ukarofi

12643 Posts
Haɗewar azumin Musulmi da na Kirista lokaci ɗaya dama ce gare mu – Tinubu

Haɗewar azumin Musulmi da na Kirista lokaci ɗaya dama ce gare mu – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga Musulmi da Kiristoci su ƙarfafa haɗin kai yayin da lokutan azumin Ramadan da na Kirista wato Lent suka zo a lokaci guda a bana, yana mai cewa hakan wata dama ce ta ƙarfafa zumunci tsakanin mabiya addinai. A cikin sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya bayyana cewa ba kasafai ake samun haɗuwar lokutan ibadar biyu ba, kuma hakan na tunatar da 'yan Nijeriya cewa "su al'umma ɗaya ce a wurin ubangiji duk da bambancin addinai". Ya ce "ga Kiristoci, lokacin azumi lokaci…
Read More
Rikici ya ɓarke yayin naɗa sabon dagacin Madobi a Kano

Rikici ya ɓarke yayin naɗa sabon dagacin Madobi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  An samu ɓarkewar rikici a Madobi bayan da aka fara shirye-shiryen naɗa sabon Dagacin Madobi sakamakon rasuwar tsohon dagacin, Alhaji Umaru Mahmud. Rikicin ya samo asali ne bayan wasu daga cikin masu neman kujerar dagacin sun kalubalanci tsarin da suka ce Hakimin Madobi, Alhaji Saleh Musa Saleh, ya bi wajen zaben sabon dagacin. ɗaya daga cikin masu neman kujerar, Tafidan Madobi, Alhaji Hussain Sarki Aliyu Rabakaya, ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda aka gudanar da tsarin zaben. Ya ce ba a bi ƙa’idojin al’ada da tsarin da aka saba amfani da su ba wajen zaɓar…
Read More
Kaduna: Dalibai a makarantar mata sun koka kan rashin ruwan sha da banɗakuna

Kaduna: Dalibai a makarantar mata sun koka kan rashin ruwan sha da banɗakuna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dalibai mata na Makarantar Firamare ta Jalo Model da ke Rigachikun a Jihar Kaduna sun nuna damuwarsu kan ƙarancin kayayyakin tsafta da ruwan sha a makarantar, lamarin da suka ce yana shafar karatunsu. Sun bayyana cewa rashin isassun bandakuna masu tsafta da kuma ruwan sha mai kyau na hana su maida hankali a aji tare da kiyaye tsaftar jikinsu, musamman a lokutan karatu. Yawancin ɗaliban, waɗanda ke aji na Basic Nine, sun bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ƙungiyar Education as a ɓaccine (EɓA) ta kai makarantar domin ƙarfafa gwiwar ‘yan mata su…
Read More
Tinubu ya yi kira ga malamai da sarakuna su sa hannu wajen yaƙi da cutattuka a Nijeriya

Tinubu ya yi kira ga malamai da sarakuna su sa hannu wajen yaƙi da cutattuka a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci sarakuna da malaman addini kan su sa hannu a yaƙin da ake yi wajen gujewa kamuwa da cututtuka, yana mai cewa kula da lafiyar ‘yan Nijeriya nauyi ne a kan kowa. Shugaba Tinubu ya yi wannan kira ne a ranar Talata a yayin da yake magana a taron malamai da sarakuna da kiwon lafiya da aka yi a gidan gwamnati a Abuja. “Yaƙi da cututtuka nauyi ne a kan kowa, kuma a matsayina na shugaban ƙasa, ga ni a gabanku cikin mutuntawa, ina tabbatar muku cewa wannan nauyi ne…
Read More
Gyaran dokar zaɓe: Majalisar Dattawa ta yi wani gyara da zai bai wa INEC damar sake saka ranar zaɓen 2027

Gyaran dokar zaɓe: Majalisar Dattawa ta yi wani gyara da zai bai wa INEC damar sake saka ranar zaɓen 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar dattawa a ranar Talata ta soke matakin da ta ɗauka kan sashe na 28 na kundin dokar zaɓe, inda ta rage yawan kwanakin da INEC za ta sanar da gudanar da zaɓe daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 180. Sannan ta yi kiran sashen da ya tilasta wa INEC sanar da shirin gudanar zaɓe kafin kwana 300 daga ranar da za ta fitar da jadawalin zaɓe. Majalisar ta ce, wannan mataki ya zama wajibi bayan da gano kuskure a cikin sashe na 22 na ƙudurin da ya haɗa da sashe na 60 wanda ya…
Read More
Watan Ramadana Mai Albarka

