ukarofi

12458 Posts
SWAN za ta shirya gasar ƙwallon ƙafa a tsakanin ma’aikatun gwamnatin Katsina

SWAN za ta shirya gasar ƙwallon ƙafa a tsakanin ma’aikatun gwamnatin Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar marubuta labarin wasanni ta ƙasa reshen Jihar Katsina (SWAN) ta kammala shirye shiryen gudanar da gasar ƙwallon ƙafa tsakanin ma’aikatun, hukumomi gwamnati da ke faɗin jihar. Gasar mai taken (Dikko Raɗɗa Inter-Ministrial Football Competition 2026) a turance, an shirya ta ne domin ƙarfafa kyakkyawar alaƙa da haɗin kai tsakanin ma’aikatan gwamnatin, tare da ƙarfafa lafiyar jiki,aiki da kyakkyawar mu’amala a tsakanin ma’aikatan gwamnatin. A cewar ƙungiyar (SWAN), gasar za ta bai wa ma’aikata daga ma’aikatu daban daban da hukumomi damar haɗuwa ta hanyar wasanni, domin ƙarfafa haɗin kai da zumunci a tsakaninsu,ba tare da…
Read More
‘Yan bindiga sun halaka mutane a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Faskari a Jihar Katsina

‘Yan bindiga sun halaka mutane a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Faskari a Jihar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kamar yadda ƙafar sadarwa ta JBC ta ruwaito lamarin ya faru ne sakamakon wani saɓani bayan kama wani mashin ɗauke da wasu mutane tare da kuɗi da ake zargi na biyan kuɗin fansa ne lamarin da yasa aka kasu aka tsare. Lamarin kamar yadda kafar sadarwa ta ruwaito ya harzuƙa 'yan bindiga da takai su ga kai hare hare kan waɗanda basu kina ba su gani ba suka kashe mutane takwas da sace mutum 38 . Sai dai daga baya an ceto mutanen da akai garkuwa da su sakamakon shiga tsakani na masu sasanci a…
Read More
Jiragen kasuwanci za su fara tashi gobe a Gusau yayin bikin cikar Zamfara 30

Jiragen kasuwanci za su fara tashi gobe a Gusau yayin bikin cikar Zamfara 30

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jihar Zamfara za ta cika shekaru 30 da kafuwa gobe, 1 ga Oktoba, tare da ƙaddamar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci zuwa Gusau a matsayin babban abin da zai haskaka bikin. Sakataren gwamnatin Jihar, Abubakar Nakwada, ya bayyana haka a wani taron manema labarai yau Laraba. Ya bayyana cewa bikin cika shekaru 30 ɗin ba biki ne kawai ba, illa dama ce ta yin nazari kan shekaru talatin na juriya da kuma tsara sabuwar hanya ga sabuwar Zamfara. Nakwada ya ce shekaru ukun da suka gabata a ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal sun shaida samun…
Read More
Majalisar dokokin Katsina na shirin kafa sabuwar hukumar kula da makarantun sakandare a jihar

Majalisar dokokin Katsina na shirin kafa sabuwar hukumar kula da makarantun sakandare a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta karɓi rahoton ƙudirin dokar ƙirƙirar hukumar kula da ilimin sakandire ta Jihar Katsina (Katsina State Secondary School Education Board). A wani rahoto da aka gabatar na zaman majalisar ƙarƙashin jagoranci kakakin majalisar dokokin Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura. Shugaban kwamitin Ilimi na majalisar, kuma ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Mai’adua, Hon. Mustapha Rabe Musa, ya gabatar da rahoton tare da yin bayani kan muhimman abubuwan da ƙudirin dokar ya ƙunsa. Sabuwar hukumar da ake shirin kafawa za ta kasance da alhakin kula da harkokin gudanarwa da bunƙasa makarantun…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutane takwas a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane takwas a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina ’Yan bindiga sun kashe mutane takwas a yankin Maigora da Sabon Layi a ƙaramar hukumar Faskari a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne sakamakon wani saɓani da ya biyo bayan kama wani mai mashin, wanda ya ɗauko wasu mutane da kuɗi wanda ake zargin kudin fansa ne, akan hanyar Maigora lamarin da ya sa aka kama mutanen tare da tsare su. Kamar yadda kafar sadarwa na BBC ta ruwaito lamari ya harzuka ’yan bindigar yankin, inda suka kai hari kan mutanan da basu jiba basu gani ba suka halaka mutum takwas, sannan suka yi garkuwa…
Read More
Kwalliya ko barazana? Lokacin da neman hasken fata ke zama haɗari

