13
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, a ranar Talata, ya tabbatar da cewa za a magance rikicin siyasa da ke ƙara ta'azzara a jihar Ribas nan ba da jimawa ba bayan shiga tsakani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi. Ministan ya faɗi haka ne a Abuja bayan ya duba wasu ayyuka da ake gudanarwa a yankin. An tattaro cewa wannan ci gaba ya samo asali ne daga sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ranar Litinin a hannun Shugaba Tunubu tsakanin Wike da Gwamna Siminalayi Fubara. "Ina ganin da yardar Allah, wannan…
