ukarofi

12643 Posts
Majalisar Ribas ta dakatar da shirin tsige Fubara

Majalisar Ribas ta dakatar da shirin tsige Fubara

Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta dakatar da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Odu daga muƙamansu, bayan tsoma bakin Shugaban ƙasa, Bola Tinubu. An cimma wannan matsaya ne a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda aka bayyana cewa za a dakatar da duk wani ci gaba kan batun har sai kotuna sun yanke hukunci kan ƙararrakin da ke gabansu, tare da kammala shawarwarin siyasa da ake yi. A watan Janairu ne ‘yan majalisar suka fara yunƙurin tsige gwamnan da mataimakiyarsa bisa zargin “mummunan rashin ɗa’a a ofis” kamar yadda Sashe na 188 na Kundin…
Read More
Jigawa, Legas da Sakkwato ne kan gaba wajen rajistar zaɓe, inji INEC

Jigawa, Legas da Sakkwato ne kan gaba wajen rajistar zaɓe, inji INEC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), ta sanar da ƙaruwar yawan sabbin masu rajistar katin zaɓe a zagaye na biyu na rajistar masu kaɗa ƙuri’a, inda sama da ’yan Nijeriya miliyan 1.2 suka kammala rajista zuwa ranar 13 ga Fabrairu, 2026. A sabuwar sanarwar da hukumar ta fitar ta shafinta na ɗ, INEC ta bayyana cewa jimillar mutane 1,228,648 ne suka kammala rajista a ƙarƙashin Mataki na II, Mako na Shida. Wannan adadi ya ƙaru daga 884,737 da aka samu a ƙarshen Mako na Biyar, alamar cewa sha’awar rajistar zaɓe na ƙaruwa a faɗin…
Read More
Tinubu ya nemi gwanjon jiragen Jamus don ƙarfafa tsaro

Tinubu ya nemi gwanjon jiragen Jamus don ƙarfafa tsaro

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi gwamnatin Jamus da ta miƙa wa Nijeriya wasu tsofaffin jiragen sama masu saukar ungulu domin ƙarfafa ayyukan leƙen asiri da sa ido a yankin Sahel, wanda ke fama da matsalar tsaro. Shugaban ya bayyana buƙatar ne yayin wata tattaunawa ta waya da Kansilan Jamus, Friedrich Merz, a yammacin ranar Laraba, tattaunawar da ta ɗauki kusan mintuna goma. A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, shugabannin biyu sun amince da zurfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, tare da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a ɓangarorin tsaro, lantarki da layin…
Read More
Kula da jiragen Shugaban ƙasa a wajen Nijeriya ke gurgunta kasafin kuɗin tsaro – ONSA

Kula da jiragen Shugaban ƙasa a wajen Nijeriya ke gurgunta kasafin kuɗin tsaro – ONSA

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kuɗin da Nijeriya ke kashewa kan Jiragen Shugaban ƙasa ya ƙaru sosai saboda shirye-shiryen gyara a ƙasashen waje, Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro na ƙasa (ONSA) ya shaida wa Majalisar Dattawa a lokacin zaman kare kasafin kuɗi na 2026. Manhaja ta ruwaito cewa Mohammed Sanusi, Sakataren Dindindin a Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro na ƙasa ne ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaron ƙasa da Leƙen Asiri don gabatar da ƙiyasin da hukumar ta tsara na kasafin  2026. Sanusi ya bayyana cewa ci…
Read More
Sojoji sun sake kama wasu bisa zargin yunƙurin kifar ga gwamnatin Tinubu

Sojoji sun sake kama wasu bisa zargin yunƙurin kifar ga gwamnatin Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojojin Nijeriya ta sake kama wasu mutane bisa zargin hannu a wani sabon shiri na kifar da gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. A cewar Sahara Reporters, daga cikin waɗanda aka tsare har da Manjo H. Yusuf na rundunar sojojin ƙasa, wanda ya kammala kwas na manyan jami’ai a Kwalejin Horas da Hafsoshin Soji da ke Jaji. Ana tsare da shi tare da wasu da ake zargi da hannu a yunƙurin juyin mulki, kodayake har yanzu hukumomi ba su fito da cikakken bayani kan zargin ba. Bincike kan lamarin ya fara…
Read More
Gwamnatin Kano ta fara duba tsarin ciyar da masu azumi a watan Ramadan

