ukarofi

12570 Posts
Kwastom ta Nijeriya ta yi murnar samun mace ta farko matuƙiyar jirgi a Amurka

Kwastom ta Nijeriya ta yi murnar samun mace ta farko matuƙiyar jirgi a Amurka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta bayyana farin ciki da jin daɗi bayan wata jami’arta, Sufurintandan Kwastom Nafisat Balogun, ta samu gagarumar nasara ta zama mace ta farko a cikin hukumar da ta mallaki lasisin tuƙin jirgi na kasuwanci mai injina da dama daga ƙasar Amurka. A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Abdullahi Maiwada, ya fitar a ranar Litinin, ya ce an gudanar da wani biki na musamman domin karrama Balogun, wanda Sashen Fasaha na Kwastom ya shirya, tare da halartar manyan jami’ai, shugabanni da abokan aiki. Sanarwar ta bayyana wannan nasara a matsayin tarihi…
Read More
Bayyanar Minista Musawa sanye da ɓangwalelen tabarau ya haddasa muhawara

Bayyanar Minista Musawa sanye da ɓangwalelen tabarau ya haddasa muhawara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministar Harkokin Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin ƙirƙire-ƙirƙire ta ƙasa, Hannatu Musa Musawa, ta janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan ta halarci wani taron jama’a sanye da tabarau mai tsada, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi tsakanin ’yan Nijeriya. Ministar ta wakilci Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a bikin kamun kifi na Nwonyo na shekarar 2026 da aka gudanar a tafkin Lake Nwonyo, cikin ƙaramar hukumar Ibi a jihar Taraba. Bikin ya ja hankalin baƙi da masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na ƙasa da ma ƙasashen waje. Da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ninka kuɗin yaƙi da ta’addanci a kasafin 2026

Gwamnatin Tarayya ta ninka kuɗin yaƙi da ta’addanci a kasafin 2026

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta ɗaga matakin yaƙi da ta’addanci ta fuskar shari’a, inda ta ware kimanin Naira biliyan 1.371 domin gudanar da shari’o’in da suka shafi ƙungiyar Boko Haram da sauran laifukan ta’addanci a kasafin kuɗin shekarar 2026. Binciken da aka yi ya nuna cewa wannan sabon tanadi ya zarce kuɗin da aka ware a shekarar 2025, inda a wancan lokaci aka ware Naira miliyan 530 kacal, lamarin da ke nuna ƙaruwa mai yawa a ƙoƙarin gwamnati na tunkarar matsalar tsaro ta hanyar doka. Wannan ci gaba ya fito ne bayan Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya…
Read More
Magoya bayan El-Rufai sun fashe da kuka bayan alƙali ya bada umarnin ci gaba da tsare shi

Magoya bayan El-Rufai sun fashe da kuka bayan alƙali ya bada umarnin ci gaba da tsare shi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi watsi da buƙatar bayar da belin tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, a ci gaban shari’ar da gwamnatin jihar ke tuhumar sa da almundahanar biliyoyin kuɗaɗe da kuma amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba, inda nan take magoya bayan tsohon gwamnan suka fashe da kuka bayan alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Darius Khobo, ya ɗage shari’ar zuwa makon farko na watan Yunin 2026, domin fara sauraron ainihin shari’ar. Alƙalin ya bayyana cewa, bayan sauraron muhawarar ɓangarorin biyu, inda ake sa ran…
Read More
Yadda INEC ke neman wanke shugabanta kan zargin goyon bayan APC

Yadda INEC ke neman wanke shugabanta kan zargin goyon bayan APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Zaɓen Mai Zaman Kanta ta Nijeriya, INEC ta ce wani binciken ƙwaƙwaf da ƙwararru suka gudanar sun tabbatar da zargin da ake yi wa shugabanta Farfesa Joash Amupitan da alhakin wallafa bayanan da suka danganta shi da jam'iyyar APC mai mulki cewa ƙirƙirarsu aka yi. A wani bayani da hukumar ta fitar ta ce wani ƙwararre da ta yi hayarsa ya gudanar da bincike tare da gano cewa an rarraba bayanan na bogi ga jama'a domin ɓata wa shugaban nata suna. Kimanin mako biyu kenan da suka gabata bayan da aka bankaɗo wani…
Read More
Dangote zai sayar da kaso 10 na matatarsa a 2026

