14
Feb
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Bagudu, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun haifar da ƙarin kuɗaɗen shiga ga jihohi da ƙananan hukumomi, lamarin da ya ba su damar samar da ƙarin ayyukan more rayuwa ga al’ummominsu. Ministan ya bayyana haka ne yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta ƙasa (NEC) wanda aka kammala a ranar Talata a Abuja, inda ya kuma yaba wa shugaban ƙasa kan yadda ya ƙarfafa tsarin tarayya a Nijeriya. Ya ce, “Shugaba Tinubu ya ƙarfafa tsarin tarayyar mu.” Bagudu ya jaddada…
