ukarofi

12456 Posts
Fiona Fullerton: ‘Yar Kaduna da ta zama jarumar James Bond

Fiona Fullerton: ‘Yar Kaduna da ta zama jarumar James Bond

Daga AISHA ASAS Mai karatu, barkanmu da sake kasancewa da ku a shafin Taurari na jarida mai farin jini, Blueprint Manhaja, shafin da ke kawo muku labaran fitattun jarumai da abubuwan da suka shafi harkar nishaɗantarwa, tare da waiwayar rayuwarsu da abubuwan da suka taimaka wajen kai su inda suke a yau. A wannan makon, shafin Taurari ya lalubo muku labarin Fiona Fullerton, jarumar da aka haifa a Ungwan Sarki da ke Kaduna, wadda tun tana yarinya ta fara taka rawa a fina-finai, kafin daga bisani ta shiga duniyar James Bond. Amma bayan shaharar da ta samu a matsayin Bond…
Read More
Pantami ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na PDP a Gombe

Pantami ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na PDP a Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar PDP na neman tikitin takarar Gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027. Pantami ya samu nasara a zaɓen da aka gudanar a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar, inda ya samu kuri’u 2,054, yayin da Khamisu Ahmed Mailantarki ya samu kuri’u 389, sannan Usman Aliyu Garry ya samu kuri’u 112. An sanar da sakamakon ne a sakatariyar PDP ta jihar Gombe. An gudanar da sabon zaɓen ne a ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta…
Read More
Ban taɓa zama ɗan jam’iyyar PDP ba – Akpabio

Ban taɓa zama ɗan jam’iyyar PDP ba – Akpabio

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya musanta cewa ya taba kasancewa mamba a jam’iyyar PDP. Akpabio ya bayyana hakan ne a zaman majalisar na ranar Talata, yayin da Sanatoci ke tattauna ƙudirin girmama marigayi tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Ibrahim Idris. Sanata Jibrin Isah, mai wakiltar Kogi ta Gabas, ne ya gabatar da kudirin, inda ya tuna cewa marigayi Ibrahim Idris ya kasance mamba a PDP. Yayin gabatar da kudirin, Isah ya ce shi da Akpabio da sauran ‘yan siyasar lokacin duk sun kasance cikin PDP. “Marigayi Ibrahim Idris ya kasance mamba a PDP;…
Read More
A cikin shekara huɗu zan gyara Nijeriya – Makinde

A cikin shekara huɗu zan gyara Nijeriya – Makinde

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya yi alkawarin sake fasalin Nijeriya cikin shekaru huɗu idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2027. Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron masu ruwa da tsaki na yankin Arewa ta Tsakiya da tawagar yaƙin neman zaɓensa ta gudanar a Lafia, Jihar Nasarawa. Ya ce shi mai son kawo sauyi ne, yana mai cewa idan aka zaɓe shi, zai yi amfani da wa’adin mulki guda wajen sake fasalin ƙasar. Makinde ya ce shirin nasa…
Read More
Atiku ya goyi bayan tafiyar ‘Tinubu Must Go’

Atiku ya goyi bayan tafiyar ‘Tinubu Must Go’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana goyon bayansa ga ƙungiyar ‘Tinubu Must Go’ (TMG), yana mai cewa yunƙurin na nuna ƙudurin ’yan Nijeriya na ceto ƙasar. Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne bayan da ya karɓi bakuncin ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa ƙungiyar, Abba Hikima, a gidansa da ke Abuja. A cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, Atiku ya ce abin da ya fi burge shi shi ne yadda ƙungiyar ke jan hankalin jama’a da kuma ƙara wayar da kan…
Read More
UNC ta wayar da kai kan zaman lafiya da yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Katsina 

UNC ta wayar da kai kan zaman lafiya da yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Katsina 

