ukarofi

12643 Posts
Me ke kawo yawan mace-macen aure, shin rashin haƙuri ne ko rashin tarbiyya?

Me ke kawo yawan mace-macen aure, shin rashin haƙuri ne ko rashin tarbiyya?

Yawan mutuwar aure, matsala ce da ta zama ruwan dare a ƙasar Hausa. Alal misali, bincike na baya-baya da aka gudanar a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya nuna cewa rabin auren da ake yi na ƙarewa da saki. Shin ko me ke janyo wannan matsala? Wane irin tasirin ta ke yi a kan zamantakewar al'umma? Me ya kamata a yi don a rage matsalar? An yi kira ga gwamnati ta sanya darasin ilimin aure a cikin manhajar karatun sakandare da nufin rage yawan mace-macen aure a cikin al’umma. Mace-macen aure matsala ne da ya yawaita a ƙasar Hausa.…
Read More
Kimiyyar siyasar uban gida: Tasiri, makoma da silar rabuwa

Kimiyyar siyasar uban gida: Tasiri, makoma da silar rabuwa

Daga SADIK TUKUR GWARZO, GGA A siyasa, a ko’ina a faɗin duniya ana amfani da harshen 'biyayya, jagoranci gami da magajin mulki'. Shugabanni da dama su kan ce suna “gina shugabannin gobe”, ko “naɗa magaji”, ko kuma “tallafawa amintattun mabiyansu na siyasa", amma a ƙarƙashin wannan zance akwai lamari mai tsauri. Siyasar ubangida (godfatherism)— tsari ne da ikon siyasa ke zarcewa ta hannun mutane masu ƙarfin iko bayan cikar wa'adinsu, ba lallai ta hanyar hukumomi ko dokoki ba.  A nahiyoyi daban-daban, wannan tsari yana bin salo iri ɗaya: uban-gida ya ɗora yaronsa na siyasa, yaron nasa ya samu iko, sannan…
Read More
Sheikh Pakistan: Duk wanda ya sayi rariya…

Sheikh Pakistan: Duk wanda ya sayi rariya…

Daga ALI ABUBAKAR SADIK ’Yan Najeriya sun wayi gari katsam da sanarwar Babban Daraktan gudanarwa na hukumar aikin Alhazai ta kasa, Sheikh Sale Pakistan cewa yayi Murabus na kashin kansa, a wata takarda da ya aikewa shugaba Bola Tinubu. Sanarwar ta katsam ce, amma duk wanda ya ke bibiyar dambarwar da ke faruwa a hukumar ya san cewa sai an zo wannan wurin ko ba daɗe, ko ba jima. Idan ma banda kasa irin tamu, ai babu ta yadda za'a yi a baiwa Sheikh Sale Pakistan rike amanar wannan hukumar Mai matukar tasiri a kasar. Dalili kuwa shine idan ba…
Read More
Rikicin cikin gidan PDP: Shin jam’iyyar za ta tsira a 2027?

Rikicin cikin gidan PDP: Shin jam’iyyar za ta tsira a 2027?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa, wato PDP, tana tsaka mai wuya yayin da take tunkarar babban zaɓen 2027. Rikice-rikicen cikin gida, shari’o’in kotu da kuma sauya sheƙar manyan jiga-jigai sun jefa jam’iyyar cikin wani yanayi na rashin tabbas, lamarin da ya sa masana siyasa ke tambayar ko za ta iya sake farfaɗowa kafin babban zaɓe mai zuwa. Rikici mai zurfi tsakanin jiga-jigai: A halin yanzu, PDP ta kasu biyu, inda ɓangare ɗaya ke goyon bayan Nyesom Wike, wani kuma ke tare da Gwamna Seyi Makinde. Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan wata kotu a Ibadan ta…
Read More
Muƙamin da Gwamna Sule ya ba ni ba shi da alaƙa da siyasa – Ɗanmalikin Masaka

Muƙamin da Gwamna Sule ya ba ni ba shi da alaƙa da siyasa – Ɗanmalikin Masaka

Daga JOHN WADA a Keffi Wani matashi wanda gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa muƙamin mai taimaka masa na musamman a kwanan nan wato, Basiru Umar yace muƙamin bai da alaƙa da harkar siyasa kamar yadda wasu ke tunani. Ɗanmalikin Masakan Basiru Umar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da 'yan jarida ciki har da wakilin mu a gidansa da ke Masaka a ƙaramar hukumar Karu kwanaki kaɗan bayan karramawar da gwamnan ya yi masa. Yace a matsayin sa na mai wannan sarautar Ɗanmalikin Masaka da ya daɗe yana tare da mai martaba sarkin Masaka…
Read More
Yanar gizo riba ce ko akasi ga tsaro?

