ukarofi

12662 Posts
’Yan bindiga sun kashe tsohuwa ’yar shekara 75 a Neja

’Yan bindiga sun kashe tsohuwa ’yar shekara 75 a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ’Yan bindiga sun kashe wata tsohuwa ’yar shekaru 75, mai suna Amina Abu-Shaki a ƙauyen Kabe da ke ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja. Sun kashe matar ne a daren ranar Talata, lokacin da maharan suka kai hari. ’Yan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 8 na dare, inda suka riƙa harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, suka fasa shaguna, suka kwashe kayan abinci da dukiyoyi. Ba su yi garkuwa da kowa ba a lokacin da suka kai harin. Wani mazaunin ƙauyen, Malam Awwalu, ya ce ƙauyuka da dama a yankin sun zama kufai saboda…
Read More
Nijeriya ta taki matsayi na 72 a jaddawalin amfani da fasahar AI a duniya

Nijeriya ta taki matsayi na 72 a jaddawalin amfani da fasahar AI a duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Nijeriya ta samu matsayi na 72 daga cikin ƙasashe 188 a jadawalin amfani da AI ta '2025 Global Government AI Readiness Indeɗ', wanda ke nuna yadda gwamnatoci ke shirye-shirye wajen amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI a ayyukan gwamnati. Wannan sakamako ya sanya Nijeriya cikin manyan ƙasashen Afirka ta kudu da Sahara da suka fi nuna ƙwazo a fannin AI. Rahoton, wanda cibiyar Oɗford Insights ta wallafa, ya yi nazari kan gwamnatoci 195 ta hanyar amfani da ma’auni 69 da aka rarraba zuwa ginshiƙai shida da suka haɗa da ƙarfin manufofi, tsarin shugabanci, gine-ginen fasaha,…
Read More
Kotun Abuja ta rufe shari’ar Sanata Natasha bayan Gwamnatin Tarayya ta janye

Kotun Abuja ta rufe shari’ar Sanata Natasha bayan Gwamnatin Tarayya ta janye

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata babbar kotu da take zamanta a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, ta rufe ƙarar ɓata suna da Gwamnatin Tarayya ta shigar kan Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Udughan. Alƙalin kotun, Mai-shari’a Chizoba Orji, ta yanke hukuncin ne bayan lauyan gwamnati, Aderonke Imana, ta shigar da buƙatar janye ƙarar. Bayan haka, lauyan Sanata Natasha, West Idahosa, ya roƙi kotu da ta yi watsi da ƙarar baki ɗaya bisa wannan mataki na gwamnati. Idahosa ya kuma buƙaci kotu da ta umarci a mayar da dukkan takardun da aka karɓa daga hannun Sanata Natasha da masu…
Read More
Rikicin tsige gwamnan Ribas ya fara taɓarɓarewa bayan majalisa ta kasa zama

Rikicin tsige gwamnan Ribas ya fara taɓarɓarewa bayan majalisa ta kasa zama

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dokokin Jihar Ribas, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Martin Amaewhule, ta kasa komawa zaman majalisa a ranar Alhamis kamar yadda aka tsara, abin da ya ƙara jefa shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, cikin ruɗani. A zaman farko na shekarar 2026 da majalisar ta yi a makon jiya, ‘yan majalisar sun ƙaddamar da shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa bisa zargin aikata manyan laifuka a mulki. Daga cikin tuhumar da aka yi musu akwai rusa ginin Majalisar Dokokin Jihar Ribas, zargin kashe kuɗaɗen gwamnati ba tare da amincewar majalisa ba, da kuma wasu…
Read More
Marinar Kano ta zama mafi daɗewa a Afrika

Marinar Kano ta zama mafi daɗewa a Afrika

*Shekaru 538 da kafuwar masana’antar rinin ƙofar Mata Daga IBRAHIM HAMISU da ABDULMUMIN GIWA a Kano Sana’ar rini, kamar sauran sana’o’i a Nijeriya, musamman a fannin waɗanda aka samar daga masaƙa, suna fuskankar ƙalubale sakamakon durƙushewar tattalin arzikin duniya ko abin da ake kallon sakaci daga ɓangarorin da abin ya shafa. Wannan sakaci ya kai ga durƙusar wata sana’a da a da ta zama ginshiƙin biyan buƙatun tufafi na jama’a daga ƙasashe irin su Mali da Libiya, har ta kusa zama inuwa ko ginshiƙi ta abin da take a baya. Sai dai a baya-bayan nan, Gwamnatin Jihar Kano ta sake waiwayar…
Read More
Sarkin Kano Sunusi ll ya koma Jami’ar Northwest

