ukarofi

12570 Posts
Majalisar Dokokin Kano ta gayyaci Shugaban SUBEB kan zargin rashin gamsuwa da ɗaukar ma’aikata

Majalisar Dokokin Kano ta gayyaci Shugaban SUBEB kan zargin rashin gamsuwa da ɗaukar ma’aikata

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci Shugaban Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB), Alhaji Yusuf Kabir, domin ya bayyana a gabanta kan zargin rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da aikin daukar sabbin ma’aikata na baya-bayan nan. Matakin na zuwa ne bayan da wasu ‘yan majalisar suka nuna damuwa kan yadda aka gudanar da aikin, inda suka bukaci a sake duba tsarin domin tabbatar da an yi komai bisa gaskiya, adalci da kuma bin ƙa’ida. Da yake gabatar da ƙudirin nuna rashin gamsuwa a zauren majalisar, ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Dambatta,…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya taya Muttaƙa Rabe murnar naɗa shi minista

Gwamna Raɗɗa ya taya Muttaƙa Rabe murnar naɗa shi minista

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya taya sabon ministan gidaje da raye birane Injiniya Muttaƙa Rabe Darma murnar samun muƙamin minista a gwamnatin Tinubu Gwamna Raɗɗa ya yaba da ƙoƙarin shugaban ƙasa wajen cigaban ƙasa. Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan cewa Dakta Muttaƙa Darma yana da ƙwarewa da zai iya kawo ci gaba a fannin gidaje da raya birane a matakin ƙasa. Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa wannan naɗin wata alama ce ta amincewa da ƙwarewa, jajircewa da kuma halayen shugabanci na Dakta Darma. “Mun yi alfahari da ganin ɗaya daga cikin ‘ya’yanmu…
Read More
Sojojin sama sun hallaka ‘yan ta’adda da Dama a dajin Sambisa

Sojojin sama sun hallaka ‘yan ta’adda da Dama a dajin Sambisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojin saman Nijeriya ta kashe wasu ‘yan ta’adda da dama bayan kai wani hari na musamman ta sama a yankin Yuwe da ke cikin dajin Sambisa a jihar Borno kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa. Majiyoyin soji sun shaida wa wata kafar yada labarai mai bibiyar yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi cewa an kai harin ne da yammacin ranar Lahadi da misalin karfe 5:45. An ce harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da kuma sa ido da aka yi, wanda ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda…
Read More
JAMB: Sama da ɗalibai 500 masu laruar gani ne su ka zana jarabawar UTME ta bana

JAMB: Sama da ɗalibai 500 masu laruar gani ne su ka zana jarabawar UTME ta bana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Akalla ɗalibai 536 masu nakasar gani ne su ka rubuta jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta  2026 (UTME), tare da sauran masu bukata ta musamman a fadin Nijeriya. Shugaban Kwamitin Daidaiton Dama na JAMB (JEOG), Farfesa Emeritus Peter Okebukola, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Litinin a Abuja, a lokacin kaddamar da zaman jarabawar musamman. Ya ce an shirya gudanar da jarabawar ga ɗalibai 536 a cibiyoyi 11 da aka ware a fadin ƙasar nan, tare da tanade-tanade na musamman da suka dace da bukatunsu.…
Read More
Fadar Shugaban ƙasa ta lissafo nasarorin sojojin Nijeriya, ta ƙalubalanci masu suka

Fadar Shugaban ƙasa ta lissafo nasarorin sojojin Nijeriya, ta ƙalubalanci masu suka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana wasu daga cikin nasarorin da dakarun sojin Nijeriya suka samu a yaƙi da ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar nan, tare da sukar masu mayar da hankali kan gazawa kawai ba tare da la’akari da irin nasarorin da ake samu ba. Mai magana da yawun shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce manufarsa ita ce wayar da kan jama’a kan irin ƙoƙarin da dakarun sojin ke yi a fagen yaƙi da ta’addanci. Onanuga…
Read More
Dakarun sojin Nijeriya sun ragargaji maɓoyar ’yan bindiga a Bauchi

