ukarofi

12458 Posts
An tsinci gawar dagaci a rami bayan sace shi a Kano

An tsinci gawar dagaci a rami bayan sace shi a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An ruwaito cewa an kashe dagacin ƙauyen Aujarawar Alƙali da ke ƙaramar Hukumar Gezawa a Jihar Kano, Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad, bayan da waɗanda suka yi garkuwa da shi suka kashe shi. An yi garkuwa da Ahmad ne a ranar 17 ga Satumba, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga suka mamaye al’ummar yankin da daddare tare da tafi da shi. Daga bisani, an gano gawarsa a wani kabari mara zurfi a ƙauyen Danladin Gezawa, bayan da mazauna yankin suka gano wurin da aka binne shi. An gudanar da sallar jana’izarsa da misalin ƙarfe 3…
Read More
Juyin mulki: Kotun soji ta ɗage yanke hukunci a karo na huɗu

Juyin mulki: Kotun soji ta ɗage yanke hukunci a karo na huɗu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun Soji ta Musamman da ke sauraron shari’ar zargin wani yunƙurin juyin mulki da ya shafi wasu jami’an sojin Nijeriya ta sake ɗage yanke hukuncin da ya shafi sahihancin bayanan da ake zargin waɗanda ake tuhuma sun bayar, inda ta sanya ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2026, domin ci gaba da zaman. Rahotanni sun ce hukuncin, wanda aka tsara za a yanke shi a ranar Laraba, 30 ga Satumba, 2026, yanzu an dage shi zuwa ranar 5 ga Oktoba. Wannan shi ne karo na huɗu da kotun ta dage yanke hukuncin kan batun. Kotun,…
Read More
Ranar ’Yanci: Nijeriya ta hau sirdi, inji Tinubu

Ranar ’Yanci: Nijeriya ta hau sirdi, inji Tinubu

*Bai kamata ta koma baya ba, a cewarsa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, Nijeriya ta samu sauyi mai muhimmanci a tafiyar tattalin arzikinta, yana mai cewa bayan shekaru uku na aiwatar da wasu gyare-gyare masu wahala tun hawan gwamnatinsa kan mulkin ƙasar, yanzu lokaci ya yi da za a mayar da hankali wajen tabbatar da wadata da inganta rayuwar ’yan Nijeriya. Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar wa ’yan Nijeriya a bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ya ce gyare-gyaren da gwamnatinsa ta…
Read More
Kano ta biya bashin ‘yan fansho na Naira biliyan 32 – Gwamna Yusuf

Kano ta biya bashin ‘yan fansho na Naira biliyan 32 – Gwamna Yusuf

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa ta biya kusan Naira biliyan 32 daga cikin bashin giratuti da sauran haƙƙoƙin da suka taru na ma’aikatan da suka yi ritaya, wanda ya gada daga tsohuwar gwamnati da ya kai Naira biliyan 48. Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a jawabinsa yayin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya, wanda aka gudanar a filin wasanni na cikin gida na Sani Abacha da ke Kano. Ya ce gwamnatin jihar ta kuma ci gaba da biyan fansho a kan kari a kowane…
Read More
Ɗakin karatu na Nasarawa ya shafe shekaru 14 ba tare da wutar lantarki ba – Angela Anya

Ɗakin karatu na Nasarawa ya shafe shekaru 14 ba tare da wutar lantarki ba – Angela Anya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ɗakin karatu na musamman na ƙasa wato National Library of Nigeria a turance reshen Jihar Nasarawa dake birnin Lafia fadar gwamnatin jihar ya koka kan rashin wutar lantarki a cibiyar yana mai cewa cibiyar ta yi ta aiki ba tare da wutar lantarki ba har na tsawon shekaru sama da 14. Shugabar reshen Mrs. Angela Anya ce ta bayyana hakan a wata hira na musamman da tayi da wakilin Manhaja a jihar a Lafia a mako da ake ciki. Anya tace duk da wutar lantarki na da matukar muhimmanci ga bincike da koyo da…
Read More
An yi kira ga ‘yan jarida da su nuna ƙwarewa wajen bada labarai kan zaɓen 2027

