ukarofi

12644 Posts
Tinubu za mu zaɓa a 2027 —Sheikh Jingir

Tinubu za mu zaɓa a 2027 —Sheikh Jingir

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne zabinsu a babban zabe na 2027. Sheikh Jingir, wanda shi ne Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ya bayyana zabin Tinubu ne a yayin taron kara wa juna sani na shekarar 2026 da kungiyar ta shirya a garin Jos. Ya ce kungiyar ta yanke shawarar goyon bayan Tinubu idan bai ci amanar ’yan Nijeriya  ba. A cewarsa, sun riga sun yi masa alkawarin goyon baya domin ya yi wa’adi na biyu,…
Read More
Waƙa: Bishiyar Zumunci

Waƙa: Bishiyar Zumunci

Daga MOHAMMED BALA GARBA  1. Rabbana ka ji ƙan zumunci,            Don a yau mun ruguza shi. 2. Babu mai duba gare shi,               Ko ya ce zai ɗabbaka shi. 3. Ga shi Allah yai bayani,               Kansa domin mu riƙe shi. 4. Ya yi alƙawari na narko,        Gun waɗanda suke katse shi. 5. ɗaha ya yi kira gare mu,                A Hadisai don mu yo shi. 6. Ya faɗo falalar zumunci,                       Da azaba in ka ƙi shi. 7. Yau idan ka tsaya ka duba,                    Duka ba ma aikata shi. 8. Mun yi watsi da zumunci,              Babu mai neman a yo shi. 9. Har…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta tura ɗalibai 34 zuwa Jamus karatun jinya da unguzoma

Gwamnatin Katsina za ta tura ɗalibai 34 zuwa Jamus karatun jinya da unguzoma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗaliban za su fara da horon koyon harshen Jamus na tsawon watanni takwas a Abuja kafin su wuce Legas domin rubuta jarabawar cancanta da za ta basu damar ci gaba da karatu a Jamus. Kwamishinan lafiya na jihar, Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana hakan a yayin bikin bankwana da ɗaliban. Ya ce shirin na daga cikin ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na bunƙasa harkar lafiya da ƙara inganta ƙwarewar ma’aikatan asibitoci a jihar. Kwamishinan ya buƙaci ɗaliban su zama jakadu nagari na jihar Katsina tare da jajircewa wajen cimma burinsu. “Ku ɗauki wannan dama a…
Read More
Yadda mawaƙiya Celine Dion ke yaƙi da cutar da duniya ba ta saba gani ba

Yadda mawaƙiya Celine Dion ke yaƙi da cutar da duniya ba ta saba gani ba

Daga AISHA ASAS Labarin ciwan da ya samu ga mawaƙiya Celine Dion ya kasance tamkar gagarumar guguwa da ta taso a sararin shahara, wadda ba ta tambayar inda ya kamata ta fuskata ba. Cutar wadda ba ta yi la'akari da tarihi ko kuɗi da duk wani gata da masoya da mawaƙiyar ke da ita ba. Tabbas Annabin Rahma ya yi gaskiya, "Ka ci moriyar lafiyarka kafin ciwo" Celine Dion ta kasance murya da ke girgiza ɗakunan kaɗe-kaɗe, ta raunana zukata, tare da samar da shauƙi na musamman. Mawaƙiyar da duniya ta yaba kuma ta amince da ta iya, har ake…
Read More
Bidiyon sanata da Leshaan Dagama: ‘Yar TikTok ta ƙaryata zargin AI da ake yi a bidiyon Adams Oshiomhole

Bidiyon sanata da Leshaan Dagama: ‘Yar TikTok ta ƙaryata zargin AI da ake yi a bidiyon Adams Oshiomhole

Daga AISHA ASAS  Fitacciyar ‘yar TikTok kuma mai wallafa hotunan manya daga Afirka ta Kudu, Leshaan Dagama, ta sake tayar da ƙura a kafafen sada zumunta bayan ta fito fili ta ƙaryata iƙirarin da ake yi cewa bidiyon da ya nuna Sanata Adams Oshiomhole a cikin jirgi mai zaman kansa an ƙirƙire shi ne ta hanyar fasahar AI. Wannan dai na zuwa ne bayan wani bidiyo ya bazu, inda ake zargin tsohon gwamnan Jihar Edo yana tausa ƙafar wata mata a cikin jirgi. Bayan bidiyon ya bazu, ‘yan Najeriya sun gano matar a matsayin Leshaan Dagama, wadda ta shahara a…
Read More
ADC na cigaba da samun karɓuwa a ƙaramar hukumar Karu – Hon. Teghtegh

