ukarofi

12643 Posts
Zawarci a ƙasar Hausa 

Zawarci a ƙasar Hausa 

Daga AISHA ASAS "Aure duniya ce guda mai zaman kanta" (Ci gaba daga makon jiya) Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Gimbiya, sannunku da jimirin bibiyarmu. Ga waɗanda suka samu damar kasancewa da mu a satin da ya gabata, mun ɗauko tattaunawa kan ɗaya daga cikin sanannun ababe marar farin jini a Kasar Hausa, wato zawarci. Kamar yadda muka tattauna da dattiijiwa Yabi Muhammadu, wannan mako ma za mu waiwayi wasu matan a inda muke buƙatar ƙarin bayani, amma kafin nan, zan so mu karkata akalar rubutunmu kan halin da mata ke shiga yayin da suka baro gidan…
Read More
Shugaban SUBEB a Katsina ya ba mutane 727 tallafin kuɗi kimanin Naira miliyan 18

Shugaban SUBEB a Katsina ya ba mutane 727 tallafin kuɗi kimanin Naira miliyan 18

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mutanen da suka amfana waɗanda 'yan asalin ƙaramar hukumar Kaita ne sun haɗa da malamai, limamai, hakimai, magaddai,masu unguwanni. Saura sun haɗa da kungiyoyi su NULGE,NUT, ƙungiyar direbobi da na matasa maza da mata. Akwai kuma masu ruwa da tsaki na jam'iyar APC a ƙaramar hukumar da sauran shugabannin jam'iyar a matakai daban daban. A jawabinsa, shugaban SUBEB a Katsina Dr Kabir Magaji Gafiya wanda ya sassaka tallafin ƙarƙashin gidauniyar sa, ya bayyana cewa ya bada wannan tallafin kuɗi ne domin alummar yankin su sami abin sayen kayan masarufi ganin azumin watan Ramadan na ƙaratowa.…
Read More
An kama matashiya ‘yar 18 da zargin kai hari wata makaranta a Kanada 

An kama matashiya ‘yar 18 da zargin kai hari wata makaranta a Kanada 

Jami’an ‘yan sanda a Kanada sun bayyana cewa, wata matashiya mai shekaru 18, Jesse Van Rootselaar, ce ta kai harin bindiga a wata makaranta a yankin British Columbia, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara ciki har da ita kanta. Da farko an ruwaito mutuwar mutum goma, amma daga bisani aka gyara adadin zuwa tara. Lamarin ya faru ne a wata ƙaramar alƙarya mai mutane kusan 2,400 a Tumbler Ridge. ‘Yan sanda sun ce ana zargin ta fara kashe mahaifiyarta mai shekaru 39 da kuma ɗan uwanta ɗan shekara 11 a gida kafin ta nufi tsohuwar makarantar da ta…
Read More
Tattaunawar Trump da Netanyahu kan Iran: Babu wata matsaya da muka tsaida – Trump 

Tattaunawar Trump da Netanyahu kan Iran: Babu wata matsaya da muka tsaida – Trump 

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ganawarsa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ba ta haifar da wata yarjejeniya tabbatacciya ba dangane da batun Iran, sai dai an amince da ci gaba da tattaunawa. Wannan shi ne karo na bakwai da shugabannin biyu suka gana cikin watanni 13 da suka gabata. Trump ya jaddada cewa, duk wata yarjejeniya dole ta tabbatar da cewa Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ko makamai masu linzami ba. Isra’ila na son tattaunawar ta wuce batun nukiliya kadai ta hada da makaman ballistic da kuma goyon bayan ƙungiyoyin da take ɗauka a matsayin barazana.…
Read More
Faransa ta miƙa batun jami’in diflomasiyya mai alaƙa da Epstein ga masu shari’a 

Faransa ta miƙa batun jami’in diflomasiyya mai alaƙa da Epstein ga masu shari’a 

Gwamnatin Faransa ta sanar da masu gabatar da kara kan wani jami’in diflomasiyya mai suna Fabrice Aidan, wanda ake zargi da aikewa Jeffrey Epstein da wasu takardu na Majalisar ɗinkin Duniya. Sunan nasa ya bayyana a fiye da takardu 200 da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta fitar. Ministan harkokin wajen Faransa ya bayyana zargin a matsayin “mai matuƙar muni,” inda aka fara binciken cikin gida da kuma matakan ladabtarwa. Ana zargin ya tura sakonnin imel daga asusun sa na ƙashin kansa da kuma na Majalisar ɗinkin Duniya tsakanin 2010 da 2016. Wata majiya ta kusa da Shugaba Emmanuel Macron ta…
Read More
Dubban jama’a sun fito zaɓen raba gardama a Bangladesh