Kwalliya ko barazana? Lokacin da neman hasken fata ke zama haɗari

(Corticosteroids a kayan kwalliya) Daga AISHA ASAS Akwai wani irin farin ciki da mace kan ji idan ta fara amfani da sabon cream, sannan cikin ’yan kwanaki ta duba jikinta ta ga abin da take kira canji. Wataƙila launin fata ya fara sauyawa, wasu tabo sun yi kamar sun ragu, fata ta yi laushi, sai zuciya ta ce, “Na samu abin da nake nema.” Daga nan sai a ƙara amfani da shi, ko ta ba ƙawarta shawara ta saya, domin idan cream ya yi aiki da sauri, me zai sa a nemi wani? Amma a duniyar kula da fata, akwai…
Read More
Saki boka, ki kama Allah

Saki boka, ki kama Allah

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI ZARIYA A cikin ɗabi'un ɗan adam a kan samu waɗanda son kansu fiye da waninsu kan yi tasiri cikin rayuwarsa, duk da ba dukka zukata ne ba sa juyawa ga bigiren aikata alkhairi ba, duk da haka akan yi la'akari da aiki a aikace ga duk jinsin da suka faɗo cikin filin wannan aikatau ɗin. Asiri, magani, sammu ko makaru dukkansu kalma ɗaya ce da ke nuni da abu guda. Ko ka yi ko kuma ayi ma ka. Duk da akan ce mai baya bai yankar ƙauna, domin ko ba ka haifa ba an haifar ma…
Read More
Tarihin takardar kuɗi ta farko da aka yi amfani da ita a Nijeriya (II)

Tarihin takardar kuɗi ta farko da aka yi amfani da ita a Nijeriya (II)

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Me ya sa aka kawo takardar kuɗi? A farkon amfani da su, takardun kuɗin ba su samu karɓuwa cikin sauƙi ba. Dalilin shi ne, al’ummar yankin sun saba da tsabar kuɗi, kwari, manila da sauran hanyoyin musayar kaya. Bugu da ƙari, darajar wasu daga cikin takardun kuɗin ta yi yawa idan aka kwatanta da ƙananan harkokin kasuwanci da jama’a suka saba gudanarwa. Ekundare ya bayyana cewa mutane da ‘yan kasuwa ba su yi maraba da takardun kuɗin sosai a farkon lokaci ba saboda suna ganin darajarsu ta yi yawa ga ƙananan hada-hadar kasuwanci. Wannan ya sa…
Read More
Tsakanin talauci, rashin ayyukan yi da tsaro

Tsakanin talauci, rashin ayyukan yi da tsaro

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Daya daga cikin muhimman kanun labaran da suka fi ɗaukar hankali cikin waɗannan ’yan makwannin shi ne batun mutuwar matasa 37 a wajen da suke a tsare a ofishin jami’an Sibil Difens na Jihar Neja. Wannan mummunan al'amari da ya faru ya ɗaga hankalin ’yan Nijeriya da dama, musamman ma iyaye, saboda akasarin matasan da suka rasa rayukansu yara ne, waɗanda ko makarantar sakandire ba su kammala ba. Hujjar da jami’an Hukumar Sibil Difens ɗin saka gabatar ita ce, an kama su ne saboda suna aikin haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba. Amma zarge-zarge sun yi…
Read More
Gombe JAAC ta gargaɗi ƙananan hukumomi kan almubazzarancin kuɗi

Gombe JAAC ta gargaɗi ƙananan hukumomi kan almubazzarancin kuɗi

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Kwamishinan ma’aikatar ƙananan hukumomi da bunƙasa al’umma ta Jihar Gombe, Barr. Sani Ahmed Haruna (Wakilin Arewa Gombe), ya gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi 11 da kuma Local Council Development Areas (LCDAs) da su guji almubazzarancin kuɗaɗen jama’a. Haruna ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da yake jagorantar taron kwamitin hadin gwiwa na asusun ƙananan hukumomi (JAAC) na watan Satumba na shekarar 2026, wanda aka gudanar a ɗakin taro na ma’aikatar. Ya umurci shugabannin ƙananan hukumomin da su mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan da za su magance buƙatun al’ummominsu na yau da kullum, musamman…
Read More