ukarofi

12458 Posts
Ummarar Sarkin Ibadan ta jawo cece-kuce kan dangantakar addini da al’adar Yarabawa

Ummarar Sarkin Ibadan ta jawo cece-kuce kan dangantakar addini da al’adar Yarabawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mai martabar Sarkin ƙasar Ibadan, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, Arusa I, ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan yaɗuwar hotunansa yayin da yake gudanar da ibadar Umrah a Saudiyya. Oba Ladoja, wanda shi ne basaraken gargajiya na 44 a tarihin ƙasar Ibadan, ya je Saudiyya ne domin gudanar da ibadar Umrah, a wani ɓangare na bukukuwan cikar shekara guda da hawansa karagar mulkin ƙasar badan a shekarar 2025. Ladoja, wanda tsohon gwamnan Jihar Oyo ne kuma a halin yanzu yake jagorantar Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Oyo, an cauke shi hoto a Saudiyya tare da…
Read More
Nijeriya za ta zamanantar da manyan tashoshin jiragen ruwan ƙasar

Nijeriya za ta zamanantar da manyan tashoshin jiragen ruwan ƙasar

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta amince da wani cikakken shiri na zamanantarwa da inganta tashoshin jiragen ruwa na Onne, Ribas, Delta da Kalaba, a wani mataki da ta ce zai ƙarfafa ababen more rayuwa na harkokin ruwa, inganta sauƙin kasuwanci da kuma mayar da Nijeriya cibiyar jigilar kayayyaki ta duniya a Afirka. Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Gboyega Oyetola, ne ya bayyana amincewar a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2026. Oyetola ya bayyana amincewar a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen aiwatar da ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) ta…
Read More
Amfani da datar intanet ya ƙaru da kashi 47 a Nijeriya – NCC

Amfani da datar intanet ya ƙaru da kashi 47 a Nijeriya – NCC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), Dakta Aminu Wada Maida, ya bayyana cewa ’yan Nijeriya sun yi amfani da data na intanet da suka haura terabyte miliyan 1.66 cikin shekara guda. Dakta Maida ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Otel ɗin Onomo Allure da ke Abuja, yayin bikin buɗe taron kwanaki biyu na dandalin Nijeriya kan Haɗin Kan Dijital da Zuba Jari, wanda Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ta shirya tare da haɗin gwiwar SwedFund da Okla. Ya ce adadin ya nuna cewa amfani da intanet a Nijeriya ya ƙaru da kashi 47 cikin…
Read More
Neja: ’Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 47, sun nemi fansar miliyan N2 kan kowanne

Neja: ’Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 47, sun nemi fansar miliyan N2 kan kowanne

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga sun sace manoma da dama a hare-hare daban-daban a ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja, inda Shugaban ƙaramar Hukumar, Alhaji Aliyu Bagga Muhamadu, ya ce adadin mutanen da aka sace ya kai 47, yayin da masu garkuwar suka nemi a biya kuɗin fansa na Naira miliyan biyu kan kowane mutum. An ce an sace manoman ne yayin da suke aikin girbin gyada a yankin Tungan Rimi, da ke Ma’undu-Beri Ward a ƙaramar Hukumar Mariga. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da rana, inda maharan suka kuma tafi da wasu maza…
Read More
’Yan sanda sun kama matar aure bisa zargin kashe kishiyarta da turmi a Bauchi

’Yan sanda sun kama matar aure bisa zargin kashe kishiyarta da turmi a Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 33, Hauwa’u Haruna, bisa zargin kashe kishiyarta, Jamila Adamu, mai shekaru 43, da turmi a Tafawa Balewa Housing Estate da ke cikin birnin Bauchi. Lamarin ya faru ne ranar 27 ga Satumba, 2026, inda daga bisani rundunar ’yan sandan jihar ta kama wadda ake zargin bayan samun bayanai kan rikicin cikin gida da ya faru tsakanin matan aure biyu da ke zaune a gida ɗaya na mijinsu. Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana…
Read More
Ruwan sama ya janyo ambaliya a Fatakwal