Dubban jama’a sun fito zaɓen raba gardama a Bangladesh

Dubban jama’a sun fito zaɓen raba gardama a Bangladesh, a zaɓen da ake kallon sa a matsayin makomar sabuwar siyasa bayan kifar da tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina a 2024 sakamakon bore na matasa (Gen Z). Mutane kusan miliyan 128 ne ke da rajistar kaɗa ƙuri’a, kuma zuwa rana ta tsaka, kaso 32.88% sun riga sun kaɗa ƙuri’unsu a yawancin cibiyoyin zaɓe 42,651. Zaɓen na fuskantar hamayya tsakanin kawancen jam’iyyun BNP ƙarƙashin Tariƙue Rahman da kuma Jamaat-e-Islami ƙarƙashin Shafiƙur Rahman. Hasashen ra’ayin jama’a na nuna BNP na da rinjaye. A birnin Dhaka, masu kaɗa ƙuri’a sun fara taruwa tun kafin buɗe…
Read More
Kamfanin tsaro na Amurka na neman damar bayar da tsaro a Gaza 

Kamfanin tsaro na Amurka na neman damar bayar da tsaro a Gaza 

Wani kamfanin tsaro na Amurka, UG Solutions, wanda a baya ya tura tsoffin sojoji ɗauke da makamai domin tsaron cibiyoyin rabon tallafi a Gaza, na tattaunawa da kwamitin “Board of Peace” na Shugaba Donald Trump kan sabuwar rawar da zai taka a yankin. Kamfanin ya bayyana hakan ne bayan rahotanni sun nuna yana ɗaukar ma’aikata masu iya Larabci da ƙwarewar yaƙi domin aiki a wuraren da ba a bayyana ba. Wata majiya mai masaniya kan shirin kwamitin ta tabbatar da cewa tattaunawar na gudana, ko da yake ba a cimma yarjejeniya ba tukuna. UG Solutions ya taɓa samar da tsaro…
Read More
NDLEA ta cafke ɗan kasuwa a Kano yana yunƙurin safarar hodar iblis zuwa Chana

NDLEA ta cafke ɗan kasuwa a Kano yana yunƙurin safarar hodar iblis zuwa Chana

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta cafke wani ɗan kasuwa mai shekaru 62 da ke zaune a Legas bisa zargin yunƙurin safarar hodar iblis zuwa ƙasar Chana ta filin jirgin saman Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano. A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar daga hedikwatar hukumar da ke Abuja, ya ce an kama mutumin ne a ranar Asabar yayin tantance fasinjojin da ke shirin tafiya Addis Ababa ta jirgin Ethiopian Airlines, mai lamba ET940, daga nan zuwa Chana. Binciken da aka yi masa…
Read More
Tinubu ya ƙaddamar da jami’in kula da ƙorafe-ƙorafen haraji don ƙarfafa gaskiya a tsarin

Tinubu ya ƙaddamar da jami’in kula da ƙorafe-ƙorafen haraji don ƙarfafa gaskiya a tsarin

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Nijeriya, Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi sabon Jami'in Kula da ƙorafe-ƙorafen Haraji na ƙasa, Mista John Nwabueze, a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, a wani mataki da ke nuni da ƙudurin gwamnati na ƙara inganta gaskiya da ɗaukar alhaki a tsarin tattara haraji. Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da aiwatar da muhimman sauye-sauye a ɓangaren kuɗaɗen shiga, domin gyara tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati, rage tangal-tangal da samar da daidaitaccen yanayi ga ‘yan kasuwa da masu zuba jari. Ofishin nai Kula da ƙorafe-ƙorafe na Haraji,…
Read More
Muna karɓar buƙatun rijistar kasuwanci 10,000 a kullum bayan fara amfani da AI – CAC

Muna karɓar buƙatun rijistar kasuwanci 10,000 a kullum bayan fara amfani da AI – CAC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Rijistar Kamfanoni ta ƙasa (CAC), ta ce a yanzu tana karɓar kusan buƙatun rijistar kasuwanci 10,000 a kowace rana, sakamakon fara amfani da fasahar ƙirƙirar basira ta zamani, wato Artificial Intelligence (AI), a ayyukanta. Babban Magatakardan Hukumar, Hussaini Magaji, ne ya bayyana hakan yayin laccar bikin cika shekaru 35 da kafa CAC, wanda aka gudanar a ranar Litinin a Abuja. Magaji ya ce, amfani da AI ya ƙara wa hukumar ƙarfi wajen sarrafa ɗimbin buƙatun rijistar kasuwanci da kuma tambayoyin kwastomomi da ke shigowa daga sassa daban-daban na ƙasar nan. A cewarsa, adadin masu neman…
Read More