Dangote zai sayar da kaso 10 na matatarsa a 2026

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana shirin sayar da kaso 10 cikin 100 na babbar matatar fetur ɗinsa ta hanyar wani gagarumin tsarin sayar da hannun jari na farko (wato IPO) a nahiyar Afirka, wanda ake sa ran za a aiwatar da shi a shekarar 2026. Dangote ya bayyana hakan ne yayin wani taro da Atlantic Council ta shirya a birnin Washington, D.C., inda ya ce wannan mataki zai taimaka wajen jawo jarin dogon lokaci da kuma bunƙasa kasuwar jari ta Afirka. A cewarsa, matatar Dangote za ta riƙa biyan masu hannun jari…
Read More
Kotu ta ba da umarnin sakin Sheikh Sani Zariya

Kotu ta ba da umarnin sakin Sheikh Sani Zariya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a saki malamin addinin nan, Sheikh Sani Abdulkadir Zariya nan take ba tare da wani sharaɗi ba. A hukuncin da Mai Shari’a Peter O. Lifu ya yanke a ranar Litinin, ta kuma ba da umarnin biyan malamin diyyar jimillar Naira miliyan 5 kan take haƙƙoƙinsa na ɗan Adam. Mai shari’a Lifu ya bayyana cewa tsare malamin na tsawon lokaci ba tare da umarnin kotu ba ya saɓa wa haƙƙoƙinsa na ’yancin kai, sauraron shari’a cikin adalci da kuma ’yancin zirga-zirga kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya…
Read More
Dagacin Bomala ya naɗa Lawan Siraka Turakin Bomala

Dagacin Bomala ya naɗa Lawan Siraka Turakin Bomala

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Dagacin Bomala da ke mazaɓar Garko a ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, Malam Dauda Adamu, ya naɗa Lawan Siraka, wanda aka fi sani da Baba Lawan, a matsayin Turakin Bomala, a wani biki mai kayatarwa da ya samu halartar jama’a daga sassa daban-daban. Da yake jawabi a madadin abokan sabon Turakin, Muhammad A. Barde, ya yabawa Dagacin bisa ganin cancantar Baba Lawan da ya ba shi wannan mukami, yana mai cewa mutum ne mai son zaman lafiya wanda bai taba shiga rikici da kowa ba tun bayan zuwansa Bomala fiye da shekaru 20 da suka…
Read More
Kuji Zambuk ya bai wa Salamatu Wambai sarautar Kuji Gwatom

Kuji Zambuk ya bai wa Salamatu Wambai sarautar Kuji Gwatom

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe A wani yunƙuri na ƙarfafa rawar da mata ke takawa a harkokin gargajiya, Kuji Zambuk ya bai wa Hajiya Salamatu Wanbai Aliyu sarautar Kuji Gwatom, (Sarauniyar Zambuk) ɗaya daga cikin muhimman muƙaman gargajiya da ake bai wa mata a masarautar. Salamatu Wanbai, wadda ta yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa, musamman a aikin jarida da harkokin siyasa, ta shafe shekaru tana aiki a gidan rediyo kafin ta tsunduma cikin siyasa, inda ta ci gaba da bada gudunmawa wajen cigaban al’umma. Haka kuma tana rike da mukamin Alkebbar Kwadom, wanda ke kara nuna darajarta da…
Read More
An yi addu’o’i na musamman ga Marigayi Bashir Ado a masallacin Gwammaja

An yi addu’o’i na musamman ga Marigayi Bashir Ado a masallacin Gwammaja

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Al’ummar unguwar Gwammaja sun bayyana marigayi shugaban kwamitin amintattu na Masallacin Ihya’ussunnah da ke rukunin gidajen ‘yan majalisu, Alhaji Bashir Ado, wanda Allah Ya karɓi ransa a makon ƙarshe kafin watan Azumin Ramadan da ya gabata, a matsayin mutum mai gaskiya, riƙon amana, haƙuri da son zaman lafiya, tare da irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban masallacin. An bayyana hakan ne a yayin wani taron addu’o’i na musamman da aka gudanar domin yi wa marigayin fatan rahama. Babban Limamin masallacin Gwammaja, Malam Lawan Abubakar Gwauron Maje, ne ya jagoranci addu’ar, inda ya bayyana…
Read More