Ruwan sama ya janyo ambaliya a Fatakwal

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassa na birnin Port Harcourt, babban birnin Jihar Rivers, inda ruwa ya mamaye gidaje da tituna tare da nutsar da motoci, lamarin da ya bar wasu mazauna yankunan cikin mawuyacin hali tare da kawo cikas ga harkokin yau da kullum. Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ta biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka shafe kwanaki ana samu a birnin, inda wasu mazauna yankunan da abin ya shafa suka makale tare da kasa gudanar da harkokinsu yadda ya kamata. Hotunan bidiyo da ke yawo…
Read More
Wanda aka tsinci gawarsa a ƙarƙashin gadar Abuja ya mutu ne a otel — ’Yan sanda

Wanda aka tsinci gawarsa a ƙarƙashin gadar Abuja ya mutu ne a otel — ’Yan sanda

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta bayyana cewa, mutumin da aka tsinci gawarsa a ƙarƙashin Gadar Katampe dake kan babban titin zuwa Kubwa ya mutu ne akan wata matar aure a wani otel da ke Gwarimpa. Kwamishinan ’Yan Sandan FCT, Ahmed Muhammed Sanusi, ne ya bayyana hakan ranar Asabar a Abuja yayin da yake yi wa ’yan jarida bayani kan binciken da rundunar ta gudanar game da gawar mutumin. Sanusi ya ce tun kafin a tsinci gawarsa, iyalan mamacin sun kai rahoton cewa ya ɓace. Ya ce an gano gawarsa da misalin ƙarfe 9:00…
Read More
El-Rufai na girbar abin da ya shuka a Kaduna ne – Shehu Sani

El-Rufai na girbar abin da ya shuka a Kaduna ne – Shehu Sani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ce tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na girbar sakamakon abubuwan da ya aikata a lokacin da yake mulkin jihar. Ya ce halin da tsohon gwamnan ke ciki a yanzu ya kamata ya zama darasi ga sauran shugabanni. Shehu Sani da El-Rufai sun daɗe suna takun saƙa a siyasar Kaduna, musamman a lokacin da El-Rufai ke matsayin gwamnan jihar daga shekarar 2015 zuwa 2023. Rikicin da ke tsakaninsu ya tsananta ne a lokacin da Shehu Sani ke matsayin Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, inda…
Read More
Kotu ta dakatar da aikin gina matatar Dangote ta Dala biliyan 16 a Kenya

Kotu ta dakatar da aikin gina matatar Dangote ta Dala biliyan 16 a Kenya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata kotu a Kenya ta bayar da umarnin dakatar da wasu ayyukan da suka shafi gina sabuwar matatar man Dangote da aka shirya ginawa a Lamu, Arewa maso Gabashin ƙasar, mai darajar kusan dala biliyan 16, bayan da wasu mazauna yankin 133 suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar yadda aka samu filayen da ake shirin gudanar da aikin. Matakin kotun ya zo ne kwanaki biyu kacal kafin bikin aza harsashin fara aikin matatar da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 30 ga Satumba, 2026. Masu ƙarar, waɗanda suka bayyana kansu a matsayin manoma da…
Read More
Rainbow Coalition: APC ta buƙaci Wike ya shiga jam’iyyar

Rainbow Coalition: APC ta buƙaci Wike ya shiga jam’iyyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu shugabannin jam’iyyar APC a jihohi sun yi watsi da ƙungiyar Rainbow Coalition da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta, inda suka buƙaci ya koma APC gaba ɗaya idan da gaske yake goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027. A kwanakin baya ma, Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce Wike ba zai iya kasancewa yana goyon bayan APC a matakin shugaban ƙasa, yayin da yake tallafa wa ’yan wasu jam’iyyu a zaɓen gwamnoni da ’yan majalisa ba. Ya ce Wike ya kamata ya zaɓi ɓangare guda, ko ya shiga APC ko…
Read More