Gwamnatin Kano ta fara duba tsarin ciyar da masu azumi a watan Ramadan

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta fara rangadin duba yadda ake shirya da rarraba abinci ga masu azumi a faɗin jihar a cikin watan Ramadan mai alfarma. Rangadin na da nufin tabbatar da cewa ana gudanar da shirin ciyarwar cikin tsari, tare da kiyaye tsafta da bin ƙa’idojin da gwamnati ta gindaya domin amfanin al’umma. Shugaban kwamitin kuma kwamishinan harkokin Addini, Sheikh Tijjani Auwal Sani, ne ya jagoranci tawagar yayin ziyarar da suka kai cibiyoyi daban-daban na rabon abincin. Ya bayyana cewa gwamnati ta ƙaddamar da wannan duba ne domin tabbatar da cewa masu azumi suna samun…
Read More
2026: Nasarori da akasin bikin kamun kifin Argungu

2026: Nasarori da akasin bikin kamun kifin Argungu

*Yadda bikin ya zama na musamman a Afrika *An rasa rayukan mutum biyu *An sace fitilun da aka saka jim kaɗan bayan kammala bikin *An yi ƙorafi kan tsafta da kwamitoci Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Biki nan mai cike da tarihi da ƙayatarwa a Afrika na kamun kifi a Argungu, wanda ake gudanarwa shekara-shekara, yana ɗaya daga cikin bukukuwan nuna al'adun gargajiya da ake yi a garin Argungu da yake a Jihar Kebbi, inda nan ne cibiyar Daular Muhammadu Kanta, wanda yana ɗaya daga cikin gwamnonin Muhamma Askia na Masarautar Songhai a baya. Bikin kamun kifi na Argungu…
Read More
Juyin mulki: DIA ta miƙa Sheikh Sani Khalifa hannun DSS

Juyin mulki: DIA ta miƙa Sheikh Sani Khalifa hannun DSS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Leƙen Asiri ta Soji (DIA) ta miƙa Malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Abdulkadir Zariya, hannun Hukumar Farin Kaya (DSS), domin ci gaba da bincike kan zarginsa da hannun a ƙoƙarin yin juyin mulki a Nijeriya. An kama malamin ne saboda zarginsa da hannu wajen yunƙurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu. A baya, wani alƙalin Kotun Tarayya da ke Abuja, ya umarci DIA da ta kawo malamin kotu a ranar 18 ga watan Fabrairu domin duba yiwuwar bayar da belinsa. Amma a lokacin sauraron shari’ar, lauyansa ya shaida wa kotu cewa DIA ba ta…
Read More
’Yan bindiga sun tilasta wa ɗaruruwan mutane tserewa daga Neja zuwa Jamhuriyar Benin

’Yan bindiga sun tilasta wa ɗaruruwan mutane tserewa daga Neja zuwa Jamhuriyar Benin

Daga. SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Borgu da Agwara, Injiniya Abdurrahman Bala Gambo, ya bayyana cewa ɗaruruwan mazauna karkara daga ƙaramar Hukumar Borgu da ke Jihar Neja, sun tsere zuwa Jamhuriyar Benin sakamakon hare-haren ’yan bindiga. Gambo, ya shaida wa BBC Hausa cewa ’yan bindigar sun kai hari garin Konkoso, lamarin da ya tsorata jama’a har suka tsere daga muhallansu. “Sun shiga Konkoso da nufin cin zarafin mutane, amma cikin ikon Allah babu wanda aka kashe domin mazauna garin sun riga sun tsere kafin su iso,” inji shi. Ya ƙara da cewa yawancin mutanen…
Read More
Samar da motoccin sulke: Ministan Tsaro ya yaba da jajircewar Gwamnan Zamfara a fannin tsaro

Samar da motoccin sulke: Ministan Tsaro ya yaba da jajircewar Gwamnan Zamfara a fannin tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa sayo motoci masu sulke, jiragen sa-ido marasa matuƙa (drones) da sauran kayan aiki domin ƙarfafa wa rundunonin tsaro a jihar. A wani biki da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Gusau ranar Laraba, Gwamna Lawal ya miƙa motoci 25 na zamani masu sulke (Armoured Personnel Carriers) ga jami’an tsaro, domin ƙara musu kariya yayin da suke gudanar da aiki a yankunan da ke da haɗarin tsaro a faɗin jihar. Sanarwar da mai magana da yawun…
Read More