ukarofi

12570 Posts
Tinubu ya amince da tallafin kamfanonin jiragen sama kan tsadar mai

Tinubu ya amince da tallafin kamfanonin jiragen sama kan tsadar mai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta amince da wasu muhimman matakan tallafi domin rage wa kamfanonin jiragen sama raɗaɗin tsadar man jirgi (Jet A1), wanda ke barazana ga ci gaba da harkokin sufurin jiragen sama a Nijeriya. Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, bayan wani muhimmin taro da ya shafe sa’o’i ana gudanarwa tare da wakilan Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, masu kamfanonin jiragen sama da kuma dillalan mai. An gudanar da taron ne sakamakon ƙara tsanantar farashin man jirgi, wanda masu harkar sufurin jiragen…
Read More
Ana tuhumar manajar bankin First da zargin ƙirƙirar takardun Dala 400,000

Ana tuhumar manajar bankin First da zargin ƙirƙirar takardun Dala 400,000

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata babbar manaja a bankin First Bank ta gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legos bisa zargin ƙirƙirar takardar bogi domin ɓoye bambancin canjin kuɗaɗen waje a wata yarjejeniyar bashi ta dala 400,000. Wacce ake tuhuma, mai suna Nnedimma Arah, manajar reshen bankin na Dosunmu a tsibirin Legos, kuma ƙwararriyar mai rajista a fannin lissafin kuɗi, jami’an bincike na SCID da ke Panti-Yaba ne suka gurfanar da ita a kotu ranar Talata. Ana tuhumar ta ne da laifi guda ɗaya na ƙirƙirar takarda kuɗi. Lauyan gwamnati, Emmanuel Eze, ya shaida wa kotu cewa an…
Read More
Tsaro: Majalisar Dattawa ta nemi a dakatar da siyasa a Kano da jihohi bakwai

Tsaro: Majalisar Dattawa ta nemi a dakatar da siyasa a Kano da jihohi bakwai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta yi la’akari da ɗaukar matakan gaggawa, ciki har da yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a wasu jihohi takwas da ke sahun gaba wajen fama da matsalar tsaro, sakamakon yadda hare-haren ’yan ta’adda ke ƙara ƙamari a wasu sassan ƙasar. Rahotanni sun nuna cewa wannan kira ya biyo bayan wani batu na gaggawa da Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya gabatar a zaman majalisar, inda ya jaddada cewa matsalar tsaro ba ta yankin guda ba ce, illa matsala ce ta ƙasa baki ɗaya da ke…
Read More
Kotu ta yi bayanin dalilan hana belin El-Rufai

Kotu ta yi bayanin dalilan hana belin El-Rufai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayyana cikakkun dalilan da suka sa ta ƙi amincewa da buƙatar beli da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya gabatar, bayan fitar da sahihin kwafin hukuncinta (CTC) da aka yanke a ranar 21 ga Afrilu. Alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Darius Khobo, ya ce barin El-Rufai a tsare yana da muhimmanci domin tabbatar da samuwarsa a kotu yayin da za a fara shari’a, yana mai jaddada cewa hakan ya dace da muradun adalci. Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) ce ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda…
Read More
Majalisar Jigawa ta fara binciken Badaru da shugabannin ƙananan hukumomi

Majalisar Jigawa ta fara binciken Badaru da shugabannin ƙananan hukumomi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata gagarumar cakwakiya ta siyasa na kunno kai a Jihar Jigawa bayan Majalisar Dokokin Jihar ta ƙaddamar da wani bincike mai zurfi kan tsohon gwamnan jihar, Mohammed Badaru Abubakar, tare da shugabannin ƙananan hukumomi 27, bisa zargin almundahana da rashin sarrafa kuɗaɗen jama’a yadda ya kamata. A zaman majalisar da aka gudanar, ’yan majalisar sun amince baki ɗaya da rahoton Kwamitin Asusun Jama’a, inda suka bayar da umarnin dawo da duk wasu kuɗaɗen da ake zargin an karkatar da su tsakanin shekarun 2019 zuwa 2024. Shugaban kwamitin, Hon. Isyaku Abubakar, ya bayyana cewa binciken ya biyo…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta yi wa masu ƙaramin ƙarfi 100 auren gata

