15
Feb
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Rijistar Kamfanoni ta ƙasa (CAC), ta ce a yanzu tana karɓar kusan buƙatun rijistar kasuwanci 10,000 a kowace rana, sakamakon fara amfani da fasahar ƙirƙirar basira ta zamani, wato Artificial Intelligence (AI), a ayyukanta. Babban Magatakardan Hukumar, Hussaini Magaji, ne ya bayyana hakan yayin laccar bikin cika shekaru 35 da kafa CAC, wanda aka gudanar a ranar Litinin a Abuja. Magaji ya ce, amfani da AI ya ƙara wa hukumar ƙarfi wajen sarrafa ɗimbin buƙatun rijistar kasuwanci da kuma tambayoyin kwastomomi da ke shigowa daga sassa daban-daban na ƙasar nan. A cewarsa, adadin masu neman…