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina  ‎ ‎Kungiyar United Nigerian Chaplaincy (UNC), Katsina Command, ta gudanar da taron wayar da kan al’umma kan muhimmancin zaman lafiya da illolin ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a shiyyar Daura. ‎An gudanar da taron ne a Sakatariyar ƙaramar Hukumar Daura, a matsayin wani ɓangare na rangadin wayar da kai da ƙungiyar ke gudanarwa a shiyyoyi uku na Jihar Katsina. ‎A yayin taron, mahalarta sun tattauna kan yadda shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ke taimakawa wajen haifar da matsalolin tsaro da sauran munanan halaye, musamman tsakanin matasa. An kuma yi kira ga al’umma da su ƙara ba da haɗin…
Read More
Na ji duk ƙorafe ƙorafenku – Gwamna Dauda ga masu ruwa da tsakin APC a Zamfara

Na ji duk ƙorafe ƙorafenku – Gwamna Dauda ga masu ruwa da tsakin APC a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan siyasa yanzu, domin lokacin siyasa ya yi. Gwamnan ya bayyana hakan yau Asabar, a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau. Gwamna Lawal ya ce tsawon shekaru uku da suka gabata, gwamnatinsa ta mayar da hankali ne wajen gudanar da ayyukan gwamnati don al'ummar jihar, inda ya lura cewa yanzu lokaci ya yi na fuskantar siyasa. "Tsawon shekaru uku mun mayar da hankali ne kan…
Read More
Zamfara @30: JB Yakubu ya yaba wa Gwamna Lawal kan jagorancin kawo sauyi

Zamfara @30: JB Yakubu ya yaba wa Gwamna Lawal kan jagorancin kawo sauyi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon Shugaban soja na Jihar Zamfara, Kanal Jibrin Bala Yakubu (mai ritaya), ya yaba wa gwamnatin Gwamna Dauda Lawal saboda sake fasalin jihar ta hanyar bunƙasa tattalin arzikin ɗan Adam da kuma sauyi mai ingancin a Jihar. Kanal Yakubu ya yi wannan sanarwar ne a ranar Juma'a a Gusau yayin da yake buɗe sakatariyar J.B Yakubu da aka gyara a matsayin wani ɓangare na ayyukan bikin cika shekaru 30 da kafa Jihar Zamfara. Da yake jawabi a wurin bikin, ya ce ya yi matuƙar farin ciki da ci gaban da gwamnatin yanzu ta samu. "Abin…
Read More
NLC ta tabbatar da tsarin fansho na da alfanu ga ma’aikatan Katsina – Mai’adua

NLC ta tabbatar da tsarin fansho na da alfanu ga ma’aikatan Katsina – Mai’adua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Katsina NLC ta sake nanata cewa tsarin fansho da gwammatin jihar ta ɓullo da shi mafita ce mai ɗorewa bayan aje aiki ga ma'aikata. Muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Kwamarad Nasiru Wada, ya bayyana haka a yayin zantawa da manema labarai dan gane da saƙon ƙungiyar na cikar Nijeriya shekaru 66 da samun yancin kai. Comrade Nasiru Wada yayi nuni da cewa babu yanda za'ayi ƙungiyar ta bari ayi amfani da wani tsari wanda zai cutar da ma'aikata kasancewar su sune jigon nasarar cigaban Nigeria a tsawon shekaru 66. "A koda…
Read More
Majalisar dokokin Katsina ta karɓi buƙatar neman ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi

Majalisar dokokin Katsina ta karɓi buƙatar neman ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalissar dokoki ta jihar Katsina, ta yi karatu na 2, akan dokar dake buƙatar yiwa kundun tsarin mulkin Nijeriya garambawul, domin ƙirƙirar 'yan sandan jihohi. Majalissar ta karɓi buƙatar yin dokar, domin yiwa kundun tsarin mulkin garambawul daga majalissar ƙasa (National Assembly) bayan da majalissar ta rattaɓa hannun a kan dokar, domin ƙirƙirar 'yan-sandan. Yanzu kuma majalissar ta tura dokar zuwa majalissun dokokin Nijeriya, domin neman amincewar su. Bayan amincewa da majalissar ƙasa tayi da dokar, dole ne sai an tura kundun dokar zuwa majalissun jihohi 34 dake faɗin Nijeria domin amincewar su, dokar ba…
Read More