ukarofi

12458 Posts
An tsinci jinjira a wani masallaci a Argungu

An tsinci jinjira a wani masallaci a Argungu

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ranar Assabar ɗin da ta gabata ne aka sami rahoton tsintuwar wata jinjira a Masallacin Shehi Musa Fakkai da ke garin Argungu. Wata darakta a hukumar Hisbah reshen ƙaramar hukumar Argungu Hajiya Rabi Ahmed ta bayyana cewa, Da safiyar Asabar ne suka sami rahoto daga ofis na jami'an tsaro na farin kaya cewa an ga wata jinjira ajiye, saboda haka suka isa wajen suka ɗauki yarinyar kamar yadda aka saba.Bayan sun ɗauke ta, suka miƙa ta ga wata ƙungiya mai suna Mar'atussaliha da ke da cibiya a Argungu ƙarƙashin jagorancin Hajiya Mariya Mera saboda ta…
Read More
Yadda wasan ƙwallo ya rikiɗe zuwa zanga-zanga a Kebbi

Yadda wasan ƙwallo ya rikiɗe zuwa zanga-zanga a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Bayanai daga karamar hukumar Jega da ke jihar Kebbi sun nuna yadda waɗansu fusatattun matasa suka shiga garin Jega suna farfasa motoci da yaga allunan Tinubu da gwamnan jihar Malam Nasir Idris bayan kammala wani wasan ƙwallon kafa. Wani matashi ya bayyanawa wakilin Jaridar Blueprint Manhaja da cewa bayan an kammala wasan ƙwallon ƙafa ne na haɗin kan matasa sai ɗaya daga cikin masu jawabi ya bijiro da maganar neman goyon bayan shugaban ƙasa Tinubu da gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris wanda wannan maganar ba ta yi wa kowa daɗi ba wanda a maimakon…
Read More
Alolo ya zama shugaban Online Media Chapel na NUJ a Katsina

Alolo ya zama shugaban Online Media Chapel na NUJ a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An naɗa Alhaji Abubakar Alolo shugaban kamfanin Mobile Media Crew a matsayin shugaban kwamitin riƙobna Online Media chapel ta ƙungiyar 'an jarida reshen Jihar Katsina,sai Mustapha Sadiq na kafar Katsina Post a matsayin sakatare da Zaharaddeen Danjuma na Katsina Times a matsayin Ma'ajin ƙungiyar. Kwamitin riƙon shi zai jagoranci ƙungiyar kafin zaɓe wanda zai kasance na farko bayan ƙaddamar da ƙungiyar.‎‎Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya Alhaji Abubakar Shafi’i Alolo, shugaban kamfanin Mobile Media Crew, murnar naɗa shi a matsayin shugaban kwamitin riƙo na sabuwar Online Media Chapel ta ƙungiyar ’yan jarida…
Read More
‘Yan sanda sun kama wani matashi bisa zargin kashe mahaifinsa a Katsina

‘Yan sanda sun kama wani matashi bisa zargin kashe mahaifinsa a Katsina

Wani matashi ɗan shekaru 27 ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifinsa mai shekaru 80 a ƙauyen Mundadu da ke ƙaramar hukumar Bindawa ta Jihar Katsina. Matashin mai suna Sada Tambai, ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin aikata abin da ya yi sanadin mutuwar mahaifinsa, Adamu Tambai, wanda ya kasance tsohon dagacin unguwar Mundadu. A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar,lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2026, bayan da aka samu rahoton cewa Adamu Tambai ya kasance kwance ba ya motsi a gaban gidansa. 'Yan sanda…
Read More
SWAN ta taya uban ƙungiyar murnar samun lambar yabo a Katsina

SWAN ta taya uban ƙungiyar murnar samun lambar yabo a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar marubuta labarin wasanni ta ƙasa (SWAN),reshen Jihar Katsina,ta taya babban uban ƙungiyar,Alhaji Usman Isyaku,murnar samun lambar yabo ta gwarzon mai ba gwamna shawara da ya fi ƙwazo a jihar. Alhaji Usman Isyaku,wanda shi ne mai ba gwamnan Jihar Katsina shawara kan farfaɗo da aikin gwamnatin ya samu wannan lambar yabo ne bisa gudunmawarsa wajen ci gaba da inganta harkokin ma’aikatan gwamnati da kuma kawo sauye sauye a tsarin aikin gwamnatin jihar. A cikin sakon taya murna,shugaban ƙungiyar ta reshen Jihar Katsina, Malam Nasiru Sani Gide, ya bayyana wannan karramawa a matsayin shaida da ke…
Read More
Guterres ya yi gargaɗi kan AI a jawabinsa na bankwana da jagorancin Majalisar Dinkin Duniya

