ukarofi

12644 Posts
Gwamnan Sakkwato ya ƙaddamar da shirin Tinubu na bayar da tallafi a jihohi 10

Gwamnan Sakkwato ya ƙaddamar da shirin Tinubu na bayar da tallafi a jihohi 10

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da wani gagarumin rabon tallafin abinci da magunguna da abinci mai gina jiki a jihohin arewacin ƙasar 10 da ke fama da matsalolin jinƙai. Yayin ƙaddamar da shirin Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ce gwamnatin tarayya ta ɓullo da shirin domin tallafa wa al'umomin da ke fama da talauci a jihohin arewacin ƙasar 10. Yayin da yake jawabi a garin Kasarawa, inda aka ƙaddamar da shirin, gwamnan ya ce shirin wanda shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya ɓullo da shi, ya zo daidai da zuwan azumin watan Ramadan, lokacin da…
Read More
Yadda asibitoci da jami’o’i ke fama da tsadar lantarki duk da alƙawarin gwamnati

Yadda asibitoci da jami’o’i ke fama da tsadar lantarki duk da alƙawarin gwamnati

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shirin Gwamnatin Tarayya na samar da ingantacciyar wutar lantarki ga jami’o’in Gwamnatin Tarayya da asibitocin koyarwa a faɗin Nijeriya ya samu babban tazgaro, bayan da aka kasa fitar da kuɗaɗen da aka ware wa aikin cikin Dokar Kasafin Kuɗin 2025. Ko da yake an tanadi kimanin naira biliyan 300 domin wani shiri na musamman na inganta lantarki, wani binciken jaridar News Point ya nuna cewa har yanzu ba a fitar da ko sisi ba daga cikin kuɗaɗen, lamarin da ya sa ba a fara aiwatar da aikin ba duk da sanar da shi tun bara. Mai…
Read More
Shugaban ƙaramar Hukumar Kwami ya yaba wa Gwamna Inuwa kan cigaban da ya samar a Gombe

Shugaban ƙaramar Hukumar Kwami ya yaba wa Gwamna Inuwa kan cigaban da ya samar a Gombe

Daga GAMBO ISA a Abuja Shugaban ƙaramar Hukumar Kwami, Honorabul Dr. Ahmed Wali Doho, ya yaba wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, saboda jajircewarsa wajen ci gaba da gudanar da mulki cikin haɗin kai a faɗin jihar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja kuma aka bai wa Blueprint Manhaja, Dr. Doho ya nuna nasarorin da gwamnan ya samu a fannin bunƙasa tattalin arzikin jama'a, noma da kiwo, ilimi, samar da kiwon lafiya, tsaro, da kuma bunƙasa ababen more rayuwa. Ya lura da gina kasuwannin zamani, tare da ayyukan da aka gudanar sama da 328 a garin…
Read More
CBN ya haramta saka furanni da kuɗi gabanin bikin Ranar Masoya

CBN ya haramta saka furanni da kuɗi gabanin bikin Ranar Masoya

Daga MAHDI MUS MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ayyana amfani da abin da ake kira “money bouƙuet” wato shirya takardun kuɗi cikin siffar furanni a matsayin cin zarafin Naira, tare da jera shi cikin laifuffukan da suka haɗa da liƙi, murza kuɗi da sauran su. Rahotanni sun ce wannan mataki na zuwa ne gabanin bikin Ranar Masoya ta bana da za a gudanar a ranar 14 ga Fabrairu, 2026, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta. A ƙarƙashin dokar CBN, duk wanda aka kama yana lalata ko muzanta kuɗin ƙasa na iya fuskantar ɗaurin aƙalla watanni shida…
Read More
Yadda jihohi suka kashe biliyan N455 wajen biyan bashin waje a 2025

Yadda jihohi suka kashe biliyan N455 wajen biyan bashin waje a 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jihohin Nijeriya sun kashe jimillar Naira Biliyan 455.38 wajen biyan bashin waje a shekarar 2025, abin da ya nuna ƙarin biliyan N93.30 idan aka kwatanta da biliyan N362.08 da aka biya a 2024, kamar yadda bayanan Rabon Asusun Tarayya da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) suka nuna. Wannan ƙarin da ya kai kashi 25.77 cikin ɗari ya ƙara nuna yadda nauyin biyan basussuka ke ƙara takura wa kasafin jihohi, inda ake cire kuɗaɗen kai tsaye daga rabon FAAC kafin su isa hannun gwamnatocin jihohi. Binciken ya nuna cewa daga watan Janairu zuwa Yuli 2025, an riƙa…
Read More
Farfesan jami’ar sojoji ya rasu bayan shekara guda a hannun Boko Haram

