ukarofi

12458 Posts
Siyasa da son zuciya ne suka hana aiwatar da shari’ar Musulunci — Kwamitin tabbatar da adalci

Siyasa da son zuciya ne suka hana aiwatar da shari’ar Musulunci — Kwamitin tabbatar da adalci

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Kwamitin Tabbatar da Adalci a cikin Al’umma, ƙarƙashin shugabancin Malam Ilyasu ɗorayi, tare da Sakataren Kwamitin, Malam Rabi’u, da Mataimakin Sakataren, Ustaz Muhammad Bello Ibrahim, sun bayyana cewa akwai dalilai da dama da suka hana aiwatar da Shari’ar Musulunci yadda ya kamata a wasu jihohin Nijeriya da suka fara aiwatar da ita tun shekarar 1999, musamman a jihohin Arewa. Sun bayyana hakan ne a yayin wani taron gangamin malamai daga ƙungiyoyi da ɗariku daban-daban, ciki har da waɗanda ba sa cikin wata ɗariƙa, wanda aka gudanar ranar Lahadi a Makarantar Nazarin Harshen Larabci da ke…
Read More
Tun 1984 da Sarkin Gumel ba ni kyauta a FGC Kano ya shiga raina — Dr Muhammad Musa

Tun 1984 da Sarkin Gumel ba ni kyauta a FGC Kano ya shiga raina — Dr Muhammad Musa

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Dakta Muhammad Musa Muhammad, Shugaban ƙungiyar ƙwararrun Likitoci ta Jihar Jigawa kuma Shugaban Sashen Fida na Asibitin Koyarwa na Rashid Shekoni da ke Jihar Jigawa, ya bayyana marigayi Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani na Biyu, a matsayin dattijo na gari, uba kuma jagora wanda ya yi tasiri sosai a rayuwarsa. Dr Muhammad Musa ya ce marigayi Sarkin Gumel ya shiga cikin rayuwarsa tun shekarar 1984, lokacin da ya ba shi wata kyauta da hukumar Federal Government College Kano ta ba shi sakamakon nuna ƙwazo da Ubangiji ya ba shi damar yi a lokacin da…
Read More
Shafa’u Linnas Habal International ya horar da ƙwararrun masu maganin gargajiya 60 a Kano

Shafa’u Linnas Habal International ya horar da ƙwararrun masu maganin gargajiya 60 a Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Sha’awar ganin an sauya mummunan kallon da wasu daga cikin al’umma ke yi wa masu maganin gargajiya ce ta sa Wazirin Maganin Jihar Kano, Alhaji Nasiru Sani Abubakar, ya sadaukar da dukiyarsa wajen ɗaukar nauyin horar da masu maganin gargajiya domin ƙara musu ilimi da ƙwarewa a sana’arsu. Wazirin Maganin, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Masu Maganin Gargajiya ta “Moden” da “ƙAA” na masu maganin gargajiya, Alhaji Nasiru Sani Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan kammala bitar kwanaki shida da aka shirya wa ƙwararrun masu maganin gargajiya 60 a Jihar Kano. An gudanar da…
Read More
Sarki Sanusi ya nuna damuwa kan yaƙi da cin hanci, ya taɓa batun ci gaba da tsare El-Rufai

Sarki Sanusi ya nuna damuwa kan yaƙi da cin hanci, ya taɓa batun ci gaba da tsare El-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, yana mai cewa siyasa na iya yin tasiri wajen bincike da gurfanar da wasu mutane. Sarkin ya kuma yi magana kan shari’a da kuma ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana mai tambayar ko yadda ake gudanar da wasu shari’o’in cin hanci da rashawa ya dace da manufar da aka kafa hukumomin yaƙi da rashawa domin cimmawa. Sanusi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da…
Read More
Majalisar Wakilai za ta fassara dokoki zuwa Hausa, Igbo da Yoruba

Majalisar Wakilai za ta fassara dokoki zuwa Hausa, Igbo da Yoruba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar dokokin Nijeriya ta ce tana shirin fara fassara dokokin ƙasar zuwa Hausa, Igbo, Yoruba da sauran harsunan gida, domin sauƙaƙa wa jama’a fahimtar dokokin da suka shafi rayuwarsu. Majalisar ta ce matakin na daga cikin shirye-shiryen amfani da fasahar zamani wajen inganta hanyoyin da jama’a ke samun bayanai kan ayyukan majalisa da dokokin ƙasa. Haka kuma, Majalisar na shirin ƙaddamar da manhajar wayar hannu ta National Assembly Library, wadda za ta bai wa jama’a damar samun bayanan majalisa cikin sauƙi. Za kuma a kafa Bills Tracker, domin bai wa jama’a damar bibiyar matakan…
Read More
Mambilla: Yadda binciken Premium Times ya taimaka wa Nijeriya ta yi nasara kan Leno Adesanya a Faransa

