ukarofi

12458 Posts
NLC ta tabbatar da tsarin fansho na da alfanu ga ma’aikatan Katsina – Mai’adua

NLC ta tabbatar da tsarin fansho na da alfanu ga ma’aikatan Katsina – Mai’adua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Katsina NLC ta sake nanata cewa tsarin fansho da gwammatin jihar ta ɓullo da shi mafita ce mai ɗorewa bayan aje aiki ga ma'aikata. Muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Kwamarad Nasiru Wada, ya bayyana haka a yayin zantawa da manema labarai dan gane da saƙon ƙungiyar na cikar Nijeriya shekaru 66 da samun yancin kai. Comrade Nasiru Wada yayi nuni da cewa babu yanda za'ayi ƙungiyar ta bari ayi amfani da wani tsari wanda zai cutar da ma'aikata kasancewar su sune jigon nasarar cigaban Nigeria a tsawon shekaru 66. "A koda…
Read More
Majalisar dokokin Katsina ta karɓi buƙatar neman ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi

Majalisar dokokin Katsina ta karɓi buƙatar neman ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalissar dokoki ta jihar Katsina, ta yi karatu na 2, akan dokar dake buƙatar yiwa kundun tsarin mulkin Nijeriya garambawul, domin ƙirƙirar 'yan sandan jihohi. Majalissar ta karɓi buƙatar yin dokar, domin yiwa kundun tsarin mulkin garambawul daga majalissar ƙasa (National Assembly) bayan da majalissar ta rattaɓa hannun a kan dokar, domin ƙirƙirar 'yan-sandan. Yanzu kuma majalissar ta tura dokar zuwa majalissun dokokin Nijeriya, domin neman amincewar su. Bayan amincewa da majalissar ƙasa tayi da dokar, dole ne sai an tura kundun dokar zuwa majalissun jihohi 34 dake faɗin Nijeria domin amincewar su, dokar ba…
Read More
Duk da matsalar tattalin arziki, APC har yanzu tana da goyon baya a Zamfara – Jaji

Duk da matsalar tattalin arziki, APC har yanzu tana da goyon baya a Zamfara – Jaji

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Birnin Magaji/Kaura Namoda a jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya ce duk da ƙalubalen tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) har yanzu tana da goyon baya mai yawa a tsakanin al'ummar jihar Zamfara. Hon. Jaji ya bayyana hakan ne a Gusau yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ƙungiyarsa ta masu goyon bayan siyasar sa wato ƙungiyar siyasa ta Jajiyya ta shirya. A cewar sa, akwai buƙatar gwamnatin jihar ta tallafa wa 'yan jam'iyya domin su shiga kowane lungu da…
Read More
Kar ku raina gudunmuwar da za ku bayar a Nasarawa – Gwamna sule

Kar ku raina gudunmuwar da za ku bayar a Nasarawa – Gwamna sule

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi kira na musamman ga membobin masu yi wa ƙasa hidima ta NYSC 2,617 da aka tura jihar cewa kada su raina gudummawar da za su iya bayarwa wajen cigaban jihar. Gwamna Sule ya yi wannan kiran ne a jiya Juma'a yayin bikin rantsar da aji na 2026 Batch 'C' Stream I a sansanin Magaji Dan Yamusa na din-din-din da ke Keffi. Gwamnan wanda kwamishinan matasa da wasanni Mista Jubril Ibrahim ya wakilta ya buƙaci masu yi wa ƙasar hidima da kada su ɗauki tura su zuwa al'ummomi…
Read More
Gidauniyar Ɗanbayo ta ƙaddamar da tallafin ilimi ga ɗalibai 83,000 a Gombe

Gidauniyar Ɗanbayo ta ƙaddamar da tallafin ilimi ga ɗalibai 83,000 a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Gidauniyar Ɗanbayo ta ƙaddamar da wani shirin tallafa wa ilimi da zai shafi kusan ɗalibai 83,000 da malamai 415 a makarantu 83 da ke faɗin Jihar Gombe, da nufin inganta yanayin koyarwa da koyo. An ƙaddamar da shirin ne ranar Juma’a, 2 ga Oktoba, 2026, a Makarantar Alabura S. Kudin Model Nursery, Primary and Junior Secondary School da ke Kumbiya-Kumbiya, Gombe, inda gidauniyar ta raba kayayyakin karatu daban-daban ga makarantar. Kayayyakin da aka raba sun haɗa da littattafan rubutu, kundin rajistar aji, littattafan tsara darasi, alƙaluman rubutu, masu auna layi, fensir, masu goge rubutu, dastar…
Read More
Atiku ya buƙaci Tinubu ya ƙara mafi ƙarancin albashi saboda tsadar rayuwa