Yanar gizo riba ce ko akasi ga tsaro?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tun ba soshiyal midiya akwai wannan kulli a zuciyar abokan gaban Hausawa don alakar Hausawa da addini. Duk tarihin miyagun kashe-kashe a baya ai an san wadanda su ka aikata kama daga zubar da jinin Zangon Kataf, Yelwan Shendam har ma rikicin da ke faruwa a cikin Jos kafin ma na Gonin Gora. Duk Hausawa da a ke kira JASAWA sun san su waye ke kai mu su farmaki da kona gidajensu. A Jos ne masu kisan za su yi taro su raba gadon dukiyar Jasawa wai in sun kashe su, za su ci bulus, wannan…
Read More
A guji ɗaukar doka a hannu

A guji ɗaukar doka a hannu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Tun bayan kisan gillar da wasu matasa su uku suka yi wa wata mata mai suna Fatima Abubakar kisan gilla tare da yaranta su shida a unguwar ɗorayi Chiranchi cikin Jihar Kano, a ranar 17 ga watan Janairu, 2026 jama'a da dama suka fusata, duba da ganin yadda aka yi wa iyalin mummunan kisan gilla na rashin imani. Don haka ne ma yayin da aka ce an sake samun wani matashi da ya burma wa wata mata almakashi a ciki, a ƙoƙarin sa na sace mata waya, a cikin wannan unguwar dai ta ɗorayi, wasu fusata…
Read More
Ramadan: NULGE a Katsina ta yi kira ga Musulmai su taimaka wa mabuƙata

Ramadan: NULGE a Katsina ta yi kira ga Musulmai su taimaka wa mabuƙata

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi reshen jihar Katsina Kwamred Nasiru Wada Mai'adua ya yi wannan kira a wata takardar sanar wa da aka rabawa manema labarai. Ya ce a wannan wata mai daraja ya zama wajibi masu hali su fito su tallafawa marayu, masu buƙatar na musamman da marasa ƙarfi. "Ya zama wajibi mu fito mu tallafa wa waɗannan mabuƙata da kayan abinci, kuɗi da sutura domin suma su sami natsuwa wajen gudanar azumin watan Ramadan",inji shugaban NULGE. Kwamred Wada Mai'adua ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da yan majalisu na ƙasa da shugaban ƙananan hukumomi…
Read More
Wutar lantarki mai amfani da hasken rana a babban asibitin Funtua ya shekara bakwai ba ya aiki

Wutar lantarki mai amfani da hasken rana a babban asibitin Funtua ya shekara bakwai ba ya aiki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wannan wutar lantarkin na ɗaya daga cikin aikin mazaɓu da tsohon Sanata Bello Mandiya ya kawo a babban asibitin. Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua kwamred Mannir Suleiman ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a Katsina. Ya ce tunda na'urar ta tsaya shekara bakwai da suka wuce har yanzu babu wanda ya waiwaiyi aikin. Haka kuma kwamred Suleiman ya bayyana cewa babban na'urar samar da wutar lantarki (Generator) shima tuni ya bar aiki a asibitin. Ya bayyana cewa marasa lafiya na ƙananan hukumomin da ke maƙwabtaka da Funtua ke tururuwa zuwa asibitin neman…
Read More
Nasarawa 2027: Al’ummar Fulani sun yi alƙawarin yi wa Sanata Wadada ruwan ƙuri’u

Nasarawa 2027: Al’ummar Fulani sun yi alƙawarin yi wa Sanata Wadada ruwan ƙuri’u

DAGA JOHN DOGO WADA, Keffi A yayin da ake cigaba da shirye-shiryen zaɓukan shekarar 2027 dake tafe, al'ummar Fulani a jihar Nasarawa sunyi alƙawarin mara wa jam'iyyar APC mai ci a jihar baya a zaben 2027 ɗin inda duk suka bayyana cewa suna tare da shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwanmnan jihar Injiniya Abdullahi Sule da kuma uwa uba Sanata Ahmed Aliyu Wadada wato ɗan takarar kujerar gwamnan jihar a 2027 kenan ɗari bisa ɗari. Al'ummar Fulanin sun bayyana haka ne a jawabansu ɗaya bayan ɗaya a wajen wani babban taron ƙaddamar da sabbin shugabannin su na ƙungiyar nan…
Read More