Mambilla: Yadda binciken Premium Times ya taimaka wa Nijeriya ta yi nasara kan Leno Adesanya a Faransa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani bincike da Premium Times ta gudanar kan wata ɗoyayyiyar yarjejeniya a ƙasashen ketare da ta shafi iyalan tsohon mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, da ɗan kasuwa Leno Adesanya, ya taimaka wa Gwamnatin Nijeriya wajen samun nasara a rikicin aikin samar da wutar lantarki na Mambilla. Binciken, wanda aka wallafa a ranar 13 ga Oktoba 2021 a matsayin wani ɗangare na aikin Pandora Papers, ya zama cikin hujjojin da Gwamnatin Nijeriya da lauyoyinta suka gabatar yayin shari’ar sasantawa a Kotun Kula da Harkokin Kasuwanci ta Duniya (ICC) da ke…
Read More
Sauye-sauyen Tinubu sun ɗora tattalin arzikin Nijeriya kan turbar ci gaba mai ɗorewa – Otedola

Sauye-sauyen Tinubu sun ɗora tattalin arzikin Nijeriya kan turbar ci gaba mai ɗorewa – Otedola

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Attajirin ɗan kasuwa kuma Shugaban Kamfanin First HoldCo Plc, Femi Otedola, ya yaba da sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar, yana mai cewa matakan sun sanya tattalin arzikin Nijeriya kan turbar samun ci gaba mai ɗorewa. Otedola ya bayyana hakan ne a birnin Paris na ƙasar Faransa ranar Litinin, bayan wata liyafar cin abinci ta sirri da ya  halarta tare da Shugaba Tinubu, wanda ke Turai domin hutun aiki. Ya ce sauye-sauyen da Tinubu ya aiwatar, waɗanda ya bayyana a matsayin matakai “masu ƙarfin hali da hangen nesa”, sun sanya…
Read More
Ba za mu amince da ƙudirin INEC Na amfani da AI a zaɗen 2027 ba – Obidient Movement 

Ba za mu amince da ƙudirin INEC Na amfani da AI a zaɗen 2027 ba – Obidient Movement 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ƙungiyar Obidient Movement ta yi watsi da shirin Hukumar INEC na amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) a babban zaɗen shekarar 2027. ƙungiyar ta ce bai kamata INEC ta fara amfani da sabuwar fasaha ba, alhali har yanzu ba a magance wasu muhimman matsaloli da suka shafi sahihancin zaɗe, bayyana sakamako da yadda ake tura sakamakon zaɗe ba. A wata sanarwa da sashen yada labarai da sadarwa na ƙungiyar ya fitar, Obidient Moɗement ta bayyana damuwa kan abin da ta kira rashin bayyana gaskiya da kuma zargin akwai alaƙa tsakanin INEC da jam’iyyar APC…
Read More
2027: Nasarar Tinubu za ta kawo ƙarshen siyasar wasu shugabannin adawa – Amaechi

2027: Nasarar Tinubu za ta kawo ƙarshen siyasar wasu shugabannin adawa – Amaechi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), kuma tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya faɗa wa shugabannin jam’iyyar cewa nasarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu a zaɓen 2027 za ta iya sa da dama daga cikinsu su daina siyasa. Amaechi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron ƙungiyar mata ta ƙasa ta ADC, wato ADC National Women League Conference, da aka gudanar a Abuja ranar Laraba. Ya yi nuni da yadda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kayar da Peoples Democratic Party (PDP) a…
Read More
2027: Zan yi murabus idan Tinubu ya sha kaye a Abuja da Ribas – Wike

2027: Zan yi murabus idan Tinubu ya sha kaye a Abuja da Ribas – Wike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa zai yi murabus daga mukaminsa na minista idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaza samun nasara a Babban Birnin Tarayya (FCT) da Jihar Ribas a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Wike ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da shugabanni da mambobin ƙungiyar Masu Gyaran Motoci da ’Yan Kasuwa ta Apo a Abuja, inda ya danganta ci gaba da kasancewarsa a matsayin minista da nasarar da zai samu wajen samar da sakamakon siyasa ga Shugaba Tinubu a wuraren da yake da tasiri. A…
Read More