Sarkin Kano Sunusi ll ya koma Jami’ar Northwest

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya samu gurbin karatu a Jami’ar Northwest University, Kano, kamar yadda jami’ar ta sanar a ranar Litinin. A wata takarda da Jafaru Sule Muhammad, shugaban sashen jarrabawa, karɓar ɗalibai da adana bayanai ya sanya wa hannu a madadin magatakarda, an bayyana cewa sarkin ya samu gurbin karatu a fannin Shari’a (LL.B. Common Law and Sharia) a matakin Level 200, daga zangon karatu na 2024/2025. Takardar, wacce aka aika zuwa Gidan Rumfa Kano, ta ce an amince da shigar sarkin ne bayan ya cika sharuɗɗan jami’a na karɓa ta musamman, tare…
Read More
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya: Kwalliya ta biya kuɗin sabulu

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya: Kwalliya ta biya kuɗin sabulu

Daga MUKHTAR YAKUBU  A ranar Laraba 31 ga Disamba 2025 aka gudanar da taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya a babban ɗakin taro na Manpower Deɓelopment Institute dake birnin Dutse Jihar Jigawa. Taron ya samu halartar marubuta manazarta tarihi da al'adu daga cikin Nijeriya da ma wasu ƙasashe na Afrika. Taron wanda ya kasance na kwana guda ne an yi jawabai da sharhi da kuma tattauna muhimman batutuwa da suka shafi rayuwar marubuta da shi kanka rubutun. An dai fara taron ne da misalin ƙarfe 11 na safe inda bayan jawabin buɗe taro aka shiga taron, inda a farkon aka…
Read More
Yadda aka gudanar da bikin auren marubuci  Zubairu Musa Balannaji

Yadda aka gudanar da bikin auren marubuci  Zubairu Musa Balannaji

Daga MUKHTAR YAKUBU  Masu magana su kan ce rana ba ta karya, sai dai uwar 'ya ta ji kunya. Kamar yau ne ake ta maganar an saka ranar auren marubuci Zubairu Musa Balannaje. Cikin hukuncin Allah sai ga shi kuma har ranar ta zo. Domin kuma a ranar  Lahadi 28 ga Disamba 2025 ne aka ɗaura auren Zubairu Musa Balannaje da amaryasa A'isha Auwal Umar. An ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 10 na safe a masallacin Juma'a na Ammar Ibn Yassir dake Unguwar Samegu Gangar ruwa a cikin garin Kano inda ɗumbun jama'a suka taru domin shaida ɗaurin auren.…
Read More
Gwamnatin Katsina ta amince da gina katafariyar kasuwa ta zamani a Daura

Gwamnatin Katsina ta amince da gina katafariyar kasuwa ta zamani a Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Haka kuma za ta sabunta wasu kasuwannin a Ɗandume,Jibiya da Mashi da ke jihar domin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al'ummar jihar. Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu Dr Salisu Bala zango ya sanar da haka ga manema labarai bayan zaman kammala zaman majalisar zartarwa karkashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da aiwatar da shawarwarin kwamitin da ya binciki makarantu masu zaman kansu (Private Tertiary Institutions) da ke bayar da shedar NCE da Diploma don inganta inganci da ɗaga darajar ilimi a manyan makarantun jihar. Haka kuma, majalisar ta amince da siyan kayan fara…
Read More
Tallafin rage talauci na N50,000 na ƙarfafa tattalin arzikin al’ummar Kano – Gwamna Yusuf

Tallafin rage talauci na N50,000 na ƙarfafa tattalin arzikin al’ummar Kano – Gwamna Yusuf

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa shirin tallafin rage talauci da ƙarfafa tattalin arziki na N50,000 duk wata da gwamnatinsa ke aiwatarwa an tsara shi ne domin bai wa masu amfana damar taka rawar gani wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Laraba. Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar rabon jari ga masu cin gajiyar shirin a ɗakin taro na Coronation Hall da ke fadar gwamnatin Jihar…
Read More