Guterres ya yi gargaɗi kan AI a jawabinsa na bankwana da jagorancin Majalisar Dinkin Duniya

Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin Duniya, Mista António Guterres, ya yi amfani da jawabinsa na ƙarshe a gaban Babban Taron Majalisar ɗinkin Duniya wajen yin kira ga ƙasashen duniya su ƙara tsaurara tsarin kula da fasahar AI tare da kawo ƙarshen yaƙe-yaƙen da ke ci gaba da haddasa asarar rayuka. Guterres, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 31 ga Disamba, ya ce duniya na fuskantar haɗuwar barazana daga yaƙe-yaƙe, sauyin yanayi, ƙaruwar rashin daidaito da kuma saurin bunƙasar fasahar AI, yayin da tsarin haɗin gwiwar ƙasashen duniya ke fuskantar matsin lamba.  Ya yi kira da a samar da tsarin ƙasa…
Read More
Babban ladani a masallacin Harami, Sheikh Al-Madani ya rasu

Babban ladani a masallacin Harami, Sheikh Al-Madani ya rasu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sheikh Ibrahim bin Adel Al-Madani, ɗaya daga cikin masu kiran sallar Asuba da sauran salloli a Masallacin Harami da ke Makkah, ya rasu a safiyar Litinin yana da kimanin shekaru 51. Tashar Al-Ekhbariya ta Saudiyya ce ta tabbatar da rasuwar, lamarin da ya janyo ɗimbin saƙonnin ta’aziyya da addu’o’i a shafukan sada zumunta. Al-Madani na daga cikin manyan masu kiran salla da ke aiki a Masallacin Harami. A kowace rana, mutum shida daga cikinsu ne ke yin kiran salla a jere domin sallolin farilla biyar, da kuma kiran farko na sallar Asuba, wato Assalatu An fi…
Read More
Trump ya yi barazanar ‘dulmiyar’ da Iran idan ba a cimma yarjejeniya ba

Trump ya yi barazanar ‘dulmiyar’ da Iran idan ba a cimma yarjejeniya ba

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa kasarsa za ta iya dulmiyewa ko ‘halaka’ gwamnatin Iran idan har ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba, a wani jawabi da ya gabatar a gaban taron Majalisar ɗinkin Duniya a birnin New York ranar Talata. Trump ya ce yana da “babban hukunci” da zai yanke kan ko Amurka za ta cimma yarjejeniya da Iran, ko kuma ta ci gaba da kai mata hare-hare. Ya kuma ce ya yi imanin cewa akwai yiwuwar a cimma matsaya tsakanin Washington da Tehran.  Ya kuma zargi Iran da jan ƙafa wajen tattaunawar da za ta…
Read More
Amurka da Denmark sun ƙulla yarjejeniyar tsaron Greenland

Amurka da Denmark sun ƙulla yarjejeniyar tsaron Greenland

Amurka, Denmark da Greenland sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsaro da za ta ba Amurka damar faɗaɗa kasancewar sojojinta a Greenland, bayan watanni ana takaddama kan makomar yankin da ke ƙarƙashin mulkin Denmark. Shugaban Amurka Donald Trump, Firaministar Denmark Mette Frederiksen da Firaministan Greenland Jens-Frederik Nielsen ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a gefen taron Majalisar ɗinkin Duniya a New York ranar Talata.  Yarjejeniyar ta tanadi yiwuwar kafa wasu sabbin sansanonin sojin Amurka guda biyu a Greenland, tare da samar da tsarin kariya daga makamai masu linzami da Amurka ta kira “Golden Dome”. Matakin ya zo ne bayan dogon…
Read More
Kotun Sri Lanka ta ɗaure mutane 15 kan harin Easter na 2019

Kotun Sri Lanka ta ɗaure mutane 15 kan harin Easter na 2019

Wata babbar kotu a Sri Lanka ta samu mutane 15 da laifin hannu a harin kunar bakin wake da aka kai a ranar Easter ta 2019, wanda ya kashe sama da mutane 260 tare da jikkata ɗaruruwan wasu. Harin na 21 ga Afrilu 2019 ya shafi majami'u uku da manyan otal-otal uku a sassan ƙasar, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin hare-haren da suka fi muni a tarihin Sri Lanka tun bayan kawo ƙarshen yakin basasa na ƙasar.  Rahotanni sun ce 15 ɗin an same su da hannu wajen shirya ko taimakawa waɗanda suka kai harin, yayin da wasu…
Read More