ukarofi

12662 Posts
Gwamna Dikko Raɗɗa ya rantsar da sabbin manyan sakatarori da mai ba da shawara na musamman

Gwamna Dikko Raɗɗa ya rantsar da sabbin manyan sakatarori da mai ba da shawara na musamman

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Waɗanda aka rantsar sun haɗa da Tukur Hassan Ɗan Ali shugaban ƙungiyar 'yan Jarida reshen jihar Katsina daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa da Junaidu Muntari daga ƙaramar hukumar Kankara sai Yahaya Abdullahi daga ƙaramar hukumar Safana. Haka zalika, Gwamna Raɗɗa ya rantsar da Alhaji Lawal Mukhtar Ɓaure a matsayin mai ba da shawara na musamman (Special Adviser). Da yake jawabi bayan rantsuwar, gwamnan ya yi kira ga sabbin masu muƙaman da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, amana da nuna kishin jiha da ƙasa baki ɗaya. Dikko ya jaddada cewa gwamnatinsa na da burin inganta tsarin…
Read More
‘Yan sanda sun kama mota maƙare da abubuwan fashewa a Katsina

‘Yan sanda sun kama mota maƙare da abubuwan fashewa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Yan sandan sun kama mutum uku da kayayyakin fashewa, yayin wani samamen sirri da suka gudanar a ƙaramar hukumar Daura ta jihar. Samamen ya biyo bayan umarnin da babban sufetan ƴan sanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun ya bayar na ƙarfafa sintiri, musamman a manyan hanyoyi. Wata sanarwa da mai magana da yawun 'yan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar, ya ce rundunar ta kama mutanen ne a ƙauyen Koza da ke ƙaramar hukumar. Ya ce jami'an rundunar sun kama wata mota ƙirar Golf da wani mai suna Musa ɗan shekara 40 ke tukawa,…
Read More
Zubar gashi: Dalilai da illoli da matakan kariya (2)

Zubar gashi: Dalilai da illoli da matakan kariya (2)

Gabatarwa: Mata da dama suna shiga wani yanayi marar daɗi kan yadda gashinsu yake zubewa. A duk lokacin da suke yin ƙorafi sukan ce “gashinsu yana zuba ba gaira babu dalili”. Gashi ya kasance wani muhimmin ɓangare ne na kamannin mutum, musamman ma ga mata. A yawancin al'adu, ana kallon gashi a matsayin kwalliya, ɗaukaka, ko kuma ƙyau. Saboda haka, zubar gashi (wanda ake kira alopecia a harshen kimiyya) na iya shafar mutum ta fuskar damuwa da kuma rashin walwalar rayuwa. A wannan rubutu, za mu duba me ke janyo zubar gashi, nau’o’in zubar gashi, hanyoyin rigakafi da kuma matakan…
Read More
Maryam Booth ta zama jaruma ta farko da ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Blackville Talents Agency 

Maryam Booth ta zama jaruma ta farko da ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Blackville Talents Agency 

Daga AISHA ASAS  Fitacciyar jaruma a masana’antun Kannywood da Nollywood, Maryam Booth, ta kafa tarihi bayan da ta zama tauraruwa ta farko da ta rattaba hannu da sabon kamfanin kula da hazaka mai suna Blackville Talents Agency Ltd, wani sabon yunƙuri da ke nufin sauya fasalin kula da masu baiwar ƙirƙira a masana’antar nishaɗantarwa ta Najeriya. An sanar da kaddamar da kamfanin ne a ranar Alhamis, 1 ga Janairu, 2026, inda shugabannin Blackville suka bayyana wannan mataki a matsayin shiga sabon fage na dabaru, domin gano, kula da kuma fitar da jajircewa da hazakar ‘yan Najeriya zuwa kasuwannin duniya. The…
Read More
Ranar Jammaje: Mudassiru ƙasim Maryam A Baba da Bello Ibrahim Bily O sun nishaɗantar da mahalarta

Ranar Jammaje: Mudassiru ƙasim Maryam A Baba da Bello Ibrahim Bily O sun nishaɗantar da mahalarta

Daga MUKHTAR YAKUBU  Taron ranar Jammaje da aka saba gudanarwa a duk shekara, a bana taron ya gudana wanda kuma za a iya cewa ya zarce na baya da ake shiryawa. A ranar talata 30 ga Disamba 2025 ne aka gudanar da taron a babban ɗakin taro na Abdullahi Musa da ke harabar Sabuwar Jama'ar Bayero da ke Kano. Taron ya gudana tun daga karfe 10 na safe har zuwa 7 na dare. Tun da farko da yake jawabi dangane da shirya taron, shugaban makarantar Jammaje Academy, Malam Kabiru Musa Jammaje, ya nuna farin cikinsa dangane da yadda matasa suka…
Read More
Sarkin Maska ya kawo abubuwan alheri a Funtua