An yi kira ga ‘yan jarida da su nuna ƙwarewa wajen bada labarai kan zaɓen 2027

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar 'yan jarida reshen kafofin yaɗa labarai (correspondent's chapel) a Katsina Yusuf Ibrahim Jargaba ya yi kira ga 'yan jarida da su nuna ƙwarewa da adalci wajen bada rahoto kan zaɓen 2027 da zai gudana a ƙasar. Jargaba ya yi wannan kira ne a wani taron ƙarawa juna sani da ƙungiyar ta shirya wa ya'yan da wasu kafofin sadarwa a Katsina. Ya bayyana cewa a Najeriya musamman Jihar Katsina 'yan jarida na da rawar da zasu taka wajen abinda ya shafi zaɓe.Ya ƙara da cewa ta hanyar faɗakarwa al'umma za su fahimci yadda ake…
Read More
Nasarawa @30: Jega da Kukah sun ce rashin shugabanci nagari ya jefa Nijeriya matsala

Nasarawa @30: Jega da Kukah sun ce rashin shugabanci nagari ya jefa Nijeriya matsala

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, Farfesa Attahiru Jega da Bishop na Katolikan Sokoto Bishop Rev. Matthew Hassan Kukah sunce rashin shugabanci nagari na dogon lokaci da gurɓacewar tarbiyya ne ke cigaba da kawo cikas ga cigaban Najeriya. Sun bayyana hakan ne a birnin Lafiya jihar Nasarawa ranar a wajen lacca ta cika shekaru 30 da ƙirƙirar jihar wato a ranar 1 ga Oktoban 1996. Farfesa Jega wanda ya gabatar da babbar lacca mai taken "Jihar Nasarawa a Shekaru 30: Daga tushe zuwa sauyi," ya ce Najeriya ta sha fama…
Read More
Mece ce makomar marubuci a zamanin fasahar AI?

Mece ce makomar marubuci a zamanin fasahar AI?

Daga AISHA ASAS A da, idan mutum ya ga wani kyakkyawan labari ko doguwar maƙala, tambayar farko da za ta zo masa ita ce: wane marubuci ne ya rubuta wannan? Yanzu kuwa akwai wata tambaya da ta fara shiga tsakanin marubuta, mawallafa da masu karatu: shin mutum ne ya rubuta, ko kuma wata na'ura ce ta taimaka masa? Wannan tambayar da a shekarun baya ta kasance kamar labarin makomar da ba ta zo ba, yanzu ta zama wani ɓangare na rayuwar rubutu. Basirar na'ura, wato Artificial Intelligence (AI), ta shiga cikin duniyar rubutu da ƙarfinta , tana taimaka wa wasu…
Read More
Raɗɗa ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2027

Raɗɗa ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2027

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A jawabinsa bayan sanya hannu a kasafin kuɗin, gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa sai da aka saurari buƙatar alummomi dake gundumomi 361 na faɗin jihar wanda aka sanya wasu a kasafin kuɗi. Haka kuma gwamnan ya ce bayan sauran alummomi "Ni da kai na sai da na saurari ma'aikatu da hukumomin gwamnatin domin kare kasafin kuɗin kafin daga baya a gabatarwa majalisar dokoki"Inji Raɗɗa. Gwamna Raɗɗa wanda shine gwamna na farko a ƙasar da ya sanya kasafin kuɗin 2027, ya yabawa Kakakin Majalisar da sauran 'yan majalisar da kammala zama kan kasafin kuɗin kan…
Read More
ASUU UMYU ta yi gargaɗi kan bashin alawus na fiye da watanni 40

ASUU UMYU ta yi gargaɗi kan bashin alawus na fiye da watanni 40

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina, ta nuna damuwa kan bashin wasu haƙƙoƙin alawus da wasu daga cikin mambobinta ke bin gwamnatin jihar, wanda ta ce ya haura na watanni 40. Ƙungiyar ta kuma zargi cewa an dakatar da biyan bashin alawus ɗin ayyukan ilimi (Earned Academic Allowances – EAA), wanda a baya ake biya a kashi-kashi, bayan fara aiwatar da yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta shekarar 2025. Shugaban ASUU na reshen UMYU, Comrade Aminu Usman, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai…
Read More