Atiku ya buƙaci Tinubu ya ƙara mafi ƙarancin albashi saboda tsadar rayuwa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa, yana mai cewa albashin Naira 70,000 da ake biya a yanzu ya rasa ƙarfinsa sakamakon tsadar man fetur da hauhawar farashin kayan masarufi. Atiku ya kuma goyi bayan buƙatar ƙungiyoyin ƙwadago na neman ƙarin albashi mai tsoka, yana mai cewa ma’aikata na fuskantar wahalar biyan sayen abinci, sufuri, haya da sauran muhimman buƙatun rayuwa. Daraktan Sadarwa da Tsare-tsaren Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu,…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta haramta wa ’yan kwangila samun ayyukanta shekaru biyar

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa ’yan kwangila samun ayyukanta shekaru biyar

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta amince da sabbin ƙa’idojin dakatar da ’yan kwangila, masu ba da shawara da masu samar da ayyuka daga shiga harkokin kwangilar gwamnati, inda aka tanadi dalilai shida da za su iya sa a hana su shiga ayyukan gwamnatin tarayya na tsawon shekaru uku zuwa biyar. Sabbin ƙa’idojin sun haɗa da bayar da cin hanci ko wasu alherai domin yin tasiri kan shawarar bayar da kwangila, samun hukuncin laifin damfara, ƙin cika sharuɗɗan kwangila da gangan, tarihin rashin kyakkyawan aiki, gurɓata takardu da kuma kasancewa wata ƙungiya ta ƙasa da ƙasa mai ɓangarori da…
Read More
Gwamnatin Tinubu na neman sabon bashin Dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya

Gwamnatin Tinubu na neman sabon bashin Dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fara tattaunawa da Bankin Duniya kan neman sabbin rance uku da jimillar kuɗinsu ta kai Dala biliyan 1.5, a daidai lokacin da jimillar bashin Nijeriya ya haura zuwa matakin da ba a taɓa gani ba, inda ya kai Naira tiriliyan 166.79 a ƙarshen watan Yuni 2026. Sabbin rancen sun ƙunshi dala miliyan 500 kowanne, waɗanda aka tsara domin tunkarar sauyin yanayi, ƙarfafa tsarin tallafa wa marasa galihu da kuma bunƙasa harkokin yara ƙanana. Bayanan ayyukan Bankin Duniya sun nuna cewa mafi kusa da fara aiwatarwa daga cikin…
Read More
Matatar Dangote ta kai kashi 105 na ƙarfin aiki

Matatar Dangote ta kai kashi 105 na ƙarfin aiki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar Dangote ta gudanar da aiki sama da cikakken ƙarfinta a watan Agustan 2026, inda ta kai kashi 105.21 cikin 100 na ƙarfin samar da mai, yayin da shigo da man fetur daga ƙasashen waje ya ragu da kashi 26 cikin 100. Hakan na ƙunshe ne cikin takardar bayanan watan Agustan 2026 da Hukumar Kula da Harkokin Haƙowa da Tace Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA) ta fitar, wadda aka raba wa ’yan jarida ranar Alhamis. Bayanan sun nuna cewa matatun mai na cikin gida sun karɓi matsakaicin ganga 683,000 na ɗanyen mai a kowace rana, wanda…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da sikila

Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da sikila

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta ta rage giɓin samun kulawa da damar rayuwa tsakanin mutanen da ke fama da cutar sikila, yayin da Nijeriya ta haɗa hannu da wasu ƙasashe da ƙungiyoyin duniya wajen ƙaddamar da sabuwar ƙawance da nufin sauya tsarin kula da masu fama da cutar. ƙaramin Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Dakta Iziaƙ Adekunle Salako, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da shirin “OneSCD – ƙawancen Duniya na Bunƙasa Daidaito da Sauya Tsarin Kula da Cutar Sikila”, wanda aka gudanar a Majalisar ɗinkin Duniya da ke New York,…
Read More