ADC na cigaba da samun karɓuwa a ƙaramar hukumar Karu – Hon. Teghtegh

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya Shugaban sabuwar jam’iyyar ADC na ƙaramar hukumar Karu jihar Nasarawa Hon. John T. Teghtegh yace a halin yanzu jam’iyyar ta samu sama da magoya baya 70,000 waɗanda aka yi musu rajista a ƙaramar hukumar ta Karu kaɗai. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a gidan sa da ke Uke a Karu. Yace bayan wannan ɗimbin magoya baya da jam’iyyar ke cigaba da samu a ƙaramar hukumar a yanzu, har ila yau jam’iyyar kawo yanzu ta kuma samu sama da ‘yan takara 20 wadanda suka fito neman kujeru…
Read More
Hon. Tony Bala ya buƙaci shugabanni su rika zuba jari a ayyukan addini

Hon. Tony Bala ya buƙaci shugabanni su rika zuba jari a ayyukan addini

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya An buƙaci ‘yan siyasa da shugabanni a duka matakai da masu hannu da shuni a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya su riƙa tallafa wa ayyuka na musamman da ke ɗaukaka harkokin addini a duk inda suka tsinci kansu. Ɗan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a mazaɓar Akwanga da Wamba da kuma Nasarawa-Eggon a jihar Nasarawa Hon. Tony Bala Shama wanda aka fi sani da TBS ne yayi wannan kira a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin mu a wajen wani taron ƙaddamar da babban masallacin Andaha da ke ƙaramar hukumar Akwanga.…
Read More
Za a iya kama ni nan da ba da daɗewa ba – El-Rufa’i

Za a iya kama ni nan da ba da daɗewa ba – El-Rufa’i

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta ADC ya yi zargin cewa dole ne ta sa wasu yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki ko kuma ci gaba da zama a cikinta. Gwamnan na yin wannan zargi ne yayin da hada-hadar siyasa ke neman ɗaukar harama gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027. A baya-bayan nan El-Rufa'i ya tsananta sukar da yake yi wa gwamnatin shugaban Nijeriya Bola Tinubu da kuma jam'iyyar APC mai mulki, wadda a ƙarƙashinta ne ya yi gwamnan jihar Kaduna…
Read More
JAMB ta ƙaryata batun tsawaita rijistar jarrabawar UTME ta 2026

JAMB ta ƙaryata batun tsawaita rijistar jarrabawar UTME ta 2026

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB), ta bayyana ƙarara cewa za ta rufe rijistar Jarrabawar Shiga Jami’o’i ta 2026 (UTME) a ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026, tare da jaddada cewa babu wani shiri na tsawaita wa’adin. Hukumar ta yi wannan bayani ne a cikin sanarwarta ta mako-mako da ta fitar a ranar Litinin, inda ta buƙaci dukkan masu niyyar rubuta jarrabawar su gaggauta kammala rijistarsu ba tare da jira zai lokaci ya ƙure ba. JAMB ta nuna damuwa kan yadda cibiyoyin rijista da dama ke fuskantar ƙarancin masu zuwa yin rijista a…
Read More
CAC a shekara 35: Mun soke rajistar kamfanoni 400,000 a 2025 – Magaji

CAC a shekara 35: Mun soke rajistar kamfanoni 400,000 a 2025 – Magaji

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Nijeriya (CAC), ta sanar da cewa ta soke rajistar kamfanoni fiye da 400,000 da ba sa aiki a shekarar 2025. Wannan mataki, a cewar shugabannin hukumar, wani ɓangare ne na babban garambawul da nufin tsaftace tsarin kasuwanci, kare tattalin arziki, da kuma dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari a cikin gida da waje. Magatakarda-Janar na hukumar, Hussaini Magaji, SAN, ne ya bayyana haka a Abuja yayin wani tattakin motsa jiki da aka shirya domin bikin cikar CAC shekaru 35 da kafuwa. Ya ce yawancin kamfanonin da aka soke rajistarsu sun daɗe…
Read More