ukarofi

12643 Posts
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da shirin tsara biranen Katsina

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da shirin tsara biranen Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Biranen da za a fara da su sun haɗa da Katsina, Daura da Funtua kamar yadda gwamnan ya sanar a jawabinsa kafin ƙaddamar da shirin a ɗakin taro na masaukin shugaban ƙasa da ke cikin gidan gwamnatin jihar. Ya ce tsara biranen har na tsawon shekara 14 zai haɗa da sauran ƙananan hukumomi 34 da ke jihar. Malam Dikko ya bayyana cewa tun 1978 ba a sake tsari irin wannan ba wanda hakan yasa ake gine gine ba tsari. "Musamman sabbin wurare da akayi gine gine zaka ga yawanci ba magudanan ruwa da fitar da…
Read More
Ko kun san daga ina ilimin lissafi ya samo asali?

Ko kun san daga ina ilimin lissafi ya samo asali?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Duk da cewa babu wanda ya san asalin inda ilimin lissafi ya samo asali, amma a yau Blueprint Manhaja za ta yi duba ne kai tsaye zuwa ga ilimin lissafi, duk da cewa babu wani abu da ya rage game da daɗaɗɗen wajen tarihin lissafi da aka lalata a ƙarni na 13, amma mun binciko tare tattaro bayanan masana dangane da inda wajen yake da kuma yadda wajen yake. Sanin asalin ilimin lissafi abu ne mai wahalar gaske amma an fara ganin lissafai masu wahala ne a kusan shekara ta 3000 kafin bayyanar Annabi Isa (300…
Read More
Tumbi: Barazanar lafiya da yadda za a kare kai a zamanin yau

Tumbi: Barazanar lafiya da yadda za a kare kai a zamanin yau

Tare da BILKISU YUSUF ALI A wannan zamani da duniya ke tafiya da sauri, sauyin rayuwa da ɗabi’un cin abinci ya jefa mutane da dama cikin matsalolin lafiya da ba a fiye kulawa da su a baya ba. ɗaya daga cikin irin waɗannan matsaloli ita ce tumbi, wadda ta zama ruwan dare gama gari ga maza da mata, matasa da manya. Duk da cewa mutane da dama na kallon tumbi a matsayin matsalar kamanni kawai, masana lafiya sun jaddada cewa tumbi babbar barazana ce ga lafiyar ɗan Adam idan ba a ɗauki matakin da ya dace ba. Tumbi dai ba…
Read More
Haƙƙin Iyali: Ciyarwa

Haƙƙin Iyali: Ciyarwa

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na wannan mako, sannunku da jimirin bibiyar jarida mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan makon, za mu tattauna kan darasin da a wannan zamani ya fi ci wa mata tuwo a ƙwarya tsayin lokaci, musamman ma a ƙasar Hausa. kafin mukai ga tattauna ƙorafin mata kan rashin ciyar da su da mazansu ke yi, bari mu fara kan mazan wanda wataƙila mu samo wata mafita ko fahimta a cikin lamarin. Akwai wani lokaci can bayan a kafar sadarwa ta ɗ wanda a baya aka fi sani da…
Read More
Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (3)

Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (3)

Daga AISHA ASAS 5. Shan ruwa isasshe a kullum: Kamar yadda muka taɓa faɗa a wannan shafin shan ruwa ba wai iya kawar da ƙishi ne aikin sa ba kamar yadda mutane da dama suke gani. Muhimmancin ruwa yana da yawa a jikin ɗan adam, ciki kuwa har da fata. Domin fata na buƙatar ruwa don kasancewa cikin ƙoshin lafiya. Isasshen ruwa a jiki na sanya fata ta kasance cikin damshi, wanda hakan ke hana ta bushewa da zai iya kai ga matsaloli masu yawa. Suna taimakon fata a ɓangaren laushi da kuma ƙyalin da ake buƙata. A taƙaicee ruwa…
Read More
Gwamnatin Kano ta ba da umarnin rufe gidajen gala da hana kiɗan DJ