Gwamnatin Zamfara ta yi wa masu ƙaramin ƙarfi 100 auren gata

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya tare da ɗaukar nauyin auren gata ga mutum 100 da aka zaɓo daga rukunin marasa ƙarfi a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar. Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa marasa galihu da inganta rayuwarsu ta hanyar tsare-tsare masu amfani. Ya bayyana hakan ne ta bakin Mataimakin Gwamna, Mani Mummune, wanda ya wakilce shi a wajen bikin. A cewarsa, gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su taimaka wajen ɗaukaka rayuwar jama’a, musamman waɗanda ke cikin buƙata. Ya ƙara…
Read More
Tinubu ya nemi sahalewar majalisa domin karɓo bashin Dala miliyan 500

Tinubu ya nemi sahalewar majalisa domin karɓo bashin Dala miliyan 500

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawan ta amince da ciyo bashin fiye da dala miliyan 516 daga babban bankin Jamus (Deutsche bank), domin aikin wani ɓangare na babbar hanyar Sakkwato zuwa Badagry. A cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Godswil Akpabio, Shugaban ƙasar ya ce an tsara aikin gina kilomita 100 na titin ne domin ya haɗa Arewa maso yammacin ƙasar da Kudu maso Yammaci. A cewar sa, babbar hanyar za ta taso ne daga Illela a jihar Sakkwato, ta bi ta jihohin Kebbi da Neja da Kwara da…
Read More
ADC: Peter Obi ya yi ganawar sirri da Gwamna Bala a Bauchi

ADC: Peter Obi ya yi ganawar sirri da Gwamna Bala a Bauchi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fitaccen ɗan siyasa a jam’iyyar ADC kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi inda ya gana da Gwamnan jihar, Bala Mohammed, a wani taro na sirri da aka gudanar a ranar Alhamis. Ganawar ta gudana ne a ɗakin taro na musamman da ke Gidan Gwamnati, ba tare da bayyana cikakken dalilin haɗuwar ba, lamarin da ya ƙara janyo hankalin masu bibiyar harkokin siyasa a ƙasar. Rahotanni na nuni da cewa wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yiwuwar sauyin sheƙa na Gwamna Bala Mohammed gabanin…
Read More
Ta’addanci: Remi Tinubu ta nemi taimakon limaman coci na duniya

Ta’addanci: Remi Tinubu ta nemi taimakon limaman coci na duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ƙasashen duniya da su fahimci matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta yadda ya dace, tare da kauce wa jirkitar da bayanai da ka iya kawo cikas ga samar da zaman lafiya mai ɗorewa. Ta bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ta karɓi bakuncin tsohon Archbishop na Canterbury, Rt. Rev. Justin Welby, a Abuja, a wata ganawa da ta mayar da hankali kan tattaunawar addinai da hanyoyin samar da zaman lafiya. A cewar mai taimaka mata na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Busola…
Read More
2027: Yadda hukuncin kotu zai rikita ADC da PDP

2027: Yadda hukuncin kotu zai rikita ADC da PDP

*Ana cikin zaman ɗar-ɗar bayan da Kotun ƙoli ta jinkirta yanke hukunta Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A wani sabon salo na rikice-rikicen dambarwar siyasa da suke ƙara dagula harkokin jam’iyyun adawa a Nijeriya, Kotun ƙoli ta Nijeriya ta jingine yanke hukunci kan shari’un da suka shafi rikicin shugabanci a cikin jam’iyyun ADC da kuma PDP, lamarin da ya haifar da damuwa da zaman ɗar-ɗar kan yiwuwar shigar su babban zaɓen 2027. Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Lawal Garba ne ya sanar da cewa, za a fitar da ranar yanke hukunci bayan kammala gabatar da hujjoji daga ɓangarorin…
Read More