12
Feb
Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta Jihar Zamfara (Islamic Future Guidance Initiative (TIFGI), ta bayyana goyon bayanta ga ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Maru da Bungudu Hon. Abdulmalik Zubairu (Zannan Bungudu) a matsayin ɗan takarar gwamna a shekarar 2027 ƙarƙashin jam'iyyar APC a Jihar Zamfara. Shugaban ƙungiyar Malam Rabiu Yahaya ya bayyana hakan a taron manema labarai yau Alhamis a Gusau. A cewar sa, ƙungiyar ta tabbatar da Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu a matsayin ɗan takarar da yafi cancanta, yana mai kira ga shugabannin jam'iyyar ta APC da suka hada da Sanata Ahmed Sani…