Farfesan jami’ar sojoji ya rasu bayan shekara guda a hannun Boko Haram

Daga MAHDI MUSA MUHAMMMAD Wani farfesa a Jami’ar Sojin Nijeriya da ke Biu a Jihar Borno ya rasu bayan kusan shekara guda yana tsare a hannun mayaƙan Boko Haram, bayan an sace shi a kan hanyar Damaturu zuwa Biu. Marigayi Farfesa Abubakar Mohammed El-Jummah an ruwaito cewa an yi garkuwa da shi ne a ranar 2 ga Maris, 2025, yayin da yake tafiya a kan titin Damaturu–Biu, wata hanya da ta daɗe tana fama da hare-haren ‘yan tada ƙayar baya da sace-sacen mutane a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya. Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da…
Read More
Kungiyar RTEAN ta ci alwashin mara wa Tinubu baya a 2027

Kungiyar RTEAN ta ci alwashin mara wa Tinubu baya a 2027

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ƙungiyar masu motocin sufuri da daukar ma'aikatan sufuri ta kasa, wato RTEAN ta ayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen shekarar 2027, tare da buƙatar Gwamnatin Tarayya ta kafa wani Bankin Sufuri na musamman domin tallafa wa masu harkar sufuri a faɗin ƙasar nan. An bayyana wannan matsaya ne a hedikwatar ƙasa ta ƙungiyar da ke Abuja ranar Alhamis, inda shugabannin ƙungiyar suka ce sun yanke shawarar ne bayan tuntuɓa mai zurfi da sassan ƙungiyar daga matakin rassa, jihohi, shiyyoyi har zuwa matakin ƙasa. Shugaban RTEAN na ƙasa, Musa Maitakobi, a…
Read More
El-Rufai ya ƙi yarda a kama shi

El-Rufai ya ƙi yarda a kama shi

...Bayan isowarsa Nijeriya daga Masar Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ƙi yarda da yunƙurin jami’an tsaron Nijeriya na su kama shi a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da yake a Abuja a jiya Alhamis. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, a wani faifen bidiyo da aka wallafa a yanar gizo jiya, an ga El-Rufai yana magana da jami’an, waɗanda suka tunkare shi bayan ya sauka daga jirgi a yayin da ya ke dawowa daga Kairo, babban birni ƙasar Masar, amma sai tsohon gwamnan ya kafe kai da fata cewa, ba zai bi…
Read More
Zan yi murabus idan aikin hanyar Abuja–Kaduna–Kano bai yi inganci ba – Minista

Zan yi murabus idan aikin hanyar Abuja–Kaduna–Kano bai yi inganci ba – Minista

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Ayyuka, Mista David Umahi, ya bayyana cewa, a shirye ya ke da ya ajiye muƙaminsa, idan aka tabbatar cewa aikin hanyar Abuja–Kaduna–Kano bai cika ƙa’idojin inganci ba. Ya ce yana maraba da a gudanar da gwaje-gwaje masu zaman kansu domin tantance nagartar aikin. Umahi ya yi wannan jawabi ne yayin da yake kare kasafin kuɗin ma’aikatarsa a gaban zaman hacin gwiwa na Majalisar Dokoki ta ƙasa. A zaman, wasu ‘yan majalisa sun nuna damuwa kan yadda aka ba wani ɓangare na aikin ga kamfani da suka ce ba a san shi sosai a fannin gine-ginen…
Read More
Ina nan daram a Jam’iyyar PDP, sai na ga abin da ya ture wa buzu naɗi – Gwamna Bala

Ina nan daram a Jam’iyyar PDP, sai na ga abin da ya ture wa buzu naɗi – Gwamna Bala

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Yayin da ake ci gaba da lissafa gwamnonin da suke sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Nijeriya, gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, ya ce yana nan a jamiyyarsa ta PDP daram. Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC. Gwamnan ya musanta hakan ne a wata hira da BBC ta yi da shugaban jam'iyyarsa ta PDP a jihar Bauchi wanda ya yi magana da yawun gwamnan. Pharmacist Sama'ila Adamu Burga, shugaban jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, ya ce jita-jita ce kawai. "Da…
Read More