Dakarun sojin Nijeriya sun ragargaji maɓoyar ’yan bindiga a Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya tabbatar da cewa dakarun sojin Nijeriya sun samu gagarumar nasara wajen fatattakar daruruwan ’yan bindiga tare da ruguza sansanoninsu a wasu samame na hadin gwiwa da aka gudanar a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala wani taron tsaro na sirri a fadar gwamnatin jihar da ke Bauchi. Ya ce an samu wannan nasara ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin sojoji, ’yan sanda, sauran hukumomin tsaro, da kuma dakarun sa-kai (ɓigilante). A cewarsa, samamen ya fi mayar…
Read More
Masu yi wa ƙasa hidima 500 na shirin karɓar horo a Zamfara

Masu yi wa ƙasa hidima 500 na shirin karɓar horo a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau An turo sama da masu yi wa ƙasa hidima 500 Jihar Zamfara da suka fara karɓar hoto ƙarƙashin shirin hukumar kula da masu yiwa ƙasa hidima ta Kasa (NYSC) a hukumance a yau Juma'a don shekarar hidimar 'A' ta 2026. Mai Shari'a Murtala Abdullahi, a ma'aikatar shari'a ta Jihar Zamfara ya jagoranci rantsar da masu yiwa ƙasa hidimar a sansanin horar da matasan da ke cibiyar horar da malamai ta UBEC, da ke Gusau. Da yake bayani a buɗe horaswar, Gwamna Dauda Lawal wanda Sakataren Dindindin na ma'aikatar matasa da wasanni, Alhaji Nasiru Galadima Ƙaura…
Read More
Sarki Sunusi ya caccaki gwamnatin tarayya kan cigaba da ciyo bashi duk da janye tallafin mai

Sarki Sunusi ya caccaki gwamnatin tarayya kan cigaba da ciyo bashi duk da janye tallafin mai

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya soki yadda gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur a ƙasar. Sanusi ya bayyana hakan ne a wani taron shekara-shekara na The Niche Annual Lecture 2026 da aka gudanar a Legas, inda ya ce bai dace a dena bada tallafin mai ba amma a ci gaba da karɓar bashi ba tare da ganin amfanin hakan ba. Ya ce cire tallafin ya zama dole saboda tsadar da yake haifarwa, tare da nuna cewa yanzu Najeriya ta fara tace…
Read More
Tinubu ya ware biliyan N17 don bunƙasa walwalar al’umma a mazaɓu 8,804

Tinubu ya ware biliyan N17 don bunƙasa walwalar al’umma a mazaɓu 8,804

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaba Bola Tinubu ya amince da fitar da kudi naira biliyan 17 domin gudanar da wani babban shiri na samar da ci gaba a matakin mazaɓu da ke faɗin ƙasar nan. Wannan tallafi, wanda aka yi wa laƙabi da “Community-Based National Social Action Fund”, an kafa shi ne domin taba rayuwar talakawa kai-tsaye a dukkanin mazabu 8,804 na Nijeriya, ta hanyar ba su damar gudanar da ayyukan da suka fi damunsu a yankunansu. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya ta fitar ranar Laraba, wadda mataimakin daraktan yaɗa labarai,…
Read More
Zargin bada bayanan ƙarya: An gurfanar da shugaban tsagin PDP, Tanimu Turaki

Zargin bada bayanan ƙarya: An gurfanar da shugaban tsagin PDP, Tanimu Turaki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  An gurfanar da shugaban ɓangaren jam’iyyar PDP, Sanata Tanimu Turaki, a gaban Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Maitama, bisa zargin bayar da bayanan ƙarya ga ‘yan sanda. An gurfanar da Turaki ne kan tuhuma guda ɗaya da Babban Sufeton ‘Yan Sanda (IGP) ya shigar a kansa, inda ake zarginsa da aikawa da ƙorafi a takardarsa mai ɗauke da kwanan watan 5 ga Oktoba, 2022, zuwa ga IGP, yana zargin wani mai suna Sa’idi Mohammed Mainasara da nufin cutar da shi ta hanyar amfani da ikon ‘yan sanda. Masu gabatar da ƙara…
Read More