14
Feb
Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An yi kira ga al'ummar jihar Kano musamman iyaye mata su fito domin yin rijista da karɓar katin zaɓe da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta ta dawo take gudanarwa a halin yanzu a faɗin ƙasar nan. Shugabar Mata ta Jam'iyyar ADC ta jihar Kano Sayyida Hajiya Maryam Sani Rogo ce ta yi kiran da take zantawa da manema labarai ta ce katin zaɓen yana da mutuƙar muhimmanci wajen zaɓen ra'ayinsu. Ta ƙara da jaddada cewa katin zaɓen shine tamkar muhimmin makami da za a yi amfani da shi wajen tabbatar da an zaɓi…
