a Yankin Afirka: ƙarfafa Ikon Afirka…
Read More