Gwamnatin Kano ta ba da umarnin rufe gidajen gala da hana kiɗan DJ

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano na sanar da ɗaukacin masu gudanar da gidajen wasanni a faɗin jihar wato gidajen gala da masu sana’ar sauti ta (DJ) cewa, daga ranar Laraba 18 ga Fabrairu, 2026, Hukumar ta rufe dukkan gidajen wasanninsu har zuwa ƙarshen watan Ramadan, wannan doka za ta fara aiki ne da misalin ƙarfe goma na dare. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Manhaja. Hukumar ta ɗauki wannan mataki ne domin ba da damar gudanar da…
Read More
Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da tallafa wa mata 500 da suka sami horo kan sana’o’i

Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da tallafa wa mata 500 da suka sami horo kan sana’o’i

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da shirin tallafa wa mata 500 da suka kammala horaswa a sana’o’i, wanda gidauniyar Auwal Lawal Daura (ALD) Foundation ta shirya. An gudanar da taron a garin Daura, tare da tallafin kuɗi domin su fara ko faɗaɗa harkokinsu. Kowace mahalarta ta samu jari na farko domin ƙarfafa sana’arta da fara kasuwanci iri-iri. Daga cikin sana’o’in da aka tallafa akwai ɗinki, ƙera takalma, yin sabulu, turare, man girki, da sauran sana’o’in da suka shafi ƙamshi. A jawabin sa, Gwamna Raɗɗa ya yaba wa gidauniyar ALD bisa…
Read More
Mutane 13 sun mutu sakamakon zazzaɓin Lassa cikin makonni biyu a Nijeriya

Mutane 13 sun mutu sakamakon zazzaɓin Lassa cikin makonni biyu a Nijeriya

Daga USMAN KAROFI a Abuja Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa (NCDC) ta sanar da cewa an samu sabbin mace-mace guda 13 sakamakon zazzaɓin Lassa cikin makonni biyu da suka gabata. A mako na huɗu na sanya ido kan cututtuka, an samu mutane 189 da ake zargi sun kamu, 28 da aka tabbatar sun kamu, da kuma mace-mace bakwai. Hakan ya kawo jimillar mutane 594 da ake zargi, 121 da aka tabbatar sun kamu, da kuma mace-mace 25 gaba ɗaya. A mako na gaba kuma, an sake samun ƙarin masu ɗauke da cutar inda aka samu mutane 160 da ake…
Read More
’Yan uwa mu nemi ilimi mu samu ɗaukaka

’Yan uwa mu nemi ilimi mu samu ɗaukaka

Shi jahilci ciwo ne mai matuƙar illa ga mutum da kuma al'umma baki ɗaya. Shi a ƙashin kansa jahili kan cutu sakamakon jahilcin da ya ke da shi, sannan kuma ayyukansa kan cutar da al'umma sakamakon ko yi da wasu za su yi da ayyukansa a rashin sani.  Ya zo cikin hadisi daga Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ke cewa; "shugaba ja'iri, da malami kangararre, da kuma mai ƙoƙari (a addini amma) jahili." Saboda haka kuwa jahili ba zai taɓa samun ɗaukaka wajen mutane ba, ballantana wajen Allah (S. W.A).  Shi kuwa haƙuri ɗaukaka…
Read More
Muhimmancin sada zumunci

Muhimmancin sada zumunci

Assalamu alaikum. Da farko dai, sada zumunci shi ne kyautatawa da jinƙai da bibiyar ’yan uwa (ma’abuta zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri gare su, da kawar da dukan sharri daga gare su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk ɓangare ne na sada zumunci. Har ila yau, ma’anar zumunci na game yin sallama ga ɗan uwa yayin haɗuwa da gaishe shi da ce masa Yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi. Sannan zuwa duba…
Read More