Watan Ramadana Mai Albarka

Musulmi a Nijeriya da sauran sassan duniya sun fara azumin watan Ramadana na shekarar 1447AH/2026 bayan sanarwar da Shugaban Majalisar ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya fitar bayan tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan. Sanarwar ta biyo bayan rahotannin kwamitocin ganin wata na jihohi daban-daban da kuma tantancewar kwamitin ganin wata na ƙasa. Kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, ganin jinjirin watan Ramadan ke nuna ƙarshen watan Sha’aban da kuma fara azumi. A saƙonsa, Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin amfani da wannan wata wajen ƙarfafa zaman lafiya, hadin kai da…
Read More
Tsaro, ilimi da lafiya suka fi samun kaso mai tsoka a kasafin kuɗin 2026 na Katsina – Malik Anas

Tsaro, ilimi da lafiya suka fi samun kaso mai tsoka a kasafin kuɗin 2026 na Katsina – Malik Anas

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana tsarinta na kasafin kuɗin shekarar 2026, inda ta ware biliyoyin nairori domin bunƙasa harkar tsaro, ilimi, lafiya, tattalin arziƙi, noma da ababen more rayuwa, a daidai lokacin da take ƙoƙarin aiwatar da ajandar Gwamna Dikko Raɗɗa mai taken “Building Your Future.” Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziƙi, Alhaji Malik Anas, ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Katsina , yana mai bayyana kasafin kuɗin a matsayin “na al'umma, wanda aka tsara bayan tattaunawa da al’umma a ɗaukacin unguwanni 361 na jihar." Kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar ta sake…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta gina rijiyoyin burtsatse 3,000

Gwamnatin Katsina za ta gina rijiyoyin burtsatse 3,000

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya faɗawa manema labarai haka da ya ke bayani kan sakamakon zaman majalisar zartarwa karo na huɗu wanda aka gudanar a zauren majalisa wanda gwamna Dikko Raɗɗa ya jagoranta. A cewarsa, majalisar ta tattauna sosai kan manufofi da ayyukan da za su inganta rayuwar jama’a, ƙarfafa masu rauni, da tabbatar da ɗorewar samun muhimman ayyuka a faɗin Jihar Katsina a cewar kwamishinan. Kwamishinar Harkokin Mata, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta bayyana cewa majalisar ta amince a fara ɗaukan matakan da suka dace domin aiwatar da manufar ƙasa ta…
Read More
Nasarata a Gasar Tsangayar Gusau ce ta ba ni lasisin amsa sunan marubuciya  – Ummi Abba

Nasarata a Gasar Tsangayar Gusau ce ta ba ni lasisin amsa sunan marubuciya  – Ummi Abba

"Ko yau na ajiye alƙalami zan iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Akwai marubutan Hausa da dama dake bayar da gudunmawa sosai ga cigaban rubutun Adabi, sai dai ba kasafai ka ke jin amon su daga Jihar Borno ba, duk kuwa da kasancewar akwai marubuta da dama da suka shahara daga wannan yankin. Fatima Abba Muhammad, ba sunanta ne kawai ya bayyana ba, ta kasance ma a cikin gwarazan da suka yi fice a Gasar Tsangayar Gusau, ɗaya daga cikin manyan gasannin marubutan Hausa da ake sa su a Arewacin Nijeriya, inda ta samu nasara…
Read More
RIC ta ƙaddamar da Ambasada Isah da wasu sabbin shugabannin kwamitin na Nasarawa

RIC ta ƙaddamar da Ambasada Isah da wasu sabbin shugabannin kwamitin na Nasarawa

DAGA JOHN DOGO WADA, a Keffi Ƙungiyar nan ta tabbatar da nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 da ake kira Renewed Hope Independent Support Groups Committee (RIC) a turance ta ƙaddamar da mai martaba sarkin baka da ke Masaka a ƙaramar hukumar Karu jihar Nasarawa Alhaji Isah Kogi a matsayin Ambasadan zaman lafiya na shiyar Arewa ta tsakiya tare da wasu shugabannin kwamitin na jihar Nasarawa. An gudanar da taron ne a Time Square hotel da ke garin Masaka ranar Laraba 18 ga watan Maris 2026. Idan ba a manta ba a 'yan kwanakin baya ne shugaban…
Read More