Sarkin Maska ya kawo abubuwan alheri a Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua kwamred Mannir Suleiman ya bayyana haka a saƙon sa na taya Sarkin Maska, Hakimin Funtua Alhaji Sambo Idris Sambo murna cika shekara 30 a karagar mulki. Ya ce babu shakka Funtua ta bunƙasa ta fanni daban daban musamman cigaba a harkokin kasuwanci da samar da ababen more rayuwa duk a lokacin hakincin Hakimin. Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa, kasuwanci ya ƙaru da kimanin 80 bisa 100 musamman kan abinda ya shafi kayan masarufi . Haka kuma an gina manyan tagwayen hanyoyi da gyaran wasu,samar da jami'a da gina sabbin manyan asibitoci…
Read More
Sabunta rajista: Jigo a jam’iyyar APC a Zamfara ya koka bisa ƙin yi wa magoya bayansa rajista

Sabunta rajista: Jigo a jam’iyyar APC a Zamfara ya koka bisa ƙin yi wa magoya bayansa rajista

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jigo a Jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya zargi kwamitin rajistar e-register na membobin APC da ke ci gaba da gudana hana magoya bayansa yin rijista a jihar. A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa kuma ya bai wa Blueprint Manhaja a Gusau yau Talata, Shinkafi ya ce korar wasu shugabannin ƙananan hukumomi da shugabannin gundumomi daga aikin wani yunƙuri ne na hana magoya bayansa shiga rajistar e-register na membobin jam'iyyar ta APC a jihar. A cewarsa, reshen APC na jihar Zamfara ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi…
Read More
Gwamnatin katsina za ta saki ‘yan bindiga 70 da ke tsare a gidan yari

Gwamnatin katsina za ta saki ‘yan bindiga 70 da ke tsare a gidan yari

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin jihar ta ce za ta saki ɓarayin daji 70 dake tsare a gidan yarin jihar, sai dai gwamnatin ta bayyana cewa yunƙurin sakin 'yan bindigar mataki ne ƙoƙarin ɗorewar yarjejeniyar zaman lafiya da ake yi da dabobin 'yan bindigar da ke addabar sassan jihar, musamman a yankunan ƙaramar hukumar Ƙanƙara. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasir Muazu ne ya yi bayani game da yarjejeniyar da aka cimma da ƙoƙarin gwamnati na kiyaye hakan, Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito. Ya kuma ce za a saki 'yan bindigar ne domin ƙarfafa yarjejeniyar sulhu da…
Read More
Zuwa ga masu ganin sun fi kowa

Zuwa ga masu ganin sun fi kowa

Ya kai mai karatu, ina rubuta maka ne ba da alƙalami na fushi ba, amma da tawada ta nasiha; ba da murya ta tsinuwa ba, amma da numfashin tausayi. Ina rubuta maka ne domin na ga wata cuta mai shiru tana yawo cikin zukatanmu, tana sanya mutum ya ɗauki kansa a matsayin madubi ɗaya tilo, ya ga sauran mutane a karkace. Ita ce cutar girman kai, wadda take sa mutum ya ɗauka cewa shi ne mizani, shi ne ma’auni, shi ne hanyar tsira, sauran kuwa duk sun ɓace. Allah Maɗaukaki ya riga ya gargaɗe mu game da wannan hali tun…
Read More
Musulunci a Amurka

Musulunci a Amurka

Alhamdulillahi, Babban Birnin New York ya shiga sabon babi na tarihi a ƙarƙashin shugabancin Musulmi, lamarin da bai yi wa shugaban Amurka Donald Trump da wasu irinsa daɗi ba. Duk da yadda wasu ke kallon wannan lamari da ido na shakku, gaskiya ita ce samun Zohra Muhammad Mamdani a matsayin jagorar birnin New York wata babbar baiwa ce daga Allah ga addinin Musulunci. Wannan al’amari ya kara tabbatar da cewa duk inda makiya ke ƙoƙarin hana hasken addini, sai Allah Ya ƙara bayyana shi. Allah Ya ba Zohra Muhammad Mamdani nasara a wannan zabe da aka yi a ƙasa irin…
Read More