29
Sep
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a KatsinaƘungiyar United Nigerian Chaplaincy (UNC), Katsina Command, ta gudanar da taron wayar da kan al’umma kan muhimmancin zaman lafiya da illolin ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a shiyyar Daura.An gudanar da taron ne a sakatariyar ƙaramar hukumar Daura, a matsayin wani ɓangare na rangadin wayar da kai da ƙungiyar ke gudanarwa a shiyyoyi uku na Jihar Katsina.A yayin taron, mahalarta sun tattauna kan yadda shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ke taimakawa wajen haifar da matsalolin tsaro da sauran munanan halaye, musamman tsakanin matasa.An kuma yi kira ga al’umma da su ƙara ba da haɗin kai ga gwamnati da hukumomin…
